Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 4

Wane Ne Yesu Kristi?

Wane Ne Yesu Kristi?

1. A wane lokaci ne aka halicci Yesu?

Waɗanne halayen Yesu ne suka sa mutane su kusace shi?​—MATTA 11:29; MARKUS 10:13-16.

Yesu ne Allah ya fara halitta. Ya bambanta da ’yan Adam domin ya yi rayuwa a sama a matsayin mala’ika kafin a haife shi a duniya. (Yohanna 8:23) Babu macen da ta haife shi kafin ya soma rayuwa a sama, amma Allah ya halicce shi da kansa kuma shi ya sa ake kiransa Ɗan Allah “haifaffe shi kaɗai.” Yesu ne Kakakin Allah, shi ya sa ake kiransa “Kalman.” (Yohanna 1:14) Yesu ya taimaka wajen halittar sauran abubuwa.​—Karanta Misalai 8:22, 23, 30; Kolosiyawa 1:15, 16.

2. Me ya sa Yesu ya zo duniya?

Allah ya aiko da Ɗansa zuwa duniya ta wurin mayar da ran Yesu daga sama zuwa mahaifan wata budurwa Bayahudiya mai suna Maryamu. Saboda haka, Yesu ba shi da mahaifi ɗan Adam. (Luka 1:30-35) Yesu ya zo duniya ne (1) don ya koyar da gaskiya game da Allah, (2) don ya kafa misali na yin nufin Allah ko sa’ad da muke fuskantar matsaloli, kuma (3) don ya ba da kamiltaccen ransa a matsayin “fansa.”​—Karanta Matta 20:28.

3. Me ya sa muke bukatar fansa?

Fansa diyya ce da ake biya don a ’yantar da mutum daga bauta. (Fitowa 21:29, 30) Mutuwa da kuma tsufa ba nufin Allah ba ne ga ’yan Adam. Ta yaya muka san hakan? Allah ya gaya wa mutumi na farko, Adamu, cewa idan ya yi zunubi zai mutu. Da a ce Adamu bai yi zunubi ba, da bai mutu ba. (Farawa 2:16, 17; 5:5) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa mutuwa ta “shigo” duniya ta wurin Adamu. Saboda haka, Adamu ya yaɗa zunubi da kuma mutuwa ga dukan zuriyarsa. Shi ya sa muke bukatar fansa don ta ’yantar da mu daga mutuwar da muka gāda daga Adamu.​—Karanta Romawa 5:12; 6:23.

Wane ne zai iya biyan fansa don ya ’yantar da mu daga mutuwa? Zunubi ne yake sa muke mutuwa. Tun da yake mu ajizai ne, babu ɗan Adam da zai fanshi wani daga mutuwa da zunubi.​—Karanta Zabura 49:7-9.

4. Me ya sa Yesu ya mutu?

Tun da yake Yesu bai gaji ajizanci ba, bai yi zunubi ba. Saboda haka, ya mutu ne domin zunuban wasu. Allah ya nuna yana ƙaunarmu sosai ta wurin aiko da Ɗansa ya mutu dominmu. Yesu ya nuna yana ƙaunarmu ta wurin yin biyayya ga Ubansa da kuma ba da ransa domin zunubanmu.​—Karanta Yohanna 3:16; Romawa 5:18, 19.

Ka kalli bidiyon nan Me Ya Sa Yesu Ya Mutu?

5. Mene ne Yesu yake yi a yanzu?

Sa’ad da Yesu yake duniya, ya warkar da marasa lafiya, ya ta da matattu kuma ya taimaka wa mutane da suke shan wahala. Ta hakan, Yesu ya nuna abin da zai yi a nan gaba ga dukan mutane masu biyayya. (Matta 15:30, 31; Yohanna 5:28) Bayan Yesu ya mutu, Allah ya ta da shi daga matattu a matsayin mala’ika. (1 Bitrus 3:18) Bayan hakan, Yesu ya jira a hannun damar Allah har sa’ad da Jehobah ya ba shi ikon yin sarauta a matsayin Sarki bisa dukan duniya. (Ibraniyawa 10:12, 13) A yanzu, Yesu yana mulki a matsayin Sarki a sama, kuma mabiyansa a duniya suna shelar bisharar a dukan duniya.​—Karanta Daniyel 7:13, 14; Matta 24:14.

Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai yi amfani da ikonsa a matsayin Sarki don ya kawar da dukan wahala da kuma waɗanda suke haddasa ta. Miliyoyin mutanen da suke ba da gaskiya ga Yesu kuma suke masa biyayya za su ji daɗin rayuwa a cikin aljanna a duniya.​—Karanta Zabura 37:9-11.