Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 03

Za Ka Iya Amincewa da Littafi Mai Tsarki?

Za Ka Iya Amincewa da Littafi Mai Tsarki?

Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da alkawura da shawarwari da yawa. Wataƙila kana so ka san saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki, amma mai yiwuwa kana ɗan jin tsoro. Zai dace ka amince da alkawura da shawarwarin da ke wannan tsohon littafin kuwa? Za ka iya amincewa da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da rayuwa a yanzu da kuma a nan gaba? Mutane da yawa sun amince da hakan. Zai dace kai ma ka bincika da kanka.

1. Abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne?

Abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki “gaskiya” ne. (Mai-Wa’azi 12:10) Labaran da ke ciki game da mutane ne kamar mu kuma abin da ya faɗa game da su gaskiya ne. (Karanta Luka 1:​3, 4; 3:​1, 2.) ’Yan tarihi da masanan neman kayan tarihi cikin ƙasa sun tabbatar da cewa kwanan wata da mutane da wurare da kuma abubuwan da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki sun faru da gaske.

2. Me ya sa muka ce saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba tsohon yayi ba ne?

An faɗi abubuwa da yawa a Littafi Mai Tsarki kafin a san da su. Alal misali, an ambata batutuwan da suka shafi kimiyya. Mutane da yawa ba su gaskata da waɗannan batutuwan ba a lokacin da aka rubuta su. Amma daga baya, ’yan kimiyya sun tabbatar da cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne. Saƙon da ke ciki “tabbatattu ne har abada abadin.”​Zabura 111:8.

3. Me ya sa za mu tabbata da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da nan gaba?

An annabta * abubuwa da yawa a Littafi Mai Tsarki da ba su “faru ba” tukun. (Ishaya 46:10) An annabta abubuwa da dama shekaru da yawa kafin su faru. Kuma an bayyana dalla-dalla abubuwan da suke faruwa a duniya a yau. A wannan darasin, za mu tattauna wasu cikin waɗannan annabce-annabcen. Ganin yadda suke cika yana da ban-sha’awa!

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu ga abin da masana kimiyya suka faɗa da ya jitu da Littafi Mai Tsarki, kuma za ka ga wasu annabce-annabce masu ƙayatarwa.

4. Kimiyya ta jitu da Littafi Mai Tsarki

A zamanin dā, yawancin mutane sun gaskata cewa an ɗora duniya a kan wani abu. Ku kalli BIDIYON nan.

Ka lura da abin da aka faɗa a littafin Ayuba wajen shekaru 3,500 da suka shige. Ku karanta Ayuba 26:​7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa furucin nan an “rataya duniya babu kome a ƙarƙashinta” yake da ban-mamaki?

Rana tana jan ruwa daga manyan tekuna. Sai a yi haɗari kuma a yi ruwan sama. Bayan haka, sai ruwan ya koma teku. Shekaru 200 da suka shige ne aka fahimci yadda ake ruwan sama. Amma ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce shekaru da yawa kafin wannan lokacin. Ku karanta Ayuba 36:27, 28, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne ya fi burge ka game da wannan bayanin?

  • Nassosin da ka karanta sun sa ka ƙara amincewa da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa kuwa?

5. Littafi Mai Tsarki ya annabta abubuwa masu muhimmanci da za su faru

Ku karanta Ishaya 44:27–45:​2, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wane annabci ne aka yi a Littafi Mai Tsarki shekaru 200 kafin a hallaka Babila?

Ku kalli BIDIYON nan.

An rubuta cewa Sairus, sarkin Fasiya da sojojinsa sun ci birnin Babila a wajen shekara 540 kafin haihuwar Yesu. Sun yi wa kogin da ya kewaye birnin wata hanya don ruwan ya ragu. Sai suka shiga birnin ta ƙofar da aka bari a buɗe kuma suka kama birnin ba tare da sun yi yaƙi ba. A yau, bayan fiye da shekaru 2,500, babu wanda ke zama a birnin Babila. Bari mu duba annabcin da aka yi a Littafi Mai Tsarki game da wannan batun.

Ku karanta Ishaya 13:19, 20, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya abin da ya faru da Babila ya cika annabcin nan?

Yadda Babila take yanzu a ƙasar Iraƙi

6. An annabta abubuwa da muke gani a yau a cikin Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya ce muna rayuwa a “kwanakin ƙarshe.” (2 Timoti 3:1) Ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan lokacin.

Ku karanta Matiyu 24:6, 7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Waɗanne abubuwa ne Littafi Mai Tsarki ya ce za su faru a kwanaki na ƙarshe?

Ku karanta 2 Timoti 3:1-5, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waɗanne irin halaye ne Littafi Mai Tsarki ya ce mutane za su nuna a kwanaki na ƙarshe?

  • Wanne cikin halayen nan ne ka lura mutane suna nunawa?

WASU SUN CE: “Abin da ke Littafi Mai Tsarki ba gaskiya ba ne.”

  • Mene ne ya fi tabbatar maka da cewa abin da ke Littafi Mai Tsarki gaskiya ne?

TAƘAITAWA

Tarihi da kimiyya da kuma annabci za su iya sa ka amince da abin da ke Littafi Mai Tsarki.

Bita

  • Shin abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne?

  • A waɗanne hanyoyi ne abin da masana kimiyya suka faɗa ya jitu da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

  • Kana ganin cewa Littafi Mai Tsarki ya faɗi abin da zai faru a nan gaba? Me ya sa ka ce hakan?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga ko abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kimiyya gaskiya ne.

“Kimiyya ta Jitu da Littafi Mai Tsarki Kuwa?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga abubuwan da suka nuna cewa muna “kwanakin ƙarshe.”

“Annabce-annabce Shida da Suke Cika Yanzu” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Mayu, 2011)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda annabcin da Littafi Mai Tsarki ya yi game da mulkin ƙasar Girka ya cika.

Bari Annabcin Littafi Mai Tsarki Su Ƙarfafa Ku (5:22)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda annabcin Littafi Mai Tsarki ya canja ra’ayin wani mutum game da Littafi Mai Tsarki.

“A Dā, Ban Yi Imani da Wanzuwar Allah Ba” (Hasumiyar Tsaro Na 5 2017)

^ sakin layi na 9 Annabci saƙo ne game da abubuwan da za su faru a nan gaba.