Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Ma’anar Furucin Nan “Ido a Maimakon Ido”?

Mene ne Ma’anar Furucin Nan “Ido a Maimakon Ido”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Dokar nan “ido a maimakon ido” tana cikin dokokin da Allah ya ba Isra’ilawa ta hannun Musa, kuma Yesu ya yi kaulinsa a hudubarsa a kan dutse. (Matiyu 5:38; Fitowa 21:​24, 25; Maimaitawar Shari’a 19:21) Hakan yana nufin cewa, sa’ad da ake hukunta masu laifi, ya kamata hukuncin ya yi daidai da laifin da mutumin ya yi. a

 Dokar ta shafi hukunci a kan wanda ya ji ma wani rauni da gangan. A dokar da aka ba da ta hannun Musa an ba da umurni game da mutumin da ya ji ma wani rauni da gangan, cewa: “Idan ya karya masa kashi, shi ma za a karya masa kashin. Idan ya cire wa wani ido, shi ma za a cire nasa idon. Idan ya balle wa wani hakori, shi ma za a balle nasa hakorin. Irin raunin da ya yi wa wani, haka za a yi masa.”​—Littafin Firistoci 24:20.

 Mene ne manufar dokar “ido a maimakon ido”?

 Dokar “ido a maimakon ido” ba ta ba mutane ’yancin daukan fansa da kansu ba. A maimakon haka, ya taimaka wa alkalai su rika yanke hukuncin da ya dace, ba tare da wuce gona da iri ko kuma saukaka hukuncin da ya kamata su yanke ba.

 Kari ga haka, dokar za ta hana mutum yi wa wani lahani da gangan ko yin makarkashiya ko kuma kulle-kulle. “Sauran mutanen [wadanda suke bin dokokin Allah] za su ji, su ji tsoro, kuma nan gaba ba za su kara aikata irin wannan laifi a cikinku ba.”​—Maimaitawar Shari’a 19:20.

 Dokar “ido a maimakon ido” ta shafi Kiristoci ne?

 A’a, wannan dokar ba ta shafi Kiristoci ba. Tana cikin dokokin da Allah ya ba Isra’ilawa ta hannun Musa, kuma mutuwar Yesu ta kawar da wannan dokar.​—Romawa 10:4.

 Duk da haka, dokar ta sa mu san ra’ayin Allah. Alal misali, Allah yana son adalci da shari’ar gaskiya. (Zabura 89:14) Dokar ta kuma nuna ka’idar Jehobah cewa ya kamata a hukunta masu laifi yadda ya dace.​—Irmiya 30:11.

 Ra’ayin karya game da dokar “ido a maimakon ido”

 Ra’ayin karya: Dokar “ido a maimakon ido” yana da tsanani ainun.

 Gaskiyar: Wannan dokar ba ta goyi bayan yin amfani da doka don cin zarafin mutum ba. A maimakon haka, idan aka yi amfani da wannan dokar yadda ya dace, alkalai za su yanke hukunci yadda ya dace bayan sun yi la’akari da dalilan da suka sa aka aikata laifin kuma suka bincika ko da gangan ne ko kuma a’a. (Fitowa 21:​28-30; Littafin Ƙidaya 35:​22-25) Dokar “ido a maimakon ido” tana sa a guji yanke hukuncin da ta wuce gona da iri.

 Ra’yin karya: Dokar “ido a maimakon ido” ta ba mutane zarafi su yi ta rama laifin da aka yi musu.

 Gaskiyar: Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa ta ce: “Ba za ka nemi hanyar ramuwa ko ka rike wani a zuciya ba.” (Littafin Firistoci 19:18) Maimakon karfafa mutane su rika rama abin da aka yi musu, dokar ta karfafa mutane su dogara ga Allah da kuma tsarin shari’a da ya kafa don magance matsaloli.​—Maimaitawar Shari’a 32:35.

a Wasu yankuna a zamanin dā sun bi wannan dokar da a wasu lokuta ake kira lex talionis a yaren Latin.