Koma ka ga abin da ke ciki

Za A Hallaka Duniyar Nan Ne?

Za A Hallaka Duniyar Nan Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 A’a. Ba za a taba hallaka Duniyar nan ko a kone ta ba. Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa Allah ya halicci duniya ne don a yi rayuwa a cikinta har abada.

  •   “Masu adalci za su gāji kasar, su zauna a ciki har abada.”​—Zabura 37:29.

  •   “Ka kafa duniya a kan tushenta daram har abada abadin.”​—Zabura 104:5.

  •   “Duniya tana nan daram har abada.”​—Mai-Wa’azi 1:4.

  •   “Mai siffata duniya, Mai Yinta, Mai Kafa ta! Bai halicci duniya ta zama wofi ba, ya yi ta domin a zauna a cikinta.”​—Ishaya 45:18.

Zai yiwu ’yan Adam su hallaka duniyar nan?

 Allah ba zai bar ’yan Adam su hallaka duniyar nan ba, ko ta yaki ko ta wajen gurbata mahalli da dai sauransu. Maimakon haka, Allah zai “halaka masu halaka duniya.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 11:18) Ta yaya Allah zai yi hakan?

 Allah zai hallaka gwamnatocin ’yan Adam wadanda suka kāsa kula da duniyar nan. Sai ya kafa nasa Mulkin a sama. (Daniyel 2:44; Matiyu 6:​9, 10) Yesu Kristi ne zai zama sarkin wannan Mulkin. (Ishaya 9:​6, 7) Sa’ad da yake duniya, Yesu ya nuna cewa yana da iko a kan abubuwan da Allah ya halitta. (Markus 4:​35-41) Idan Yesu ya soma sarauta a bisa duniya, zai nuna ikonsa a kan abubuwan da Allah ya halitta. Zai sabonta yanayin duniya, ya mai da shi yadda yake a lokacin da Allah ya halicci gonar Adnin.​—Matiyu 19:28; Luka 23:43.

Ba Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa za a kone duniya da wuta ba?

 A’a, bai koyar da hakan ba. Mutane da yawa sun yi wa 2 Bitrus 3:7 bahaguwar fahimta shi ya sa suke wannan tunanin. Ayar ta ce: “Sama da kasa wadanda suke a nan yanzu, suna jira a halaka su da wuta.” Ga abubuwa biyu da za su taimaka mana mu fahimci ma’anar wannan ayar:

  1.   Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmomin nan “sama,” da “kasa,” wato duniya, da kuma “wuta,” don ya yi nuni ga abubuwa dabam-dabam. Alal misali, Zabura 33:8 ta ce: “Bari dukan duniya su ji tsoron Yahweh.” A wannan ayar, “duniya” tana nufin dukan ’yan Adam.

  2.   Abin da aka ambata kafin 2 Bitrus 3:7 ya nuna abin da sama da kasa da wuta suke nufi. Ayoyi 5 da 6 sun nuna cewa irin abin da ya faru a lokacin Ambaliyar zamanin Nuhu ne zai faru a nan gaba. An hallaka duniya a lokacin, amma ba duniyar da muke zama a ciki aka hallaka ba. A maimakon haka, “duniyar” da ambaliyar ta hallaka, mugayen mutane ne. (Farawa 6:11) Kari ga haka, ta kuma hallaka “sama,” wato mutane da suke sarauta a duniya a lokacin. Mugayen mutane ne aka hallaka, ba doron kasa ba. Nuhu da iyalinsa sun tsira kuma sun ci gaba da rayuwa a duniya bayan Ambaliyar.​—Farawa 8:​15-18.

 Kamar yadda ambaliyar zamanin Nuhu ta hallaka mugaye, haka ma hallaka ko “wuta” da 2 Bitrus 3:7 ta ambata za ta kawo karshen mugayen mutane ne, ba doron kasarmu ba. Allah ya ce zai kawo “sabon sammai da sabuwar kasa, inda adalci zai kasance kullum.” (2 Bitrus 3:13) “Sabuwar kasa,” tana nufin mutanen kirki wadanda “sabon sammai” ko kuma sabon gwamnati, wato Mulkin Allah, zai yi sarauta a bisansu. Mulkin Allah zai sa duniya ta zama aljanna.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​1-4.