Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 15

Yaya Dattawa Suke Hidima a Ikilisiya?

Yaya Dattawa Suke Hidima a Ikilisiya?

Finland

Koyarwa

Ziyarar ƙarfafawa

Yin wa’azi

Ba mu da limaman da ake biya albashi a ƙungiyarmu. A maimakon haka, kamar yadda aka yi a dā sa’ad da aka kafa ikilisiyar Kirista, muna da dattawan da suka cancanta, waɗanda aka naɗa don su “yi kiwon ikilisiyar Allah.” (Ayyukan Manzanni 20:28) Waɗannan dattawan mutane ne da suke da dangantaka mai kyau da Allah, kuma suna yi wa ikilisiya ja-gora ‘ba da tilas ba, amma da yardan rai, bisa ga nufin Allah; ba kuwa domin riba mai-ƙazanta ba.’ (1 Bitrus 5:1-3) Wane aiki ne suke yi a madadin mu?

Suna kula da mu kuma suna kāre mu. Dattawa suna amfani da nassi su yi mana ja-gora kuma suna taimaka wa ikilisiya ta ci gaba da kusantar Jehobah. Domin sun san cewa Allah ne ya ba su hakkin kula da mutanensa, dattawa ba sa juya mu yadda suka ga dama, a maimakon haka, suna kula da mu kuma suna sa mu farin ciki. (2 Korintiyawa 1:24) Kamar yadda makiyayi yake kula sosai da tumakinsa, dattawa suna ƙoƙartawa su san kowane mutumin da ke cikin ikilisiya.

Suna koya mana yadda za mu yi nufin Allah. A kowane mako, dattawa suna ja-gorantar taron da ake yi a ikilisiya don su ƙarfafa bangaskiyarmu. (Ayyukan Manzanni 15:32) Saboda ƙwazonsu, suna kan gaba wajen yin wa’azi, suna fita wa’azi tare da mu kuma suna nuna mana hanyoyi dabam-dabam da za mu bi mu yi wa’azi.

Suna ƙarfafa kowanenmu. Domin su taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, dattawan da ke ikilisiyarmu suna iya tattaunawa da mu a gidanmu ko a Majami’ar Mulki ta wajen yin amfani da Nassi.—Yaƙub 5:14, 15.

Ƙari ga hidimar da suke yi a cikin ikilisiya, yawancin dattawan nan suna da aikin da suke yi, kuma suna bukatar su kula da iyalinsu, hakan yana bukatar lokacinsu da kuma kulawarsu. ’Yan’uwan nan da suke hidima da ƙwazo sun cancanci mu daraja su.—1 Tasalonikawa 5:12, 13.

  • Wane aiki ne dattawa suke yi a cikin ikilisiya?

  • A waɗanne hanyoyi ne dattawa suke nuna cewa suna kula da kowannenmu?