Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kyauta wa Karnukana

Kyauta wa Karnukana

WANI mutum mai suna Nick da ke zama a jihar Oregon na ƙasar Amirka, ya ce: “A farkon shekara ta 2014, na soma fita yawo da ƙananan karnukana guda biyu. Na haɗu da Shaidun Jehobah suna tsaye a tsakiyar birnin kusa da amalanken wa’azinsu kamar yadda suka saba. Suna sanye da riguna masu kyau kuma suna gai da kowa da kowa da fara’a.

“Ba mutane ne kaɗai Shaidun suka nuna wa alheri ba, sun ma nuna alheri ga karnukana. Wata rana, Elaine wadda take tsaye kusa da amalanken wa’azin ta ba wa karnukana biskit. Bayan hakan, a duk lokacin da muka je kusa da amalanken wa’azin, karnukan sukan maso kusa da ita don ta ba su biskit.

“A kwana a tashi, karnukana sun ci gaba da jin daɗin biskit ɗinsu, kuma ni ma na soma jin daɗin tattaunawa na ɗan lokaci da Shaidun. Amma ban so in riƙa tattaunawa da su sosai ba. A lokacin na riga na wuce shekaru 70, kuma ban san abin da Shaidun Jehobah suke koyarwa sosai ba. Da yake ban ji daɗin yadda wasu coci suke ba, sai na yanke shawara cewa zai dace in yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kaina.

“A wannan lokacin, na ga wasu Shaidu dabam a wasu wurare a birnin suna wa’azi da amalanke. Su ma suna fara’a sosai. Suna amsa duk wata tambaya da na yi musu daga Littafi Mai Tsarki kuma hakan ya sa na daɗa yarda da su.

“Wata rana, sai Elaine ta ce, ‘Ka gaskata cewa dabbobi kyauta ne daga Allah?’ Sai na ce ‘E na gaskata!’ Sai Elaine ta nuna min Ishaya 11:​6-9. Tun daga lokacin, sai na soma son in koyi abubuwa daga Littafi Mai Tsarki, amma na ci gaba da ƙin karɓan littattafansu.

“Na ji daɗin tattaunawa na gajeren lokaci da Elaine da kuma mijinta Brent. Sun shawarce ni in karanta littafin Matiyu zuwa Ayyukan Manzanni domin in san abin da zama Kirista ya ƙunsa. Na bi shawararsu, kuma bayan haka, sai na yarda Brent da Elaine su yi nazari da ni. Mun soma nazarin a tsakiyar shekara ta 2016.

“Nakan yi marmarin nazarin da muke yi da kuma taron ikilisiya a kowane mako. Na yi farin cikin koyan abin da ke Littafi Mai Tsarki. Jim kaɗan bayan shekara ɗaya, sai na yi baftisma. Shekaruna 79 a yanzu, kuma ina farin ciki cewa na sami addini na gaskiya. Jehobah ya yi mini albarka ta wajen saka ni a cikin iyalinsa da ke bauta masa a duk faɗin duniya.”