Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ta Yaya Za Ka Yi Addu’a Kuma Allah Ya Amsa?

Ta Yaya Za Ka Yi Addu’a Kuma Allah Ya Amsa?

Jehobah Allah ne “mai jin addu’o’i.” (Zabura 65:2) Za mu iya yin addu’a a duk inda muke da kuma a kowane lokaci, a cikin zuciyarmu ko mu furta a ji. Jehobah yana so mu kira shi ‘Uba’ kuma ba shakka, ba mu da Uban da ya kai shi. (Matiyu 6:9) Domin Jehobah yana ƙaunar mu, ya koya mana yadda za mu yi addu’a kuma ya saurare mu.

KA YI ADDU’A GA JEHOBAH A CIKIN SUNAN YESU

“Uba zai ba ku duk abin da kuka roƙa a cikin sunana.”​Yohanna 16:23.

Kalaman Yesu sun nuna cewa Jehobah yana so mu yi addu’a ga shi kaɗai ne a cikin sunan Yesu, ba na gumaka ko waliyai ko mala’iku ko kakanninmu da suka mutu ba. Idan muka yi addu’a a cikin sunan Yesu, hakan zai nuna cewa muna daraja abin da Yesu ya yi mana. Shi ya sa Yesu ya ce, “Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.”​—Yohanna 14:6.

KA FAƊI ABIN DA KE ZUCIYARKA

“Ku faɗa masa dukan zuciyarku.”​Zabura 62:8.

Sa’ad da muke addu’a ga Jehobah, mu yi magana kamar yadda za mu yi da mahaifi mai ƙauna. Zai dace mu gaya masa abin da ke zuciyarmu cikin ladabi, maimakon mu karanta addu’ar daga wani littafi ko mu maimaita abin da muka haddace.

KA YI ADDU’AR DA TA JITU DA NUFIN ALLAH

“Idan mun roƙi kome bisa ga nufinsa, zai saurare mu.”​—1 Yohanna 5:14.

A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya gaya mana abin da zai yi mana da abin yake so mu yi masa. Idan muna so Allah ya amsa addu’armu, dole mu yi addu’a “bisa ga nufinsa.” Kafin mu san nufinsa, sai mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki don mu san halinsa. Idan mun yi hakan, Allah zai amsa addu’armu.

A KAN ME DA ME ZA MU IYA YIN ADDU’A?

Ka Roƙi Allah Ya Biya Bukatunka. Za mu iya addu’a Allah ya tanadar mana da abinci da kayan sakawa da kuma wurin kwana. Za mu iya roƙon Allah ya ba mu hikimar yanke shawarwarin da suka dace da kuma ƙarfin jimre matsaloli. Za mu iya roƙon Allah ya sa mu daɗa yin imani da shi, ya gafarta mana kuma ya taimaka mana.​—Luka 11:​3, 4, 13; Yaƙub 1:​5, 17.

Ka Yi Addu’a a Madadin Mutane. Iyayen da ke son yaransu suna farin ciki idan suka ga yaran suna ƙaunar juna. Dukanmu ’ya’yan Allah ne, kuma yana so mu riƙa ƙauna da kula da juna. Saboda haka, ya kamata mu yi addu’a a madadin mijinmu ko matarmu ko yaranmu ko danginmu ko kuma abokanmu. Wani mabiyin Yesu mai suna Yaƙub ya ce, mu riƙa “yi wa juna addu’a.”​—Yaƙub 5:16.

Ka Gode wa Allah. Allah ne Mahaliccinmu kuma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yana yin alherin ba ku ruwan sama da damina mai albarka. Yana ƙosar da ku da abinci a daidai lokaci, yana kuma sa ku yi farin ciki.” (Ayyukan Manzanni 14:17) Idan muka tuna da dukan abubuwan da Allah ya yi mana, hakan zai sa mu gode masa sa’ad da muke yin addu’a. Ƙari ga haka, zai dace mu yi wa Allah biyayya don hakan zai nuna godiyarmu.​—Kolosiyawa 3:15.

KA ZAMA MAI HAƘURI KUMA KA CI GABA DA ADDU’A

A wasu lokuta, idan ba a amsa addu’armu game da wani abu da muke bukata nan da nan ba, hakan zai iya sa mu baƙin ciki. Shin, hakan yana nufin Allah bai damu da mu ba ne? A’a. Ga wasu labaran da suka nuna cewa zai dace mu ci gaba da yin addu’a.

Steve wanda aka ambata a talifi na farko na mujallar nan ya ce, “Addu’a ce ta taimaka mini in sake yin farin ciki a rayuwa.” Me ya sa ya canja ra’ayinsa? Ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya koyi cewa yana bukatar ya riƙa yin addu’a ba fasawa. Steve ya kuma ce, “Ina yin addu’a kuma in gode wa Allah don taimakon da na samu daga wurin abokaina. Yanzu ina farin ciki sosai fiye da dā.”

Jenny kuma fa, wadda ta ji kamar ba ta cancanci Allah ya saurari addu’arta ba? Ta ce, “A lokacin da nake cikin tsananin baƙin ciki, nakan roƙi Allah ya taimaka mini in fahimci dalilin da ya sa nake ji kamar ban cancanta ba.” Ta yaya hakan ya taimaka mata? Ta ce, “Yin addu’a ya taimaka mini in ɗauki kaina yadda Allah yake ɗauka na kuma in ga cewa ko da zuciyata tana gaya min cewa ni mai laifi ce, a wurin Allah ba haka ba ne. Ƙari ga haka, addu’a ta taimaka mini kada in fid da rai.” Mene ne sakamakon nacewa da yin addu’a? Ta ce, “Yin addu’a ya taimaka min in ga cewa Jehobah yana wanzuwa da gaske, shi Allah da Uba da Aboki ne mai ƙauna, wanda zai taimaka min a kowane lokaci muddin ina iya ƙoƙarina in faranta masa rai.”

Isabel ta ce ‘a duk lokacin da na ga ɗana yana farin ciki duk da naƙasarsa, hakan yana tabbatar min cewa Allah ya amsa addu’ata’

Ka yi la’akari da abin da ya faru da Isabel. Da ta samu juna biyu, sai likitocinta suka gaya mata cewa za ta haifi yaronta da naƙasa. Hakan ya sa ta baƙin ciki sosai. Wasu mutane ma sun ce mata ta zubar da cikin. Ta ce, “Saboda tsananin baƙin cikin da nake fama da shi, na ji kamar zan mutu.” Mene ne ta yi? Ta ce, “Na yi ta yin addu’a ga Allah don ya taimaka min.” A kwana a tashi ta haifi ɗanta mai suna Gerard kuma ya fito da naƙasa. Shin, a ganin Isabel Allah ya amsa addu’arta? Ƙwarai kuwa. Ta yaya? Ta ce, “Shekarun ɗana 14 ne yanzu kuma a duk lokacin da na gan shi yana jin daɗin rayuwa duk da naƙasarsa, hakan yana tabbatar min cewa Allah ya amsa addu’ata domin shi kyauta ne mai girma da Allah ya ba ni.”

Irin labaran nan suna tuna mana da abin da wani marubucin Zabura ya ce: “Ya Yahweh, za ka ji kukan marasa ƙarfi. Za ka saurare su, ka ba su ƙarfin zuciya.” (Zabura 10:17) Waɗannan dalilai ne masu kyau da suka nuna cewa ya kamata mu ci gaba da yin addu’a.

Za mu iya ganin addu’o’i da yawa da Yesu ya yi a cikin Littafi Mai Tsarki. Wadda aka fi sani ita ce addu’ar da ya koya wa almajiransa. Me za mu iya koya daga addu’ar?