Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Idan Ka Kamu da Cuta Mai Tsanani

Idan Ka Kamu da Cuta Mai Tsanani

Linda, mai shekara 71 ta ce: “Da likita ya gaya min cewa ina da kansa a hantana da kuma hanjina, na ji kamar an yanke mini hukuncin kisa. Amma bayan na koma gida, sai na yi tunani, ‘To, ko da yake ba abin da nake tsammani ba ne, dole ne in yi abin da zai taimaka min in jimre.’”

Elise, mai shekara 49 ta ce: “Na yi fama da wata cuta mai zafin tsiya a jijiyoyin da ke gefen fuskata. A wasu lokuta, nakan yi baƙin ciki sosai saboda zafin da ciwon yake mini. Na yi fama da kaɗaici kuma na yi tunanin kashe kaina sau da yawa.”

IDAN kai ko wani na kusa da kai ya daɗe yana fama da cuta mai tsanani, za ka san irin baƙin cikin da hakan yake janyowa. Ban da cutar da kake fama da ita, za ka kuma yi fama da tunani. Tsoro da ɗawainiyar da kake ciki za su ƙaru sosai sa’ad da ake ƙoƙarin gano cutarka. Ban da haka ma, wahalar da za ka sha don samun jinyar da kake bukata ko kuɗin jinyar ko kuma abubuwan da za ka fuskanta bayan jinyar za su iya sa ka tsoro da damuwa sosai. Ɗawainiyar da ke tattare da rashin lafiya, tana sa baƙin ciki sosai.

Mene ne zai iya taimaka mana? Mutane da yawa sun shaida cewa yin addu’a da kuma karanta nassosin Littafi Mai Tsarki na ƙarfafa su. Za a kuma iya samun taimako daga wurin ’yan’uwa da abokan arziki.

ABIN DA YA TAIMAKA MA WASU SU JIMRE

Robert mai shekara 58 ya ce: “Idan ka ba da gaskiya ga Allah, zai taimaka maka ka jimre da rashin lafiyar da kake fama da shi. Ka yi addu’a ga Jehobah. Ka gaya masa yadda kake ji. Ka roƙe shi ya ba ka ruhu mai tsarki. Ka roƙe shi ya ba ka ƙarfi don ka iya tallafa ma iyalinka duk da rashin lafiyarka.

“Yana da muhimmanci sosai idan ’yan’uwanka sun taimaka maka kuma sun kasance tare da kai a koyaushe. A kowace rana mutum ɗaya ko biyu sukan kira ni kuma sukan tambaye ni, ‘Yaya jiki?’ Ina samun ƙarfafa daga abokan arziki daga wurare dabam-dabam. Sukan ƙarfafa ni kuma hakan yana taimaka mini in ci gaba da jimrewa.”

Idan kana son ka ziyarci abokinka da bai da lafiya, ka lura da abin da Linda ta faɗa da zai taimaka maka: “Babu shakka marar lafiyar zai so ya yi abubuwa kamar yadda ya saba yi a lokacin da yake da lafiya kuma ba kullum ba ne zai so ya tattauna game da rashin lafiyarsa. Saboda haka, ka tattauna da shi abubuwan da kuka saba tattaunawa.”

Idan muka nemi taimako daga wurin Jehobah da karanta ayoyi masu ban ƙarfafa daga Littafi Mai Tsarki da kuma taimako daga wurin ’yan’uwa da abokan arziki, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa za mu iya jimrewa duk da rashin lafiya mai tsanani da muke fama da shi.