Koma ka ga abin da ke ciki

Maryamu Uwar Allah ce?

Maryamu Uwar Allah ce?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 A’a, Littafi Mai Tsarki bai koyar cewa Maryamu uwar Allah ce ba. Ban da haka, bai ba Kiristoci umurnin su rika bauta da kuma daukaka Maryamu ba. a Ka yi la’akari da wannan:

  •   Maryamu ba ta taba da’awa cewa ita uwar Allah ce ba. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa ta haifi “Dan Allah” ne, ba Allah ba​—Markus 1:1; Luka 1:32.

  •   Yesu kristi bai taba cewa Maryamu uwar Allah ce ba ko kuma a ba ta daraja ta musamman. Ban da haka ma, ya yi wa wata mata gyara saboda ta mai da hankali ga gatan da maryamu ta samu na haifan sa, ya ce: “I, amma albarka tā fi tabbata ga wadanda ke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”​—Luka 11:27, 28.

  •   Lakabin nan “Uwar Allah” da “Theotokos” (Wadda ta haifi Allah) ba sa cikin Littafi Mai Tsarki.

  •   Furucin nan “Sarauniyar Sammai” da aka ambata a Littafi Mai Tsarki ba ya nufin Maryamu, amma allahiyar karya ce da Isra’ilawan da suka yi ridda suke bautawa.(Irmiya 44: 15-​19) Watakila Sarauniyar Sammai” nan Ishtar (Astarte) ce wadda Babiloniyawa ke bautawa.

  •   Kiristoci a karni na farko ba su bauta wa Maryamu ba, balle ma su ba ta wata daraja ta musamman. Wani masani ya ce Kiristoci a karni na farko “ba su amince da bautar gumaka ba kuma watakila sun guji nuna wa Maryamu daraja fiye da kima domin kada mutane su yi zargin su da bauta wa allahiya. ”​—In Quest of the Jewish Mary.

  •   Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana wanzuwa. (Zabura 90:1, 2; Ishaya 40:28) Tun da yake ba shi da mafari, ba zai yiwu a ce yana da uwa ba. Ban da haka ma, Maryamu ba za ta iya daukar Allah a cikinta ba; Littafi Mai Tsarki ya bayana cewa sammai da kanta ta yi masa kadan.​—1 Sarakuna 8:​27.

Maryamu​—Uwar Yesu ba “Uwar Allah ba”

 Maryamu Bayahudiya ce, kuma daga zuriyar Sarki Dauda ta fito. (Luka 3:​23-31) Ta sami tagomashi daga Allah saboda bangaskiya da kauna da take da shi. (Luka 1:​28) Allah ya zabe ta ta haifi Yesu. (Luka 1:​31, 35) Maryamu ta haifa wa mijinta Yusufu wasu ’ya’ya.​—Markus 6:3.

 Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Maryamu ta zama almajirar Yesu, babu wani karin bayani da aka bayar game da ita.—A. M. 1:14.

a Yawancin darikun Kiristoci suna koyar da cewa Maryamu uwar Allah ce. Suna kiran ta da lakabi kamar “sarauniyar sammai” ko kuma Theotokos, wato kalmar Hellenanci da ke nufin “Uwar Allah.”