Koma ka ga abin da ke ciki

Wadanne Dalilai Biyu Ne Suke Sa Allah Ya Ki Jin Wasu Addu’o’i?

Wadanne Dalilai Biyu Ne Suke Sa Allah Ya Ki Jin Wasu Addu’o’i?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Da akwai wasu addu’o’i da Allah ba ya amsawa. Ka bincika dalilai biyu da zai iya sa Allah ya ki amsa addu’ar mutum.

1. Addu’ar da ba ta jitu da nufin Allah ba

 Allah ba ya amsa roko da bai jitu da nufinsa ko kuma ka’idodinsa da suke cikin Littafi Mai Tsarki ba. (1 Yohanna 5:14) Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya bukaci mu guji yin hadama. Caca aikin hadama ne. (1 Korintiyawa 6:​9, 10) Saboda haka, Allah ba zai amsa addu’arka don ka ci wani caca ba. Allah ba wani aljani ba ne da zai bi umarnin da ka ba shi. Hakika, wannan abin godiya ne. Idan ba haka ba, ba za so abin da wasu za su roki Allah ya yi ba.—Yakub 4:3.

2. Idan wanda yake addu’ar yana aikata mugunta

 Allah ba ya sauraron wadanda suka kudurta su yi masa rashin biyayya ta wurin ayyukansu ba. Alal misali, Allah ya gaya wa wadanda suke da’awa cewa suna bauta masa amma suna abubuwan da ba su da kyau cewa: “Sa’anda ku ke yi mani yawan addu’o’i, ba ni ji ba: hannuwanku cike su ke da jini.” (Ishaya 1:15) Amma idan suka juya daga hanyoyinsu kuma suka yi “bincike tare” da Allah, zai saurare su sa’ad da suka yi addu’a gareshi.—Ishaya 1:18.