Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 12

Yaya Ake Tsara Wa’azin da Muke Yi Game da Mulki?

Yaya Ake Tsara Wa’azin da Muke Yi Game da Mulki?

Sifen

Belarus

Hong Kong

Peru

Gab da mutuwarsa, Yesu ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14) Amma ta yaya za a cim ma wa’azin nan a faɗin duniya? Ta wajen bin misalin da Yesu ya kafa sa’ad da yake duniya.—Luka 8:1.

Muna yi wa mutane wa’azi a gidajensu. Yesu ya koya wa almajiransa su bi gida-gida suna bishara. (Matta 10:11-13; Ayyukan Manzanni 5:42; 20:20) An ba masu wa’azi a ƙarni na farko yankunan da za su yi wa’azi. (Matta 10:5, 6; 2 Korintiyawa 10:13) Hakazalika, a yau wa’azin da muke yi yana da tsari sosai, kuma an ba kowace ikilisiya yankin da za ta yi wa’azi. Hakan yana taimaka mana mu cika umurnin da Yesu ya ba mu na yi wa “jama’a wa’azi” kuma mu gaya musu abin da ya ce dalla-dalla.—Ayyukan Manzanni 10:42.

Muna yin wa’azi a duk inda mutane suke. Har ila, Yesu ya kafa misali na yin wa’azi a duk inda mutane suke, kamar su bakin teku ko kuma wurin da ake ɗiban ruwa. (Markus 4:1; Yohanna 4:5-15) Mu ma muna tattaunawa da mutane a duk inda muka gan su, a kan titi da wuraren kasuwanci da wuraren shaƙatawa ko kuma ta hanyar tarho. Muna kuma yi wa maƙwabtanmu wa’azi da abokan aikinmu da ’yan ajinmu da dangoginmu a lokacin da muka samu damar yin hakan. Wannan ƙoƙarin da muke yi ya sa miliyoyin mutane a faɗin duniya sun ji ‘labarin ceto.’—Zabura 96:2.

Akwai wanda kake ganin za ka iya gaya wa wannan bishara ta Mulkin Allah da kuma yadda za ta shafi rayuwarsa a nan gaba? Kada ka yi gum da wannan saƙon na bege. Ka gaya wa mutane wannan saƙon!

  • Wajibi ne mu yi wace “bishara”?

  • Ta yaya Shaidun Jehobah suke yin wa’azi kamar yadda Yesu ya yi?