Koma ka ga abin da ke ciki

Akwai Ayoyi a Cikin Littafi Mai Tsarki da Ba Su Jitu da Juna Ba?

Akwai Ayoyi a Cikin Littafi Mai Tsarki da Ba Su Jitu da Juna Ba?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 A’a, dukan bayanan da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun jitu da juna. Za ka iya gani kamar wasu ayoyi a cikin Littafi Mai Tsarki ba su jitu da sauran ayoyin ba, amma idan ka bi wadannan mizanan da ke gaba, za ka iya fahimtarsu da kyau:

  1.   Ka yi la’akari da ainihin batun da ake tattaunawa. Idan wani mawallafi ya yi rubutu kuma aka yi kaulinsa rabi da rabi, masu sauraro za su iya gani kamar kalmominsa ba su da jituwa.

  2.   Ka yi la’akari da ra’ayin marubucin. Mutane dabam-dabam za su iya ba da labarin wani abu da ya faru daidai amma dukansu ba za su yi amfani da kalamai iri daya ba.

  3.   Ka yi la’akari da tarihin mutanen da ke cikin labarin da kuma al’adunsu.

  4.   Ka bambanta furucin da aka yi a alamance da wanda aka yi a zahiri.

  5.   Ka fahimci cewa za a iya ce mutum ya yi wani abu, ko da yake ba shi da kansa ne ya yi abin ba. a

  6.   Ka yi amfani da juyin Littafi Mai Tsarki da ya yi daidai.

  7.   Kada ka gwada daidaita abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa da koyarwar addinan karya.

 Misalai na gaba za su nuna yadda wadannan ka’idodin za su taimaka mana mu fahimci batutuwan da muke gani kamar sun saba da juna a cikin Littafi Mai Tsarki.

Ka’ida ta 1: Ainihin batun da ake tattaunawa

  Idan Allah ya huta a rana ta bakwai, a wace hanya ce yake ci gaba da aiki a yau? Ainihin batun da ake tattaunawa a cikin littafin Farawa game da halitta ya sa mun fahimci cewa wannan furucin “[Allah] ya huta fa a kan rana ta bakwai daga dukan aikinsa da ya yi” yana nufin Allah ya huta daga aikinsa na halittar duniya ne. (Farawa 2:​2-4) Amma da Yesu ya ce “[Allah] yana aiki har yanzu,” maganarsa ba ta saba wa wannan furucin ba domin yana magana ne game da wasu ayyukan Allah dabam. (Yohanna 5:​17) Ayyukan Allah sun kunshi yadda ya hure ’yan Adam su rubuta Littafi Mai Tsarki da yadda yake yi wa mutane ja-gora da kuma kula da su.—Zabura 20:6; 105:5; 2 Bitrus 1:​21.

Ka’idodi na 2 da 3: Ra’ayi da kuma tarihi

  A ina ne Yesu ya warkar da wani makaho? Littafin Luka ya ce Yesu ya warkar da wani makaho sa’ad da “ya kusato Jericho,” amma littafin Matta ya ambata makafi biyu, kuma ya ce hakan ya faru ne sa’ad da ya ‘fita daga Jericho.’ (Luka 18:35-43; Matta 20:29-34) Da gaske ne cewa abubuwan da wadannan marubutan sun fada sun bambanta, amma su biyun sun ba da bayanai da za su sa mu fahimci labarin sosai. Matta ya mai da hankali ga yawan mutanen kuma ya ce su biyu ne, amma Luka ya mai da hankali ga ainihin mutumin da Yesu ya yi magana da shi. Game da wurin da Yesu ya yi warkarwar kuma, ’yan tonan kasa sun ce a zamanin Yesu, Jericho ya kunshi birane biyu. Dayan birnin tsoho ne da Yahudawa ke zama a ciki, kuma yana da nisan wajen kilomita daya da rabi (wato, mil 1) daga sabon yankin birnin da Romawa suke zama a ciki. Kila Yesu yana tsakanin wadannan biranen ne sa’ad ya yi mu’ujizar.

Ka’ida ta 4: Furucin da aka yi a alamance da kuma a zahiri

  Anya za a hallaka duniya? Littafin Mai-Wa’azi 1:4, ya ce duniya za “ta dawwama,” amma wasu suna ganin wannan ayar ta saba da wadda ta ce “duniya kuwa da ayyukan da ke cikinta za su kone.” (2 Bitrus 3:10) Amma, Littafi Mai Tsarki yakan yi amfani da kalmar nan “duniya” a zahiri da kuma a alamance. Idan ya yi amfani da kalmar a zahiri, to yana nufin duniya da kanta, amma idan a alamance ne, yana nufin mutanen da ke cikin duniya. (Farawa 1:1; 11:1) Hallakar duniya da aka yi maganarsa a littafin 2 Bitrus 3:10 tana nufin “halakar mutane masu fajirci” ne ba hallakar doron kasa ba.—2 Bitrus 3:7.

Ka’ida ta 5: Yin abu a madadin wasu

  Wane ne ya roki Yesu ya yi warkarwa a Kafarnahum? Littafin Matta 8:​5, 6 ya ce jarumin (shugaban sojoji) ya zo wurin Yesu da kansa, amma Luka 7:3 ta ce jarumin ya aiki dattawan Yahudawa su je su roki Yesu a madadinsa. Wannan ba sabani ba ne domin jarumin ne ya tura dattawan Yahudawan su je su yi roko a madadinsa.

Ka’ida ta 6: Fassarar da ta yi daidai

  Shin dukanmu masu zunubi ne? Littafi Mai Tsarki ya ce dukanmu mun gāji zunubi daga Adamu, mutum na farko. (Romawa 5:​12) Wasu ayoyi a cikin wasu juyin Littafi Mai Tsarki da suka ce mutum nagari “ba ya zunubi” sun saba da abin da aka ambata a nan. (1 Yohanna 3:6, The Bible in Basic English) Amma a asalin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita don “zunubi” a 1 Yohanna 3:6 tana nufin abu da ake yi a kai a kai. Akwai bambanci tsakanin zunubin da muka gāda da kuma zunubin ganganci da ake yi a kai a kai. Shi ya sa wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun bayyana bambancin dalla-dalla ta wajen yin amfani da jimlolin nan “ba ya aikata zunubi” ko kuma “ba ya ci gaba da yin zunubi.”—Juyin Littafi Mai Tsarki da kuma na Phillips.

Ka’ida ta 7: Mu bi koyarwar Littafi Mai Tsarki, ba koyarwar addinai ba

  Shin matsayin Yesu da Allah daya ne ko kuma Allah ya fi Yesu girma? Akwai lokacin da Yesu ya ce: “Ni da Ubana daya ne.” Za a iya dauka cewa wannan furucin ya saba wa wanda Yesu ya yi cewa “Uba ya fi ni girma.” (Yohanna 10:30; 14:28) Idan muna so mu fahimci ayoyin nan, wajibi ne mu bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da Jehobah da kuma Yesu maimakon mu yi kokarin sa ayoyin su jitu da koyarwar allah-uku-cikin daya, wadda ba koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ce. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah Uban Yesu ne kuma shi ne Allahn da Yesu yake bauta wa. (Matta 4:​10; Markus 15:34; Yohanna 17:3; 20:17; 2 Korintiyawa 1:3) Matsayin Yesu da Allah ba daya ba ne.

 Asalin batun da Yesu yake tattaunawa a nan a kan yadda nufinsa da na Ubansa, Jehobah, sun jitu ne, shi ya sa ya ce “ni da Ubana daya ne.” Daga baya Yesu ya ce: “ra’ayina da na Ubana ɗaya ne.” (Yohanna 10:38, New World Translation) Mabiyan Yesu ma suna bin wannan ra’ayin, shi ya sa Yesu ya yi addu’a ga Allah a madadinsu cewa: “Daukakar da ka yi mini, ita na yi musu, domin su zama daya kamar yadda muke daya.”—Yohanna 17:22, 23, Littafi Mai Tsarki.

a Alal misali, a cikin wani talifi a kan ginin Taj Mahal da aka rubuta a cikin Encyclopædia Britannica, an ce “sarki Mughal Shah Jahān ne ya gina.” Amma ba shi ne ya yi ginin da hannunsa ba, domin talifin ya nuna cewa “ma’aikata sama da 20,000 ne suka yi” ginin.