Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Ake Nufi da Zunubi?

Mene Ne Ake Nufi da Zunubi?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Zunubi yana nufin duk wani abu da ya saba wa ka’idodin Allah. Hakan ya kunshi taka dokokin Allah ta wajen yin abubuwa marasa kyau ko kuma abubuwa da ba su dace ba a gaban Allah. (1 Yohanna 3:4; 5:17) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa idan mutum bai yi abin da ya kamata ya yi ba, hakan zunubi ne.—Yakub 4:17.

 A asalin harsuna da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, kalmomin da aka yi amfani da su a madadin zunubi suna nufin “kasa isa maki” ko saiti. Alal misali, an yi wasu sojoji a kasar Isra’ila ta dā wadanda suka iya harbi da dutse har ba za su yi “kuskure” ba. Idan aka fassara wannan furucin kalma bayan kalma, fassarar tana iya nufin “ba za su yi zunubi ba.” (Alkalawa 20:16) Hakazalika, yin zunubi yana nufin kasa bin ka’idodin Allah yadda ya kamata.

 A matsayinsa na Mahalicci, Allah ya isa ya kafa wa ’yan Adam ka’idodin da ya kamata su bi. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Kowannenmu zai ba da lissafin kansa.—Romawa 14:12.

Zai yiwu mu daina yin zunubi gaba daya?

 A’a. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Romawa 3:23; 1 Sarakuna 8:46; Mai-Wa’azi 7:20; 1 Yohanna 1:8) Me ya sa ya zama hakan?

 Mutane na farko, wato Adamu da Hawwa’u kamilai ne a lokacin da aka halicce su domin ba a halicce su da zunubi ba kuma an halicce su a cikin kamannin Allah. (Farawa 1:27) Amma sun zama ajizai domin ba su yi biyayya ga Allah ba. (Farawa 3:5, 6, 17-19) Sa’ad da suka haihu, sun ba wa ’ya’yansu zunubi da ajizanci. (Romawa 5:12) Sarki Dauda na Isra’ila ya ce, “Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.”—Zabura 51:5.

Akwai zunubai da suka fi wasu muni ne?

 E. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce mutanen Saduma “mugaye ne masu aikata zunubi kwarai” kuma zunubansu sun yi “muni kwarai.” (Farawa 13:13; 18:20, Littafi Mai Tsarki) Ka yi la’akari da abubuwa uku da za su iya nuna cewa wani zunubi yana da muni sosai.

  1.   Irin zunubin. Littafi Mai Tsarki ya umurce mu mu guje wa miyagun zunubai kamar su fasikanci da bautar gumaka da sata da buguwa da giya da kisa da yin sha’ani da aljanu da kuma kwace. (1 Korintiyawa 6:9-11; Ru’ya ta Yohanna 21:8) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa akwai bambanci tsakanin irin wadannan zunuban da kuma zunubin da aka yi cikin rashin sani kamar yin magana ko kuma yin wani abu da zai bata ma wasu rai. (Misalai 12:18; Afisawa 4:31, 32) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya umurce mu kada mu yi wasa da kowane irin zunubi domin zai iya sa mu yi babban laifi a gaban Allah.—Matta 5:27, 28.

  2.   Dalili. Wasu sukan yi zunubi domin ba su san dokar Allah ba. (Ayyukan Manzanni 17:30; 1 Timotawus 1:13) Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai ba mu hujjar aikata irin wadannan zunuban ba, ya nuna cewa sun sha bambam da zunubin ganganci. (Littafin Lissafi 15:30, 31) ‘Mugun zuciya’ ne ke sa mutane yin zunubin ganganci.—Irmiya 16:12, LMT.

  3.   Yawan aukuwa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa akwai bambanci tsakanin zunubin da mutum ya yi sau daya da kuma zunubin da aka dade ana yi. (1 Yohanna 3:4-8) Wadanda suka “ci gaba da yin zunubi da gangan” bayan sun san abin da ya kamata su yi za su fuskanci hukunci daga wurin Allah.—Ibraniyawa 10:26, 27.

 Lamirin wadanda suka yi zunubi mai tsanani yakan dame su sau da sau. Alal misali, Sarki Dauda ya rubuta cewa: “Kurakuraina sun sha kaina: kamar kaya mai-nauyi sun fi karfina.” (Zabura 38:4) Amma Littafi Mai Tsarki ya yi wannan furuci mai ban karfafa: “Bari mugaye su bar irin al’amuransu, su sāke irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi mai jinkai ne, mai saurin gafartawa.”—Ishaya 55:7, LMT.