Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yin Hakuri da Mutane​—Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Mana

Yin Hakuri da Mutane​—Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Mana

 A shekara ta 1995, kungiyar UNESCO na Majalisa Dinkin Duniya ta yi magana a kan kaꞌidodin amincewa da mutane, ta ce: “Wajibi ne mutane su rika yin hakuri da juna don a yi zaman lafiya a duniya.”

 Amma idan mutane ba sa yin hakuri da juna, hakan zai sa su tsani juna kuma su dinga yi wa kansu bakar magana da nuna wariya da tashin hankali.

 Amma mutane suna da raꞌayoyi dabam-dabam game da abin da yin hakuri da mutane yake nufi. Wasu sun gaskata cewa wajibi ne mutane da ke yin hakuri da mutane su so dukan ayyuka da halayen mutanen. Wasu kuma sun amince da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki cewa wadanda suke yin hakuri da mutane suna daraja zabin da mutane suke yi da kuma imaninsu, ko da ba sa son hakan.

 Shin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa mutane su rika yin hakuri da juna a zamaninmu?

Littafi Mai Tsarki ya nuna dalilin yin hakuri da mutane

 Littafi Mai Tsarki yana so mu rika yin hakuri da mutane. Ya ce: “Bari ku kasance da halin haƙuri cikin dangantakarmu da kowa.” (Filibiyawa 4:5) Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu rika bi da mutane a hanyar da ta dace. Ba lallai ba ne cewa wadanda suke bin wannan shawara za su amince da raꞌayoyin wani ba, amma suna barin shi ya yi abin da yake so da kuma ya bi imaninsa.

 Amma Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya fada irin halayen da ya kamata ꞌyan Adam su kasance da su. Ya ce: “Ya kai dan Adam, Yahweh ya riga ya nuna maka abin da yake mai kyau.” (Mikah 6:8) Ya fadi abubuwan da Allah ya kafa don ya taimaka wa mutane su ji dadin rayuwa mafi kyau.​—Ishaya 48:​17, 18.

 Allah bai ba mu ikon shariꞌanta mutane ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ne kadai mai ba da Koyarwa, shi ne kuma mai yin shariꞌa. . . . Wane ne kai da har ka isa ka dora wa danꞌuwanka laifi?” (Yakub 4:12) Allah ya ba kowannenmu ꞌyancin yin zabi da za mu kasance da alhakinsa.​—Maimaitawar Shariꞌa 30:19.

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da yin ladabi

 Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata mu rika “yi wa kowa ladabi.” (1 Bitrus 2:​17, New Jerusalem Bible) Saboda haka, wadanda suka zabi su bi kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki suna ba dukan mutane ladabi, ko da mene ne mutanen suka yi imani da shi ko kuma irin salon rayuwa da suke yi. (Luka 6:31) Hakan ba ya nufin cewa wadanda suke bi kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su amince da kowane imani ko raꞌayin da wasu suke bi ba. Kuma hakan ba ya nufin cewa za su goyi bayan kowace shawara da wasu suka yanka. Maimakon su rika rashin ladabi ko taurin kai, za su yi iya kokarinsu su yi koyi da yadda Yesu ya yi cudanya da wa wasu.

 Alal misali, Yesu ya taba haduwa da wata mata da ke bin addini da bai amince da shi ba. Kari ga haka, wannan matar tana zama da mutumin da ba mijinta ba, Yesu bai so irin rayuwar da matar take yi. Duk da haka, ya daraja ta saꞌad da yake yi mata magana.​—Yohanna 4:​9, 17-24.

 Kamar Yesu, Kiristoci suna a shirye su bayyana imaninsu ga wadanda suke so su saurara, amma suna yin hakan “da ban girma.” (1 Bitrus 3:15) Littafi Mai Tsarki ya gargadi Kiristoci kada su tilasta wa mutane su bi raꞌayoyinsu. Ya ce kada mabiyin Kristi “ya zama mai yawan gardama, amma dai ya zama mai kirki ga kowa,” har da wadanda suke bin wani imani.​—2 Timoti 2:24.

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kiyayya

 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana mu ꞌyi iyakacin kokari mu zauna lafiya da kowa.’ (Ibraniyawa 12:14) Wanda yake son zaman lafiya da mutane ba ya son nuna kiyayya. Ko da yake ba ya yi abin da zai taka dokar Allah, yana yin iya kokarinsa ya yi zaman lafiya da mutane. (Matiyu 5:9) Littafi Mai Tsarki ya kuma karfafa Kiristoci su rika kaunar magabtansu ta wajen yi wa wadanda suke wulakanta su alheri.​—Matiyu 5:44.

 Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana ‘kin’ ayyuka da ke wulakanta mutane ko kuma jawo musu lahani, wadannan abubuwa “abin kyama” ne a gare shi. (Karin Magana 6:​16-19) Amma Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “ki” don ya kwatanta rashin so wasu mugayen ayyuka. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah yana a shirye ya gafarta wa mutane da suke so su canja salon rayuwarsu kuma su soma rayuwa da ta jitu da kaꞌidodinsa, ya kuma ce zai taimaka musu.​—Ishaya 55:7.

Ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana a kan yin hakuri da mutane da kuma ladabi

 Titus 3:2: Ku “kasance da saukin kai, [kuna] yi wa kowa cikakken tawaliꞌu.”

 Mutum mai sanin yakamata ba ya nace wa raꞌayinsa, hakan yana sa mutane su rika daraja juna.

 Matiyu 7:12: “Duk abin da kuke so mutane su yi muku sai ku ma ku yi musu.”

 Dukanmu muna farin ciki saꞌad da mutane suka nuna mana ladabi kuma suka nuna cewa sun damu da yadda muke ji da kuma daraja raꞌayinmu. Don ka kara koya game da yadda za ka bi wannan dokar hali da Yesu ya koyar, ka duba talifin nan “What Is the Golden Rule?

 Yoshuwa 24:15: “Ku zabi wanda za ku bauta masa.”

 Idan muna daraja zabin da mutane suka yi, hakan zai sa a yi zaman lafiya.

 Ayyukan Manzanni 10:34: “Allah ba ya nuna bambanci.”

 Allah ba ya nuna bambanci da alꞌada da jinsi da kasa da kabila ko kuma wurin da mutum ya fito. Wadanda suke so su yi koyi da Allah suna daraja dukan mutane.

 Habakkuk 1:​12, 13: Allah ba ya amincewa da mugunta.

 Allah yana da iyaka a kan abin da yake amincewa da shi. Ba zai bar mugaye su ci gaba da yin mugunta har abada ba. Don ka kara koya game da hakan, ka kalli bidiyon nan Me Ya Sa Allah Ya Kyale Mutane Su Sha Wahala?

 Romawa 12:19: “Ku bar wa Allah ya rama muku da fushinsa. Don kuwa a rubuce yake cikin Maganar Allah cewa, “Ramuwa tawa ce, ni kuwa zan rama, in ji [“Jehobah,” a New World Translation]

 Jehobah bai ba kowa ikon yin ramuwa ba. Zai tabbata cewa an yi adalci a daidai lokacinsa. Don samun karin bayani, ka karanta talifin nan “Za A Taba Samun Adalci a Dukan Duniya Kuwa?

a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah. (Zabura 83:18) Ka karanta talifin nan “Wane ne Jehovah?