Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 12

Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?

Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?

1. Allah yana amsa dukan addu’o’i ne?

Allah yana gayyatar mutane daga dukan al’ummai su kusace shi ta wajen yin addu’a. (Zabura 65:2) Amma, ba dukan addu’o’i ba ne yake sauraro ba. Alal misali, ba zai ji addu’ar mutum da ke wulaƙanta matarsa ba. (1 Bitrus 3:7) Sa’ad da Isra’ilawa suka nace wajen yin mugunta, Allah ya ƙi sauraron addu’o’insu. Hakan ya nuna cewa yin addu’a ga Allah babban gata ne. Kuma, idan masu yin zunubi suka tuba, Allah zai amsa addu’arsu.​—Karanta Ishaya 1:15; 55:7.

Ka kalli bidiyon nan Allah Yana Amsa Dukan Addu’o’i Kuwa?

2. Ta yaya za mu yi addu’a?

Addu’a gata ce kuma bauta ce ga Allah, saboda haka, ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah kaɗai. (Matta 4:10; 6:9) Kuma tun da yake mu ajizai ne, za mu yi addu’a ne a cikin sunan Yesu domin ya mutu don zunubanmu. (Yohanna 14:6) Jehobah ba ya son mu maimaita addu’o’in da aka haddace ko waɗanda aka rubuta. Yana so mu yi addu’a ne daga zuciyarmu.​—Karanta Matta 6:7; Filibiyawa 4:6, 7.

Mahaliccinmu yana jin addu’o’in da aka yi a cikin zuciya. (1 Sama’ila 1:12, 13) Ya gaya mana mu yi addu’a a kowane lokaci, alal misali, sa’ad da muka tashi daga barci da kuma daddare sa’ad da za mu yi barci da lokacin cin abinci da kuma sa’ad da muke fuskantar matsaloli.​—Karanta Zabura 55:22; Matta 15:36.

3. Me ya sa ya kamata mu yi taro?

Kasancewa kusa da Allah ba shi da sauƙi domin muna zaune ne a tsakanin mutanen da ba su yi imani da Allah ba kuma suna yi wa Allah ba’a don alkawarin da ya yi na kawo salama a duniya. (2 Timotawus 3:1, 4; 2 Bitrus 3:3, 13) Saboda haka, muna bukatar mu riƙa yin tarayya mai ƙarfafawa tare da ’yan’uwanmu Kiristoci.​—Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.

Za ka iya kusantar Allah idan ka yi abota da mutanen da suke ƙaunar Allah. Taron da Shaidun Jehobah suke yi zai ba ka zarafin samun ƙarfafa daga bangaskiyar ’yan’uwa.​—Karanta Romawa 1:11, 12.

4. Ta yaya za ka iya zama aminin Allah?

Za ka iya kusantar Jehobah ta wajen yin bimbini a kan abin da ka koya daga Kalmarsa. Ka yi tunani a kan ayyukansa da shawararsa da kuma alkawuransa. Yin bimbini tare da addu’a za su sa ka kasance da godiya saboda ƙauna da kuma hikima da Allah ya nuna.​—Karanta Joshua 1:8; Zabura 1:1-3.

Za ka iya kusantar Allah idan ka dogara da shi kaɗai kuma ka gaskata da shi. Amma, bangaskiya tana kama da abu mai rai da ke bukatar a riƙa kula da shi kullum. Wajibi ne ka riƙa ƙarfafa bangaskiyarka a kai a kai ta wajen yin bimbini a kan abubuwan da ka koya.​—Karanta Matta 4:4; Ibraniyawa 11:1, 6.

5. Ta yaya zaman aminin Allah zai amfane ka?

Jehobah yana kula da waɗanda suke ƙaunarsa. Yana kāre su daga dukan wani abin da zai sa su rasa bangaskiyarsu da kuma begensu na rai na har abada. (Zabura 91:1, 2, 7-10) Ya gargaɗe mu game da irin rayuwar da za ta iya yi wa lafiyar jikinmu da kuma farin cikinmu barazana. Jehobah yana koya mana hanya mafi kyau na yin rayuwa.​—Karanta Zabura 73:27, 28; Yaƙub 4:4, 8.