Koma ka ga abin da ke ciki

Dabbobi Suna Zuwa Sama Ne?

Dabbobi Suna Zuwa Sama Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa a dukan halittun da ke duniya, mutane ne kadan za su je sama. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:​1, 3) Za su je ne su yi hidimar firistoci da kuma sarakuna tare da Yesu. (Luka 22:​28-30; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:​9, 10) Yawanci mutane kuma da za a ta da daga mutuwa za su yi rayuwa a aljanna a duniya.​—Zabura 37:​11, 29.

 A Littafi Mai Tsarki ba a ambata cewa dabbobi za su je sama ba. Me ya sa? Dabbobi ba za su iya daukan matakan samun “kiran nan na sama” ba. (Ibraniyawa 3:1) Wadannan matakan sun kunshi koyo game da Allah da yin imani da shi da kuma bin umurnansa. (Matiyu 19:17; Yohanna 3:16; 17:3) Mutane ne kadai aka halitta don yin rayuwa na har abada.​—Farawa 2:​16, 17; 3:​22, 23.

 Kafin halittun duniya su je sama, ana bukatar a ta da su daga mutuwa. (1 Korintiyawa 15:42) Littafi Mai Tsarki ya ambata wasu tashin matattu da aka yi. (1 Sarakuna 17:​17-24; 2 Sarakuna 4:​32-37; 13:​20, 21; Luka 7:​11-15; 8:​41, 42, 49-56; Yohanna 11:​38-44; Ayyukan Manzanni 9:​36-42; 20:​7-12) Amma dukansu mutane ne aka ta da.

 Dabbobi suna da kurwa ne?

 A’a. Littafi Mai Tsarki ya ce dabbobi da ’yan Adam dukansu kurwa ne. (Littafin Ƙidaya 31:28) Sa’ad da aka halicci mutum na farko, wato Adamu, Allah bai saka masa kurwa ba amma ‘mutum ya zama mai rai.’ (Farawa 2:7) Kurwa tana dauke da abubuwa biyu: “Ƙurar ƙasa” da kuma “numfashin rai.”

 Kurwa tana iya mutuwa kuwa?

 E, Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa kurwa tana iya mutuwa. (Littafin Firistoci 21:11; Ezekiyel 18:20) Sa’ad da dabbobi da kuma ’yan Adam suka mutu, dukansu suna zama ƙurar ƙasa. (Mai-Wa’azi 3:​19, 20) Wato za su daina wanzuwa. a

 Dabbobi suna iya yin zunubi?

 A’a. Yin zunubi yana nufin tunani ko kuma yin abin da ya saba wa ka’idodin Allah. Kafin halittu su iya yin zunubi, suna bukatar su san abu mai kyau da marar kyau, amma dabbobi ba za su iya yin hakan ba. A dan gajeriyar rayuwa da suke da ita suna yin abubuwa ne bisa iliminsu. (2 Bitrus 2:12) Idan kwanakinsu ya kare sai su mutu duk da cewa ba su yi zunubi ba.

 Zai dace a rika cin zalin dabbobi ne?

 A’a. Allah ya ba ’yan Adam iko a kan dabbobi amma ba don su rika cin zalinsu ba. (Farawa 1:28; Zabura 8:​6-8) Allah ya damu da dukan dabbobi har da kananan tsuntsaye. (Yona 4:11; Matiyu 10:29) Ya umurci bayinsa su rika bi da dabbobi yadda ya dace.​—Fitowa 23:12; Maimaitawar Shari’a 25:4; Karin Magana 12:10.

a Don samun karin bayani, ka duba babi na 6 a littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?