Koma ka ga abin da ke ciki

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Bulgariya

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Bulgariya

 Shaidun Jehobah a kasar Bulgariya suna koya wa mutane game da Allah da kuma Kalmarsa da kwazo. Somawa daga shekara ta 2000, darurruwan Shaidu daga wasu kasashe sun kaura zuwa Bulgariya don su taimaka da yin waꞌazi. Wadanne kalubale ne ke tattare da kaura zuwa wata kasa? Akwai amfanin daukan wannan matakin? Ga abin da wasu da suka kaura zuwa Bulgariya suka fada.

Ka Kafa Makasudi

 Wani danꞌuwa mai suna Darren, wanda yake zama a Ingila ya ce: “Tun da dadewa, mun kafa wa kanmu makasudin kaura zuwa kasar da ake bukatar masu shela sosai. Bayan da na auri matata Dawn, sai muka koma Landan da zama don mu taimaka da koya wa mutane Littafi Mai Tsarki a yaren Rasha. Akwai lokutan da muka yi shirye-shirye don mu kaura amma hakan bai yiwu ba don wasu dalilai. Mun kusan fid da rai, sai wani abokinmu ya taimaka mana mu ga cewa yanayinmu ya canja kuma zai yiwu mu kaura.” Sai Darren da Dawn suka fara neman kasar da ake bukatar masu shela sosai da za ta dace da su. A 2011, sun kaura zuwa Bulgariya.

Darren da Dawn

 Misalin ꞌyanꞌuwa da suka ji dadin kaura zuwa wasu kasashe ya karfafa wadanda dā ma ba su da makasudin kaura zuwa wata kasa. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Giada, wadda take zama da mijinta mai suna Luca a Italiya ta ce: “Na hadu da ꞌyanꞌuwa mata masu waꞌazi da kwazo da suke hidima a Kudancin Amirka da Afirka. Labaransu da yadda suke farin ciki sun burge ni sosai. Hakan ya sa na canja makasudina a hidimata ga Jehobah.”

Luca da Giada

 Danꞌuwa Tomasz da matarsa Veronika sun kaura daga Jamhuriyar Czech zuwa Bulgariya a 2015, tare da yaransu biyu, Klara da Mathias. Me ya sa suka kaura? Tomasz ya ba da amsar ya ce: “Mun yi tunani a kan misalin wadanda suka kaura zuwa wata kasa. Yadda suke farin ciki ya burge mu sosai kuma mukan yi tadinsu a gida.” Yanzu, wannan iyalin suna hidima da farin ciki a sabon yankinsu a birnin Montana a Bulgariya.

Klara, Tomasz, Veronika, da Mathias

 Linda ma wata Mashaidiya ce da ta kaura zuwa Bulgariya. Ta ce: “Shekarun baya na kai ziyara a kasar Ecuador kuma na hadu da wasu Shaidu da suka kaura zuwa kasar don su yi waꞌazi. Hakan ya sa na gaya wa kaina cewa, kila wata rana ni ma zan iya kaura zuwa inda ake bukatar masu shela sosai.” Wasu maꞌaurata daga kasar Finland masu suna Petteri da Nadja ma sun yi tunani a kan misalin wasu. Sun ce: “A ikilisiyarmu ta dā, muna da kwararrun masu shela da suka kaura zuwa wasu wurare don su taimaka da yin waꞌazi. Sukan gaya mana yadda suka ji dadin hidimarsu a wuraren da suka kaura kuma sukan ce lokutan ne suka fi yin farin ciki.”

Linda

Nadja da Petteri

Soma Shiri Tun da Wuri

 Dole ne wadanda suke so su kaura zuwa wata kasa su yi shiri da kyau. (Luka 14:​28-30) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Nele, daga kasar Belgium ta ce: “Da zarar na soma tunanin kaura zuwa wata kasa, sai na yi adduꞌa kuma na bincika littattafanmu da suka yi magana game da yin hidima a wata kasa. Na yi nazarin su sosai kuma na yi tunanin abubuwan da ya kamata in yi don in kaura.”

Nele (dama)

 Kristian da Irmina, ꞌyan kasar Polan ne da suka yi shekaru tara yanzu a Bulgariya. Sun gano cewa yin hidima a wani rukunin da ake yaren Bulgariya a Polan kafin su kaura ya taimaka musu sosai. ꞌYanꞌuwa da ke rukunin sun karfafa su kuma sun taimaka musu su koyi yaren. Kristian da Irmina sun ce: “Mun fahimci cewa idan ka ba da kanka ka yi wa Jehobah hidima, Jehobah zai biya bukatunka kuma hakan abu ne mai ban karfafa. Idan ka gaya wa Jehobah cewa ‘Ga ni nan, ka aike ni!’ zai taimaka maka ka yi abubuwan da ba ka taba tsammani za ka iya yi ba.”​—Ishaya 6:8.

Kristian da Irmina

 Wasu maꞌaurata daga Siwizalan masu suna Reto da Cornelia sun saukaka salon rayuwarsu don su shirya kansu kuma su iya tara kudi don kaura. Sun bayyana cewa: “Shekara daya kafin mu kaura, mun je kasar Bulgariya mun yi mako daya don mu ga yadda rayuwa a kasar take. Da muka isa, mun yi magana da wasu maꞌaurata masu waꞌazi a kasar waje kuma sun ba mu shawara da ta taimaka mana sosai.” Reto da Cornelia sun bi shawarwarin da aka ba su kuma yanzu sun yi fiye da shekaru 20 a Bulgariya.

Cornelia da Reto, da yaransu Luca da Yannik

Shawo kan Matsaloli

 Wadanda suka kaura zuwa wata kasa za su bukaci su saba da yanayoyi da za su iya yi musu wuya. (Ayyukan Manzanni 16:​9, 10; 1 Korintiyawa 9:​19-23) Wani babban kalubale da ꞌyanꞌuwa da yawa suka fuskanta shi ne koyan sabon yare. Luca, wanda aka ambata a baya ya ce: “A ikilisiyarmu ta dā, muna jin dadin yin kalamai daga zuciyarmu a taro. Amma da farko da muka kaura, ya yi wa ni da matata wuya mu shirya kalami, ko da mai sauki ne, a yaren Bulgariya! Ya bi ya zama kamar mu yara ne. Kai, ko yaran da suke yaren ma sun fi mu ba da kalamai masu maꞌana.”

 Ravil, daga Jamus ya ce: “Koyan yaren yana sa ni gajiya. Na yi ta gaya wa kaina cewa, ‘Kar ka damu da kurakuran da kake yi a yaren, amma ka mai da su abin dariya.’ Ban dauki kalubalen a matsayin matsala ba, amma na dauke su a matsayin damar yi wa Jehobah hidima.”

Ravil da Lilly

 Linda, wadda aka ambata a baya ta ce: “Ni ba mai saurin koyan sabon yare ba ce. Yaren Bulgariya ba shi da saukin koya, kuma sau da yawa na yi tunanin daina koyan yaren. Mutum yakan kadaita idan ba ya iya magana da mutane kuma ba ya fahimtar abin da suke fada. Duk abin da nake nazarinsa, a yaren Swedish ne nake karantawa don in karfafa dangantakata da Jehobah. A karshe, ꞌyanꞌuwana maza da mata sun taimaka mini don in koyi yaren.”

 Wadanda suka kaura suna fuskantar wani kalubale kuma, wato yin kewar iyalinsu da abokansu. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Eva, da ta kaura zuwa Bulgariya tare da mijinta Yannis ta ce: “Da farko, na kadaita. Abin da ya taimaka mana mu magance matsalar shi ne, mukan kira iyalinmu da abokanmu da ke gida a kai a kai ko mu tura musu sako, kuma mun yi kokari don mu sami sabbin abokai a nan ma.”

Yannis da Eva

 Akwai wasu kalubale kuma ban da wadannan. Robert da Liana da suka kaura daga Siwizalan sun bayyana cewa: “Babban kalubalen da muka fuskanta a nan shi ne koyan yare da alꞌadun mutanen, da kuma sabawa da balaꞌin sanyi da ake yi a nan.” Amma kasancewa da raꞌayin da ya dace da zama masu faraꞌa ya taimaka wa maꞌauratan nan su ci gaba da yin hidimarsu, kuma sun yi shekaru 14 yanzu suna hidima a Bulgariya.

Robert da Liana

Albarkun Kaura Zuwa Inda Ake Bukatar Masu Shela

 Lilly tana karfafa duk wadanda za su iya kaura zuwa wuraren da ake bukatar masu shela su yi hakan. Ta ce: “Na ga yadda Jehobah ya taimaka mini a hanyoyi dabam-dabam, kuma da ban kaura ba, watakila da ban ga hakan ba. Ina taimaka ma wasu su koya game da Jehobah. Hakan yana sa in dada kusantar Jehobah, in yi farin ciki kuma in sami gamsuwa.” Mijinta Ravil ya yarda da abin da ta fada. Ya ce: “Wannan ce hanyar rayuwa mafi kyau da kuma damar sanin Kiristoci masu kwazo daga kasashe dabam-dabam da suka kware a koya wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Na koyi abubuwa sosai daga wurin su.”

 Halin sadaukarwa na ꞌyanꞌuwa da yawa da suka ba da kansu ya sa ana yin waꞌazin labari mai dadi na “Mulkin Sama koꞌina a duniya.” (Matiyu 24:​14, Mai Makamantu Ayoyi) Da yake sun yarda su je su taimaka wa mutane, wadanda suka je Bulgariya sun ga yadda Jehobah ya ba su abin da zuciyarsu take so, kuma ya ba su nasara cikin dukan shirye-shiryensu.​—Zabura 20:​1-4.