Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Akwai Shawarwari Masu Kyau a Littafi Mai Tsarki

Akwai Shawarwari Masu Kyau a Littafi Mai Tsarki

Idan muka yanke shawara bisa ga raꞌayinmu da na wasu kawai, ba za mu kasance da tabbaci cewa zaɓinmu zai kawo mana sakamako mai kyau ba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da ya sa. Ban da haka ma, yana ɗauke da shawarwarin da za su taimaka mana a rayuwa, kuma hakan zai sa mu yi farin ciki.

MUNA BUKATAR JA-GORANCIN ALLAH

A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah a Allah ya bayyana cewa yana so ꞌyan Adam su nemi taimakon daga wurinsa, maimakon su ja-goranci kansu. (Irmiya 10:23) Shi ya sa ya ba da shawara da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Yana ƙaunar ꞌyan Adam kuma ba ya so mu yanke shawarwarin da za su sa mu baƙin ciki kuma mu sha wahala a rayuwa. (Maimaitawar Shariꞌa 5:29; 1 Yohanna 4:8) Ban da haka, shi ne Mahaliccinmu, yana da hikima kuma ya san abin da zai fi amfanar mu. (Zabura 100:3; 104:24) Duk da haka, Allah ba ya tilasta wa mutane su bi ƙaꞌidodinsa.

Jehobah ya ba mata da miji na farko, wato Adamu da Hauwaꞌu duk abin da suke bukata da zai sa su farin ciki. (Farawa 1:​28, 29; 2:​8, 15) Kuma ya ba su umurni da ya so su bi. Amma, ya ba su ꞌyanci su zaɓa ko za su bi umurninsa ko aꞌa. (Farawa 2:​9, 16, 17) Abin baƙin ciki shi ne, Adamu da Hauwaꞌu sun zaɓi su bi nasu raꞌayin maimakon na Allah. (Farawa 3:6) Mene ne sakamakon? Shin mutane suna farin ciki don suna yin duk abin da suke gani ya dace? Aꞌa. A cikin shekarun da suka shige, mun gano cewa ƙin bin ƙaꞌidodin Allah ba ya kawo farin ciki da kwanciyar hankali na dindindin.—Mai-Waꞌazi 8:9.

Littafi Mai Tsarki na ɗauke da shawarar da muke bukata don yanke shawarwari masu kyau da za su taimaka mana ko a ina ne muke da zama ko daga ina ne muka fito. (2 Timoti 3:​16, 17; ka duba akwatin “ Littafi Don Dukan Mutane.”) Ka ga yadda Littafi Mai Tsarki yake hakan.

Ka ƙara koyan dalilin da ya sa ya dace da aka kira Littafi Mai Tsarki “kalmar Allah.”—1 Tasalonikawa 2:13. Ka kalli bidiyon Wane ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki? a dandalin jw.org/ha.

LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊI ABIN DA ALLAH YAKE SO MU YI

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da dangantakar Jehobah da ꞌyan Adam tun daga farko. Abin da ke cikinsa ya taimaka mana mu fahimci abin da ya dace a gaban Allah da abin da bai dace ba. Ban da haka, za mu fahimci abin da zai amfane mu da kuma abin da zai jawo mana lahani. (Zabura 19:​7, 11) Za mu koyi ƙaꞌidodin da za mu yi amfani da su a kowane lokaci kuma za su taimaka mana mu yi zaɓi masu kyau a rayuwa.

Alal misali, ka yi laꞌakari da shawara da ke Karin Magana 13:20: “Wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima, amma abokin tafiyar wawaye zai lalace.” Wannan shawarar ta dace da zamanin nan, kamar yadda take a dā. Littafi Mai Tsarki yana cike da irin waɗannan ƙaꞌidodi masu kyau.—Ka duba akwatin “ Littafi Mai Tsarki Yana da Amfani a Koyaushe.”

Amma kana iya yin tunani, ‘Ta yaya zan tabbata cewa shawara da ke cikin Littafi Mai Tsarki za ta taimaka mini a yau?’ A talifi na gaba za a tattauna misalan wasu mutane.

a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.—Zabura 83:18.