Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA TAKWAS

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah
  • Ta yaya ake yin baftisma na Kirista?

  • Waɗanne matakai kake bukatar ka ɗauka domin ka cancanci yin baftisma?

  • Ta yaya mutum yake keɓe kansa ga Allah?

  • Menene dalili na musamman na yin baftisma?

1. Me ya sa Bahabashe ma’aikacin kotu ya roƙi a yi masa baftisma?

“GA RUWA! Me za ya hana a yi mini baftisma?” Tambayar da Bahabashe ma’aikacin kotu ya yi ke nan a ƙarni na farko. Wani Kirista mai suna Filib ya tabbatar masa cewa Yesu shi ne Almasihu. Da abin da ya koya daga Nassosi suka motsa zuciyarsa, sai Bahabashen ya ɗauki mataki. Ya nuna cewa yana so a yi masa baftisma!—Ayukan Manzanni 8:26-36.

2. Me ya sa za ka yi tunani da kyau game da baftisma?

2 Idan ka yi nazarin babunan baya na wannan littafi da kyau da wani Mashaidin Jehobah, kana iya jin ya kai ka yi tambaya, ‘Me za ya hana a yi mini baftisma?’ A yanzu ka riga ka koyi game da alkawarin Littafi Mai Tsarki na rai madawwami a Aljanna. (Luka 23:43; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Kuma ka koyi game da yanayin gaske na matattu da kuma begen tashin matattu. (Mai-Wa’azi 9:5; Yohanna 5:28, 29) Wataƙila kana tarayya da Shaidun Jehobah a taron ikilisiyarsu kuma ka gani da idanunka yadda suke yin addini na gaskiya. (Yohanna 13:35) Mafi muhimmanci ma, wataƙila ka fara ƙulla dangantaka da Jehobah Allah.

3. (a) Wane umurni ne Yesu ya ba wa mabiyansa? (b) Yaya ake yin baftisma na ruwa?

3 Ta yaya za ka nuna cewa kana so ka bauta wa Allah? Yesu ya gaya wa mabiyansa: ‘Ku tafi ku almajirtadda dukkan al’ummai, kuna yi masu baftisma.’ (Matta 28:19) Yesu kansa ya kafa misali ta wajen yin baftisma cikin ruwa. Ba a yafa masa ruwa ba, ba kuwa zuba masa ruwa kawai a ka ba. (Matta 3:16) Kalmar nan “baftisma” daga Hellenanci ce tana nufin “tsoma.” Saboda haka, baftisma na Kiristoci tana nufin a tsoma, ko kuma a nutsa cikin ruwa.

4. Menene baftisma cikin ruwa yake nufi?

4 Baftisma cikin ruwa bukata ce ga dukan waɗanda suke so su ƙulla dangantaka da Jehobah Allah. Yin baftisma a fili yana nuna muradinmu na bauta wa Allah. Yana nuna cewa kana farin ciki ka yi nufin Jehobah. (Zabura 40:7, 8) Domin ka cancanci baftisma, dole ne ka ɗauki wasu matakai.

ANA BUKATAR SANI DA KUMA BANGASKIYA

5. (a) Menene mataki na ɗaya domin cancanta don baftisma? (b) Me ya sa tarurruka na Kirista suke da muhimmanci?

5 Ka riga ka fara ɗaukan mataki na farko. Ta yaya? Ta wajen neman sanin Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi ta nazarin Littafi Mai Tsarki a tsanake. (Yohanna 17:3) Amma da abubuwa da yawa na koyo har yanzu. Kiristoci suna so a cika su da ‘sanin nufin’ Allah. (Kolossiyawa 1:9) Halartar tarurruka a ikilisiya na Shaidun Jehobah zai yi taimako a wannan. Yana da muhimmanci a halarci irin waɗannan tarurruka. (Ibraniyawa 10:24, 25) Halartar taro a kai a kai zai taimake ka ka ƙara saninka na Allah.

Samun cikakken sani na Kalmar Allah mataki ne mai muhimmanci domin cancanta ga baftisma

6. Yaya yawan ilimin Littafi Mai Tsarki da kake bukata domin ka cancanci yin baftisma?

6 Hakika, ba ka bukatar sanin dukan abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki kafin ka cancanci a yi maka baftisma. Bahabashen ma’aikacin kotu yana da ɗan sani, amma ya bukaci taimako domin ya fahimci wasu ɓangarori na Nassosi. (Ayukan Manzanni 8:30, 31) Hakazalika, za ka bukaci ka koyi abubuwa masu yawa. Hakika, ba za ka taɓa daina koyo game da Allah ba. (Mai-Wa’azi 3:11) Amma, kafin a yi maka baftisma, kana bukatar ka sani kuma ka gaskata muhimman koyarwa na Littafi Mai Tsarki. (Ibraniyawa 5:12) Irin waɗannan koyarwa sun haɗa da gaskiya game da yanayin matattu da kuma muhimmancin sunan Allah da kuma Mulkinsa.

7. Yaya ya kamata yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya shafe ka?

7 Sani kawai bai isa ba, domin “ba shi kuwa yiwuwa a gamshe [Allah] ba sai tare da bangaskiya.” (Ibraniyawa 11:6) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa wasu mutane a birnin Koranti na dā suka saurari saƙon Kiristoci, suka “bada gaskiya, aka yi musu baftisma.” (Ayukan Manzanni 18:8) Hakanan a yau, nazarin Littafi Mai Tsarki ya kamata ya cika ka da bangaskiya cewa lalle Kalmar Allah ce hurarriya. Nazarin Littafi Mai Tsarki ya kamata ya taimake ka ka gaskata alkawuran Allah da kuma ikon ceto na hadayar Yesu.—Joshua 23:14; Ayukan Manzanni 4:12; 2 Timothawus 3:16, 17.

KA SANAR DA MUTANE GASKIYAR LITTAFI MAI TSARKI

8. Mecece za ta motsa ka ka gaya wa wasu abin da ka koya?

8 Sa’ad da bangaskiya ta cika zuciyarka, zai yi maka wuya ka rufe bakinka ka ƙi faɗar abin da ka koya. (Irmiya 20:9) Za ta motsa ka ka gaya wa mutane game da Allah da kuma nufinsa.—2 Korinthiyawa 4:13.

Bangaskiya ya kamata ta motsa ka ka gaya wa mutane abin da ka gaskata

9, 10. (a) Ga wa za ka iya fara sanar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki? (b) Menene za ka yi idan kana so ka yi aikin wa’azi da Shaidun Jehobah?

9 Za ka iya fara gaya wa wasu game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki cikin basira ta wajen yin magana game da ita ga danginka, abokananka, maƙwabta, da kuma abokan aiki. Bayan wani lokaci, za ka so ka fara aikin wa’azi da Shaidun Jehobah. A wannan lokaci, kana iya tattauna batun da Mashaidin da ya koya maka gaskiya ta Littafi Mai Tsarki. Idan ka cancanci ka fita wa’azi na fage, za a yi shiri kai da malaminka ku sadu da dattawan ikilisiya.

10 Wannan zai taimaka maka ka san wasu dattawa Kiristoci, waɗanda suke kiwon garken Allah. (Ayukan Manzanni 20:28; 1 Bitrus 5:2, 3) Idan waɗannan dattawa suka fahimci cewa kana da muhimman sani na Littafi Mai Tsarki, kuma kana rayuwa cikin jituwa da mizanan Allah, kuma da gaske kana so ka zama Mashaidin Jehobah, za su sanar da kai cewa ka cancanci ka fita hidimar fage ka zama mai shela da bai yi baftisma ba.

11. Waɗanne canje-canje wasu za su bukaci su yi domin su cancanci fita wa’azi?

11 A wani ɓangare kuma, wataƙila ka bukaci ka yi wasu canje-canje a hanyoyin rayuwarka ko halayenka domin ka cancanci fita wa’azi. Waɗannan za su haɗa da wasu ayyuka da kake yi a ɓoye. Hakika, kafin ka ce za ka zama mai shela da bai yi baftisma ba, kana bukatar ka rabu da yin zunubai masu tsanani, kamar su lalata, maye, da shan miyagun ƙwayoyi.—1 Korinthiyawa 6:9, 10; Galatiyawa 5:19-21.

TUBA DA JUYOWA

12. Me ya sa tuba ta wajaba?

12 Dole ne a ɗauki wasu matakai kafin a cancanci yin baftisma. Manzo Bitrus ya ce: “Ku tuba fa, ku juyo, domin a shafe zunubanku.” (Ayukan Manzanni 3:19) Tuba yin nadama ne matuƙa domin wani abin da ka yi. Tuba ta dace idan mutum ya yi rayuwa ta lalata, kuma dole ne ko da mutum ya yi rayuwa mai tsabta. Me ya sa? Domin dukan mutane masu zunubi ne kuma muna bukatar gafarar Allah. (Romawa 3:23; 5:12) Kafin ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki, ba ka san ko menene nufin Allah ba. Saboda haka, ba zai yiwu ka rayu cikin cikakkiyar jituwa da nufinsa ba. Domin haka, tuba ta wajaba.

13. Menene juyowa?

13 Dole ne kuma juyowa ya bi tuba. Dole ne ka yi abin da ya fice nadama kawai. Kana bukatar ka guji irin rayuwarka ta dā kuma ka ƙuduri niyyar yin abin da yake nagari daga yanzu har zuwa gaba. Tuba da juyowa matakai ne da dole ka ɗauka kafin ka yi baftisma.

KEƁE KANKA

14. Wane mataki ne mai muhimmanci dole ne ka ɗauka kafin ka yi baftisma?

14 Da wani mataki mai muhimmanci da za ka ɗauka kafin ka yi baftisma. Dole ne ka keɓe kanka ga Jehobah Allah.

Ka keɓe kanka ga Allah kuwa cikin addu’a?

15, 16. Menene yake nufi ka keɓe kanka ga Allah, kuma menene yake motsa mutum ya yi haka?

15 Sa’ad da ka keɓe kanka ga Jehobah Allah a cikin addu’a, ka yi masa alkawari ne cewa za ka bauta masa shi kaɗai har abada. (Kubawar Shari’a 6:15) Me ya sa, mutum zai so ya yi haka? Alal misali, a ce wani mutum yana neman wata yarinya da aure. Da zarar ya fahimci tana da halin kirki, hakan nan zai ci gaba da sha’awarta. Bayan wani ɗan lokaci, zai ce zai aure ta. Hakika, yin aure yana nufin zai ƙara hakkin da zai ɗauka a gare ta. Amma ƙauna za ta motsa shi ya ɗauki wannan hakkin.

16 Sa’ad da ka fahimci kuma ka ƙaunaci Jehobah, za ka motsa ka bauta masa ba tare da ja da baya ba ko kuma kafa wani iyaka ga bautarsa. Duk wanda yake so ya bi Ɗan Allah, Yesu Kristi, dole ne ya yi “musun kansa.” (Markus 8:34) Muna musun kanmu ta wajen tabbata cewa babu wani muradinmu ko kuma makasudi da ya tare hanyar yi wa Allah cikakkiyar biyayya. Kafin a yi maka baftisma yin nufin Allah dole ne ya kasance ainihin ma’anar rayuwarka.—1 Bitrus 4:2.

CIM MA TSORON KASAWA

17. Me ya sa wasu suke ƙin keɓe kansu ga Allah?

17 Wasu suna ƙin keɓe kansu ga Jehobah domin suna tsoron ɗaukan irin wannan mataki mai muhimmanci. Suna iya tsoron ba da lissafi ga Allah domin sun keɓe kansu sun zama Kiristoci. Suna tsoron kada su gaza su ba Jehobah kunya, suna tunanin cewa ya fi kada su keɓe masa kansu.

18. Menene zai motsa ka ka keɓe kanka ga Jehobah?

18 Sa’ad da ka koyi ka ƙaunaci Jehobah, za ka motsa ka keɓe masa kanka kuma ka yi iya ƙoƙarinka ka cika wannan. (Mai-Wa’azi 5:4) Bayan ka keɓe masa kanka, tabbatacce ne za ka so ka ‘cancanci bautar Ubangiji, kana faranta masa ta kowane fanni.’ (Kolossiyawa 1:10) Domin ƙaunarka ga Allah, ba za ka yi tunanin cewa yana da wuya a yi nufinsa ba. Babu shakka za ka yarda da abin da manzo Yohanna, ya rubuta: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa; dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.”—1 Yohanna 5:3.

19. Me ya sa bai kamata ka ji tsoron keɓe kanka ga Allah ba?

19 Ba dole sai ka kamilta ba kafin ka keɓe kanka ga Allah. Jehobah ya san kasawarka kuma ba ya bukatar ka yi abin da ba za ka iya yi ba. (Zabura 103:14) Yana so ka yi nasara kuma zai tallafa maka kuma ya taimake ka. (Ishaya 41:10) Ka tabbata cewa idan ka dogara ga Jehobah da dukan zuciyarka, shi kuma “za ya daidaita hanyoyinka.”—Misalai 3:5, 6.

KA NUNA KEƁE KANKA TA WAJEN BAFTISMA

20. Me ya sa keɓe kai ga Jehobah ba zai ci gaba da kasancewa abin sirri ba?

20 Tuna abin da muka tattauna yanzu zai taimake ka ka keɓe kanka ga Jehobah cikin addu’a. Duk wanda yake ƙaunar Allah dole ne ‘da baki ya yi shaida zuwa ceto.’ (Romawa 10:10) Ta yaya za ka yi wannan?

Baftisma tana nufin mutuwa a hanyar rayuwarka ta dā da kuma kasancewa a raye domin yin nufin Allah

21, 22. Taya za ka ‘yi shaidar’ bangaskiyarka?

21 Ka sanar da shugaban dattawa na ikilisiyarku cewa kana so ka yi baftisma. Zai shirya wasu dattawa su maimaita wasu tambayoyi game da koyarwa masu muhimmanci na Littafi Mai Tsarki. Idan waɗannan dattawa sun yarda cewa ka cancanta, za su gaya maka cewa za ka yi baftisma sa’ad da zarafi ya samu. * Ana ba da jawabi da yake ba da bayani game da ma’anar baftisma a irin wannan lokaci. Sai mai jawabin ya gayyaci dukan waɗanda suke da niyyar baftisma su amsa tambayoyi biyu masu sauƙi, wannan hanya ce ta ‘shaidar’ bangaskiyarsu.

22 Baftismar ce take nuna a fili cewa kai mutum ne da ya keɓe kansa ga Allah kuma a yanzu ka zama Mashaidin Jehobah. Ana nitsar da masu niyyar baftisma cikin ruwa su nuna a fili sun keɓe kansu ga Jehobah.

MA’ANAR BAFTISMARKA

23. Menene ake nufi a yi baftisma da “sunan Uban, da na Ɗa, da na Ruhu Mai-Tsarki”?

23 Yesu ya ce za a yi wa mabiyansa baftisma da “sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai-Tsarki.” (Matta 28:19) Wannan yana nufin cewa wanda yake da niyyar baftisma ya fahimci ikon Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi. (Zabura 83:18; Matta 28:18) Kuma ya fahimci matsayi da kuma ayyukan ruhu mai tsarki na Allah, ko kuma ikon aikinsa.—Galatiyawa 5:22, 23; 2 Bitrus 1:21.

24, 25. (a) Baftisma alamar menene ne? (b) Wace tambaya ce take bukatar amsa?

24 Amma, baftisma ba wanka ba ne kawai. Alama ce ta wani abu mai muhimmanci. Nitsewa cikin ruwa alama ce ta cewa ka mutu ga hanyar rayuwarka ta dā. Fito da kai daga cikin ruwa yana nuna cewa yanzu kana raye domin ka yi nufin Allah. Ka tuna kuma cewa ka keɓe kanka ga Jehobah Allah, ba ga aiki ba, ko kuma wani tafarki, ko kuma wasu mutane, ko kuma ƙungiya. Keɓewar kanka da kuma yin baftisma mafari ne na abokantaka da Allah, da kuma kasancewa amininsa.—Zabura 25:14.

25 Baftisma ba ta ba da tabbacin ceto. Manzo Bulus ya rubuta: “Ku yi aikin cetonku da tsoro da rawan jiki.” (Filibbiyawa 2:12) Baftisma mafari ne kawai. Tambayar ita ce, Ta yaya za ka kasance cikin ƙaunar Allah? Babin mu na gaba zai amsa wannan tambayar.

^ sakin layi na 21 Ana yin baftisma shekara shekara a manyan tarurruka da kuma taron gunduma na Shaidun Jehobah.