Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Ake Nufi da Zuwan Yesu?

Mene ne Ake Nufi da Zuwan Yesu?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 An rubuta annabce-annabce da dama a cikin Nassosi game da lokacin da Yesu zai zo ya hukunta mutane. a Alal misali, Matta 25:31-33 sun ce:

 “Sa’an da Dan mutum [Yesu Kristi] za ya zo cikin darajarsa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’annan za ya zauna bisa kursiyin darajarsa: a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai: shi kuwa za ya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi yakan rarraba tumaki da awaki: kuma za ya sanya tumaki ga hannun damansa, amma awaki ga hagu.”

 Wannan lokacin shari’a zai zama lokacin “kunci mai girma” wanda bai taba faruwa a duniya ba. Za a sha wannan kunci har zuwa yakin Armageddon. (Matta 24:21; Ru’ya ta Yohanna 16:16) Magabtan Kristi, wato wadanda Yesu ya ce da su awaki a kwatancinsa za su “sha hukuncin madawwamiyar halaka.” (2 Tasalonikawa 1:9, Littafi Mai Tsarki; Ru’ya ta Yohanna 19:11, 15) Amma, bayinsa masu aminci da aka ce da su tumaki, za su sami “rai na har abada.”​—Matta 25:46.

Yaushe ne Kristi zai zo?

 Yesu ya ce: “Zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani.” (Matta 24:36, 42; 25:13) Amma ya ba da jerin ‘alamu’ da za su nuna cewa lokacin zuwansa ya kusa.—Matta 24:3, 7-14; Luka 21:10, 11.

Kristi zai zo da jikin ruhu ne ko na zahiri?

 An ta da Yesu daga mutuwa da jikin ruhu, saboda haka zai zo a matsayin ruhu ne, ba a matsayin dan Adam ba. (1 Korintiyawa 15:45; 1 Bitrus 3:18) Wannan dalilin ne ya sa kwana daya kafin mutuwar Yesu, ya gaya wa manzanninsa cewa: “Saura dan lokaci kadan duniya ba za ta kara ganina ba.”—Yohanna 14:19, LMT.

Wasu ra’ayoyi game da zuwan Kristi da ba daidai ba

 Ra’ayi: Yesu zai bayyana a zahiri domin Littafi Mai Tsarki ya ce mutane za su gan shi yana “zuwa kan gajimare.”—Matta 24:30.

 Gaskiyar al’amarin: Sau da yawa idan aka yi magana game da gajimare a cikin Littafi Mai Tsarki, ana nufin abin da ba a gani. (Levitikus 16:2; Littafin Lissafi 11:25; Kubawar Shari’a 33:26) Alal misali, Allah ya gaya wa Musa cewa: “Ina zuwa gare ka cikin bakin hadari,” ko kuma gajimare. (Fitowa 19:9) Musa bai gan Allah ido-da-ido ko kuma a zahiri ba. Hakazalika, idan aka ce Kristi yana “zuwa kan gajimare” ana nufin mutane za su gane cewa ya zo, ko da yake ba za su gan shi ido-da-ido ba.

 Ra’ayi: Furucin nan “kowane ido kuma za ya gan shi” a Ru’ya ta Yohanna 1:7, yana da ma’ana ta zahiri.

 Gaskiyar al’amarin: A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmomin Helenanci da akan yi amfani da su domin “ido” da kuma “gani” suna iya nufin gane wani abu, ba ganin abu a zahiri ba. b (Matta 13:15; Luka 19:42; Romawa 15:21; Afisawa 1:18) Littafi Mai Tsarki ya ce bayan an ta da Yesu daga mutuwa, mazauninsa na “cikin haske wanda ba shi kusantuwa ... ba kuwa mai-ikon ganinsa.” (1 Timotawus 6:16) Saboda haka, furucin nan “kowane ido kuma za ya gan shi,” yana nufin mutane za su gane cewa Yesu ne zai zartar da hukunci a kansu.—Matta 24:30.

a Ko da yake mutane da yawa suna amfani da furucin nan “zuwa na biyu” sa’ad da suke zancen zuwan Kristi, babu wannan furucin a cikin Littafi Mai Tsarki.

b Ka duba The New Thayer’s Greek-English Lexicon of the New Testament (1981), shafuffuka na 451 da 470.