Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 7

Mene Ne Mulkin Allah?

Mene Ne Mulkin Allah?

1. Mene ne Mulkin Allah?

Me ya sa Yesu ne sarkin da ya dace?​—MARKUS 1:40-42.

Mulkin Allah gwamnati ce ta sama. Zai sauya dukan gwamnatoci kuma zai sa a yi nufin Allah a sama da kuma duniya. Albishiri ne cewa Allah zai yi amfani da Mulkinsa don ya cim ma waɗannan abubuwan. Nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai biya bukatar ’yan Adam na gwamnati mai kyau. Kuma zai sa dukan mutanen da suke duniya su kasance da haɗin kai.​—Karanta Daniyel 2:44; Matta 6:9, 10; 24:14.

Dole ne mulki ya kasance da mai sarauta. Jehobah ya naɗa Ɗansa, Yesu Kristi, ya zama Sarkin Mulkinsa.​—Karanta Ru’ya ta Yohanna 11:15.

Ka kalli bidiyon nan Mene ne Mulkin Allah?

2. Me ya sa Yesu ne Sarkin da ya dace?

Ɗan Allah ne Sarkin da ya dace domin yana da kirki, kuma yana tashi tsaye a kan abin da ke da kyau. (Yohanna 1:14) Yana kuma da isashen ikon taimaka wa mutane domin zai yi sarauta daga sama bisa duniya. Bayan da aka ta da Yesu daga matattu, ya koma sama kuma ya jira a hannun damar Jehobah har sa’ad da aka ba shi izinin soma sarauta. (Ibraniyawa 10:12, 13) A ƙarshe, Allah ya ba shi ikon yin sarauta daga sama.​—Karanta Daniyel 7:13, 14.

3. Su waye ne za su yi sarauta tare da Yesu?

Wani rukunin mutane da ake kira ‘tsarkakku’ za su yi mulki tare da Yesu a sama. (Daniyel 7:27) Waɗanda aka soma zaɓa domin su zama tsarkakku su ne amintattun manzannin Yesu. Har zuwa wannan lokacin, Jehobah ya ci gaba da zaɓan amintattun maza da mata a matsayin tsarkakku. Kamar Yesu, ana ta da su daga matattu a matsayin ruhu.​—Karanta Yohanna 14:1-3; 1 Korintiyawa 15:42-44.

Mutane nawa ne za su je sama? Yesu ya kira su “ƙaramin garke.” (Luka 12:32) A ƙarshe, adadinsu zai kai 144,000. Za su yi sarauta bisa duniya tare da Yesu.​—Karanta Ru’ya ta Yohanna 14:1.

4. Mene ne ya faru sa’ad da Yesu ya soma sarauta?

Mulkin Allah ya soma sarauta a shekara ta 1914. * Jim kaɗan bayan haka, Yesu ya jefo Shaiɗan tare da aljanunsa zuwa duniya. Shaiɗan ya yi fushi kuma ya soma tayar da rigima a duniya. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-10, 12) Tun daga lokacin, matsalolin ’yan Adam suka ƙaru sosai. Yaƙe-yaƙe da yunwa da annoba da girgizar ƙasa suna cikin alamun da ke nuna cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai soma sarauta bisa duniya.​—Karanta Luka 21:7, 10, 11, 31.

5. Mene ne Mulkin Allah yake yi yanzu kuma mene ne zai cim ma a nan gaba?

Ta wajen aikin wa’azin da ake yi a dukan duniya, Mulkin Allah yana taimaka wa miliyoyin mutane daga dukan al’ummai. Miliyoyin mutane masu tawali’u suna zama talakawan Yesu. Mulkin Allah zai kāre su sa’ad da zai kawo ƙarshen wannan mugun yanayin da duniya take ciki. Saboda haka, ya kamata duk waɗanda suke son su amfana daga Mulkin Allah su koyi yadda za su zama talakawan Yesu masu biyayya.​—Karanta Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14, 16, 17.

A cikin shekara dubun, Mulkin zai cika ainihin nufin Allah ga ’yan Adam. Duniya za ta zama aljanna. A ƙarshe, Yesu zai miƙa Mulkin ga Ubansa. (1 Korintiyawa 15:24-26) Akwai wanda za ka so ka gaya masa game da Mulkin Allah?​—Karanta Zabura 37:10, 11, 29.

 

^ sakin layi na 6 Domin samun cikakken bayani game da yadda annabci na Littafi Mai Tsarki yake nuni ga shekara ta 1914, ka duba shafuffuka na 215-218 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?