Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA TAKWAS

Menene Mulkin Allah?

Menene Mulkin Allah?
  • Menene Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da Mulkin Allah?

  • Menene Mulkin Allah zai yi?

  • Yaushe ne Mulkin zai sa a yi nufin Allah a duniya?

1. Wace fitacciyar addu’a ce za a bincika a yanzu?

MILIYOYIN mutane a dukan duniya suna sane da addu’ar da yawanci suke kira Ubanmu, ko kuma Addu’ar Ubangiji. Waɗannan furci biyu suna magana ne game da fitacciyar addu’ar da Yesu Kristi kansa ya yi na kwatanci. Addu’a ce mai ma’ana ƙwarai, bincika abubuwa uku da ya roƙa da fari za ta taimake mu mu koyi abin da ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.

2. Menene abubuwa uku daga cikin abin da Yesu ya koya wa almajiransa su roƙa a addu’a?

2 A farkon addu’ar kwatanci, Yesu ya umurci masu sauraronsa: “Da hakanan fa za ku yi addu’a: Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo, abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin Sama.” (Matta 6:9-13) Menene muhimmancin waɗannan roƙo guda uku?

3. Me muke bukata mu sani game da Mulkin Allah?

3 Mun riga mun fahimci abubuwa da yawa game da sunan Allah, Jehobah. Kuma mun tattauna game da nufin Allah—abin da ya yi da kuma waɗanda zai yi ga ’yan adam. Amma, me Yesu yake magana a kai sa’ad da ya gaya mana mu yi addu’a: “Mulkinka shi zo”? Menene Mulkin Allah? Ta yaya zuwansa zai tsarkake sunan Allah? Kuma ta yaya zuwan Mulkin yake da nasaba da yin nufin Allah?

ABIN DA MULKIN ALLAH YAKE NUFI

4. Menene Mulkin Allah, kuma waye ne Sarkin?

4 Mulkin Allah gwamnati ne da Jehobah Allah ya kafa kuma ya zaɓa masa Sarki. Wanene Sarkin Mulkin Allah? Yesu Kristi. Sarki Yesu ya fi dukan sarakuna mutane saboda haka aka kira shi “Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.” (1 Timothawus 6:15) Yana da ikon ya yi alheri fiye da dukan wani sarki mutum, har ma mafi kirki a tsakaninsu.

5. Daga ina Mulkin Allah zai yi sarauta, kuma a kan waye?

5 Daga ina ne Mulkin Allah zai yi sarauta? To, a ina Yesu yake? Ka tuna ka koyi cewa an kashe shi a kan gungumen azaba, sai kuma aka tashe shi daga matattu. Ba da daɗewa ba bayan haka, ya koma sama. (Ayukan Manzanni 2:33) Saboda haka, a nan ne Mulkin Allah yake—a sama. Abin da ya sa ke nan Littafi Mai Tsarki ya kira shi ‘Mulkin sama.’ (2 Timothawus 4:18) Ko da yake Mulkin Allah yana sama, zai mallaki duniya.—Ru’ya ta Yohanna 11:15.

6, 7. Menene ya sa Yesu ya zama Sarki na musamman?

6 Menene ya sa Yesu ya zama Sarki na musamman? Dalili ɗaya shi ne, ba zai mutu ba. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki yake kwatanta Yesu da sarki ɗan adam, ya ce “shi kaɗai yana da rashin mutuwa, mazauni cikin haske wanda ba shi kusantuwa.” (1 Timothawus 6:16) Wannan yana nufin cewa dukan alherin da Yesu zai yi zai dawwama. Kuma zai yi manyan abubuwa nagari.

7 Ka yi la’akari da wannan annabci na Littafi Mai Tsarki game da Yesu: “Ruhun Ubangiji za ya zauna bisansa, ruhun ilimi da na ganewa, ruhun shawara da iko, ruhun sani da na tsoron Ubangiji: jin daɗinsa kuma za ya kasance a cikin tsoron Ubangiji: ba za ya yi shari a bisa ga abin da ya bayyana ga idanunsa ba, ba kuwa za shi yanka magana bisa ga abin da kunnensa ke ji ba: amma da adalci za ya yi ma talakawa shari’a, da daidaita kuma za ya yanka magana domin masu-tawali’u na duniya.” (Ishaya 11:2-4) Waɗannan kalmomin sun nuna cewa Yesu zai kasance Sarki mai adalci mai juyayi bisa mutanen duniya. Za ka so ka sami sarki kamar haka?

8. Waye zai yi mulki da Yesu?

8 Da wani abu kuma game da Mulkin Allah: Yesu ba zai yi sarauta shi kaɗai ba. Zai kasance da abokan sarauta. Alal misali, manzo Bulus ya gaya wa Timothawus: “Idan mun jimre, za mu kuma yi mulki tare da shi.” (2 Timothawus 2:12) Hakika, Bulus, Timothawus, da wasu masu aminci da Allah ya zaɓa za su yi sarauta tare da Yesu a Mulkin sama. Mutane nawa ne za su sami wannan gatar?

9. Mutane nawa ne za su yi sarauta tare da Yesu, kuma yaushe Allah ya fara zaɓansu?

9 Kamar yadda aka nuna a Babi na 7 na wannan littafin, an bai wa manzo Yohanna wahayi da ya ga “Ɗan ragon [Yesu Kristi] yana tsaye bisa dutsen Sihiyona [matsayinsa na sarauta a sama], tare da shi kuma mutum zambar ɗari da zambar arba’in da huɗu, suna da sunansa, da sunan Ubansa, a rubuce bisa goshinsu.” Su waye ne waɗannan 144,000? Yohanna da kansa ya gaya mana: Su ne kan bi Ɗan Rago inda ya tafi duka. Aka fanshi waɗannan daga cikin mutane, su zama nunan fari ga Allah da Ɗan Rago.” (Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4) Hakika, mabiyan Yesu Kristi ne masu aminci da aka zaɓa musamman su yi sarauta tare da shi a sama. Bayan an ta da su daga matattu zuwa rayuwa ta sama, za su kuwa yi “mulki bisa duniya” tare da Yesu. (Ru’ya ta Yohanna 5:10) Tun daga zamanin manzanni, Allah ya yi ta zaɓan Kiristoci masu aminci domin su cika wannan adadi na 144,000.

10. Me ya sa ƙauna ce shirin da aka yi Yesu da mutane 144,000 su yi sarauta bisa ’yan adam?

10 Shirin da aka yi domin Yesu da mutane 144,000 su yi sarauta bisa ’yan adam ƙauna ce. Dalili guda shi ne, Yesu ya san wahalar mutane. Bulus ya ce Yesu ba “wanda ba shi taɓuwa da tarayyar kumamancinmu ba: amma wanda an jarabce shi a kowace fuska kamarmu, sai dai banda zunubi.” (Ibraniyawa 4:15; 5:8) Abokanan sarautarsa ma sa’ad da suke mutane sun wahala kuma sun jure. Ƙari ga haka, sun yi fama da ajizanci kuma sun jimre wa dukan ire-iren cututtuka. Hakika, za su fahimci matsaloli da mutane suke fuskanta!

MENENE MULKIN ALLAH ZAI YI?

11. Me ya sa Yesu ya ce wa almajiransa su yi addu’a a yi nufin Allah a sama?

11 Sa’ad da Yesu ya ce wa almajiransa su yi addu’a Mulkin Allah ya zo, ya kuma ce su yi addu’a a yi nufin Allah “cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” Allah a sama yake, kuma a kullum mala’iku masu aminci suna yin nufinsa. A Babi na 3 na wannan Littafin, mun koyi cewa wani mugun mala’ika ya daina yin nufin Allah kuma ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi. A Babi na 10, za mu sami ƙarin bayani game da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da wannan mugun mala’ika, da muka sani da Shaiɗan Iblis. Shaiɗan da kuma wasu mala’iku da suka zaɓi su bi shi—da ake kira aljannu—an ƙyale su su zauna a sama na ɗan lokaci. Saboda haka, ba duka ba ne suke yin nufin Allah a sama a lokacin. Haka ba zai kasance ba sa’ad da Mulkin Allah ya fara sarauta. Sabon Sarki da aka naɗa, Yesu Kristi, zai yaƙi Shaiɗan.—Ru’ya ta Yohanna 12:7-9.

12. Waɗanne aukuwa biyu ne masu muhimmanci aka kwatanta a Ru’ya ta Yohanna 12:10?

12 Waɗannan kalmomi na annabci sun kwatanta abin da zai faru: “Na ji babbar murya kuma cikin sama, ta ce, Yanzu ceto, da iko, da mulkin Allahnmu ya zo, da sarautar Kristinsa kuma: gama an jefarda mai-saran ’yan’uwanmu, shi wanda ya ke sararsu dare da rana a gaban Allahnmu.” (Ru’ya ta Yohanna 12:10) Ka lura da aukuwa biyu masu muhimmanci da aka kwatanta a wannan ayar Littafi Mai Tsarki? Na farko, Mulkin Allah a hannun Yesu Kristi ya fara sarauta. Na biyu, an jefo Shaiɗan daga sama zuwa duniya.

13. Menene sakamakon jefo Shaiɗan daga sama?

13 Menene sakamakon waɗannan aukuwa biyu? Game da abin da ya faru a sama, mun karanta: “Domin wannan fa, ku yi farinciki, ya sammai, da ku mazauna a ciki.” Hakika, mala’iku masu aminci a sama sun yi farin ciki domin Shaiɗan da aljannunsa ba sa sama kuma, kowa a sama mai aminci ne ga Jehobah Allah. Sun sami cikakken salama da jituwa. Ana yin nufin Allah a sama.

Jefo Shaiɗan da aljannunsa daga sama ya jawo matsifu ga duniya. Irin waɗannan matsifun za su ƙare ba da ɗaɗewa ba

14. Menene ya faru domin an jefo Shaiɗan zuwa duniya?

14 To, duniya kuma fa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kaiton duniya da teku: domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Shaiɗan yana fushi domin an jefo shi daga sama kuma lokacinsa ya ƙure. A cikin fushinsa yana haddasa matsaloli, ko kuma ‘kaito,’ ga duniya. Za mu sami ƙarin bayani game da “kaiton” a babi na gaba. Amma da tunanin wannan, za mu iya tambaya, Ta yaya Mulkin zai sa a yi nufin Allah a duniya?

15. Menene nufin Allah ga duniya?

15 To, ka tuna nufin Allah ga duniya. Ka koyi game da wannan a Babi na 3. A Adnin, Allah ya nuna cewa nufinsa ne duniya ta zama aljanna cike da mutane masu adalci marasa mutuwa. Shaiɗan ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, wannan ya jinkirta cikan nufin Allah ga duniya amma bai canja shi ba. Har yanzu Jehobah ya nufa cewa “masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” (Zabura 37:29) Kuma Mulkin Allah zai cim ma wannan. A wace hanya?

16, 17. Menene Daniel 2:44 ta gaya mana game da Mulkin Allah?

16 Ka yi la’akari da annabci da ke Daniel 2:44. A nan mun karanta: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” Menene wannan ya gaya mana game da Mulkin Allah?

17 Da fari, ya gaya mana cewa za a kafa Mulkin Allah a “cikin zamanin waɗannan sarakuna” ko kuma sa’ad da wasu mulkoki suke sarauta. Na biyu, ya gaya mana cewa Mulkin za ya tsaya har abada. Kuma ba za a yi nasara a kansa ba ko kuma a sake shi da wasu gwamnatoci. Na uku, mun ga cewa za a yi yaƙi tsakanin Mulkin Allah da mulkokin duniya. Mulkin Allah zai yi nasara. A ƙarshe zai zama shi ne kaɗai gwamnati a kan ’yan adam. Sa’an nan mutane za su more sarauta mafi kyau.

18. Menene sunan yaƙin ƙarshe tsakanin Mulkin Allah da gwamnatocin duniya?

18 Littafi Mai Tsarki yana da abubuwa da yawa da zai ce game da wannan yaƙi na ƙarshe tsakanin Mulkin Allah da gwamnatocin duniya. Alal misali, ya koyar da cewa sa’ad da ƙarshe ya yi kusa, miyagun ruhu za su yaɗa ƙarya domin su yaudari “sarakunan dukan duniya.” Domin menene? “Garin su tattara su zuwa yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” Sarakunan duniya za a tattara su a “wurin da a ke ce da shi da Ibrananci Har–Magedon.” (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Domin abin da aka ce a waɗannan ayoyi biyu, yaƙi na ƙarshe tsakanin gwamnatocin mutane da Mulkin Allah ana kiransa yaƙin Har–Magedon ko Armagedon.

19, 20. Me yake hana yin nufin Allah a duniya a yanzu?

19 Menene Mulkin Allah zai cim ma ta wajen Armagedon? Ka sake tunani game da nufin Allah ga duniya. Nufin Jehobah Allah shi ne duniya ta cika da mutane masu adalci, kamilai da suke bauta masa a cikin Aljanna. Menene ya hana wannan daga faruwa a yanzu? Na farko, muna masu zunubi, kuma muna rashin lafiya muna mutuwa. Mun koya a Babi na 5, cewa Yesu ya mutu dominmu, saboda mu rayu har abada. Wataƙila, ka tuna da kalaman da ke rubuce a Linjilar Yohanna: “Gama Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.”—Yohanna 3:16.

20 Wani dalili kuma shi ne cewa mutane suna aikata mugunta. Suna ƙarya, suna cuta, kuma suna yin lalata. Ba sa so su yi nufin Allah. Mutane da suke yin miyagun abubuwa za a halaka su a lokacin yaƙin Allah na Armagedon. (Zabura 37:10) Wani dalili kuma da ya sa ba a yin nufin Allah a duniya shi ne cewa gwamnatoci ba sa ƙarfafa mutane su yi shi. Wasu gwamnatoci suna da rauni, wasu kuma azzalumai ne, ko kuma malalata. Littafi Mai Tsarki ya faɗa kai tsaye: “Mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya ciwuce shi.”—Mai-Wa’azi 8:9.

21. Ta yaya Mulkin zai sa a yi nufin Allah a duniya?

21 Bayan Armagedon, ’yan adam za su kasance a ƙarƙashin gwamnati guda kawai, wato Mulkin Allah. Wannan Mulkin zai yi nufin Allah kuma zai kawo albarkatai masu ban sha’awa. Alal misali, zai kawar da Shaiɗan da aljannunsa. (Ru’ya ta Yohanna 20:1-3) Za a yi amfani da ikon hadayar Yesu, saboda mutane masu aminci kada su ƙara yin ciwo ko kuma su mutu. Maimakon haka, a ƙarƙashin sarautar Mulki za su rayu har abada. (Ru’ya ta Yohanna 22:1-3) Za a mai da duniya ta zama aljanna. Ta haka Mulkin zai sa a yi nufin Allah a duniya, kuma zai tsarkake sunan Allah. Menene wannan yake nufi? Wannan yana nufin cewa a ƙarshe dukan waɗanda suke ƙarƙashin Mulkin Allah za su ɗaukaka sunan Jehobah.

YAUSHE MULKIN ALLAH ZAI SA A YI NUFINSA A DUNIYA?

22. Ta yaya muka sani cewa Mulkin Allah bai zo ba sa’ad da Yesu yake duniya ko kuma nan da nan bayan tashinsa daga matattu?

22 Sa’ad da Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi addu’a, “Mulkin ka shi zo,” a bayyane yake cewa Mulkin bai zo ba tukuna a lokacin. Ya zo ne sa’ad da Yesu ya koma sama? A’a, domin Bitrus da Bulus suka ce bayan tashin Yesu daga matattu, annabcin da ke Zabura 110:1 ta cika a kansa: “Ubangiji ya ce ma ubangijina, Ka zauna ga hannun damana, har in maida maƙiyanka matashin sawunka.” (Ayukan Manzanni 2:32-34; Ibraniyawa 10:12, 13) Da akwai lokacin jira.

A ƙarƙashin sarautar Mulkin, za a yi nufin Allah a duniya kamar yadda ake yi a sama

23. (a) Yaushe Mulkin Allah ya fara sarauta? (b) Menene za a tattauna a babi na gaba?

23 Yaya tsawon lokacin jiran? A ƙarni na 19, tun lokacin da ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka lissafa tsawon lokacin jiran, zai ƙare a shekara ta 1914. (Game da wannan kwanan wata, dubi Rataye, shafi na 215-218.) Abubuwa da suke aukuwa a duniya tun daga shekara ta 1914 sun tabbatar da cewa lissafin waɗannan ɗaliban Littafi Mai Tsarki daidai ne. Cikan annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a shekara ta 1914, Kristi ya zama Sarki kuma Mulkin Allah na sama ya fara sarauta. Saboda haka, muna rayuwa ne a lokacin “kaɗan” da ya rage wa Shaiɗan. (Ru’ya ta Yohanna 12:12; Zabura 110:2) Kuma za mu iya cewa da tabbaci ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai sa a yi nufin Allah a duniya. Wannan ya kasance labari ne mai ban mamaki a gare ka? Ka gaskata cewa gaskiya ne? Babi na gaba zai taimake ka ka ga cewa da gaske Littafi Mai Tsaki ya koyar da waɗannan abubuwa.