Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 5

Mene Ne Nufin Allah ga Duniya?

Mene Ne Nufin Allah ga Duniya?

1. Me ya sa Allah ya halicci duniya?

Jehobah ya halicci duniya don ’yan Adam. Duniya wurin zamanmu ne. An halicci Adamu da Hauwa’u don su yi rayuwa su kuma haifi ’ya’ya a duniya ba a sama ba. Allah ya riga ya halicci mala’iku domin su zauna a sama. (Ayuba 38:4, 7) Shi ya sa Jehobah ya saka mutumi na farko a cikin aljanna mai kyau a duniya. (Farawa 2:15-17) Kuma ya ba Adamu da zuriyarsa begen jin daɗin rayuwa har abada a duniya.​—Karanta Zabura 37:29; 115:16.

Da farko, lambun Adnin ne kaɗai aljanna. Allah ya umurci ma’aurata na farko su haifi ’ya’ya su cika duniya. Yayin da iyalin take ƙaruwa, za su mallaki duniya kuma su mai da ita aljanna. (Farawa 1:28) Ba za a taɓa halaka duniya ba. Za ta kasance wurin zaman ’yan Adam har abada.​—Karanta Zabura 104:5.

Ka kalli bidiyon nan Me Ya Sa Allah Ya Halicci Duniya?

2. Me ya sa duniya ba aljanna ba ce yanzu?

Adamu da Hauwa’u sun yi rashin biyayya ga Allah, shi ya sa aka kore su daga lambun Adnin. Daga nan ne aka rasa aljanna, kuma babu wani ɗan Adam da ya yi nasarar sake kafa ta. Littafi Mai Tsarki ya ce: “An miƙa duniya ga hannun miyagu.”—Ayuba 9:24.​—Karanta Farawa 3:23, 24.

Jehobah bai manta da ainihin nufinsa ga ’yan Adam ba domin Allah maɗaukaki ba ya kuskure. (Ishaya 45:18) Zai mai da ’yan Adam kamiltattu.​—Karanta Zabura 37:11, 34.

3. Ta yaya za a mai da duniya Aljanna?

Duniya za ta zama aljanna sa’ad da Yesu ya soma sarauta a matsayin Sarkin da Allah ya naɗa. A yaƙin Armageddon, Yesu zai ja-goranci mala’ikun Allah kuma za su halaka dukan waɗanda suke hamayya da Allah. Bayan haka, Yesu zai ɗaure Shaiɗan har tsawon shekara 1,000. Amma bayin Allah za su tsira domin Yesu zai ja-gorance su kuma ya kāre su. Za su ji daɗin rayuwa har abada a Aljanna a duniya.​—Karanta Ru’ya ta Yohanna 20:1-3; 21:3, 4.

4. A wane lokaci ne za a daina shan wahala?

A wane lokaci ne Allah zai kawar da mugunta a duniya? Yesu ya ba da “alamar” da za ta nuna sa’ad da ƙarshe ya yi kusa. Yanayin da duniya take ciki a yau yana barazana ga rayuwar ’yan Adam kuma hakan ya nuna cewa muna rayuwa a “karewar zamani.”​—Karanta Matta 24:3, 7-14, 21, 22.

A lokacin da Yesu zai yi sarauta na shekara 1,000 daga sama bisa duniya, zai kawar da dukan wahala. (Ishaya 9:6, 7; 11:9) Ban da ayyukan da zai yi a matsayin Sarki, Yesu zai yi aiki a matsayin Babban Firist kuma zai yafe zunuban waɗanda suke ƙaunar Allah. Da hakan, Yesu zai yi amfani da ikon da Allah ya ba shi don ya kawar da ciwo da tsufa da kuma mutuwa.​—Karanta Ishaya 25:8; 33:24.

5. Su waye ne za su kasance a cikin Aljanna?

A Majami’ar Mulki, za ka haɗu da mutane da suke ƙaunar Allah kuma suke son su koya yadda za su faranta masa rai

Mutanen da suke yin biyayya ga Allah za su kasance a cikin Aljanna. (1 Yohanna 2:17) Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi almajirai kuma su koya musu yadda za su bauta wa Allah a hanyar da ta dace. A yau, Jehobah yana shirya miliyoyin mutane don su yi rayuwa a cikin Aljanna a duniya a nan gaba. (Zafaniya 2:3) A Majami’un Mulki na Shaidun Jehobah, mutane suna koyon yadda za su zama magidanta da matan aure da kuma iyaye maza da mata masu halin kirki. Yara da iyaye suna bauta tare kuma suna koyon yadda za su amfana daga bisharar.​—Karanta Mikah 4:1-4.