Koma ka ga abin da ke ciki

Abin da Littafi Mai Tsarki ya Ce Game da Daniyel?

Abin da Littafi Mai Tsarki ya Ce Game da Daniyel?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Daniyel Bayahude, annabi ne da ya kware sosai, kuma ya yi rayuwa wajen shekaru 600 kafin haihuwar Yesu. Allah ya sa Daniyel ya iya bayyana mafarkai da nuna masa wahayi game da abubuwan da za su faru a nan gaba, kuma ya sa ya rubuta littafin da ke dauke da sunansa a cikin Littafi Mai Tsarki.​—Daniyel 1:17; 2:19.

Wane ne Daniyel

 Daniyel ya yi girma a Yahuda, wurin da birnin Urushalima da haikalin Yahudawa yake. A shekara ta 617 kafin haihuwar Yesu, Nebukadnezzar sarki Babila ya ci Urushalima kuma ya kwashi “manyan mutanen kasar” zuwa bauta a Babila. (2 Sarakuna 24:15; Daniyel 1:1) An tafi da Daniyel ma, wanda watakila shi matashi ne a lokacin.

 An kai Daniyel da wasu matasa (har da Shadrak da Meshak da kuma Abednego) zuwa fadar sarki a Babila don a yi musu koyarwa ta musamman da zai taimaka musu su rika yi wa gwamnatin Babila aiki. Ko da yake an matsa musu su yi abubuwan da ba su dace ba, Daniyel da abokansa uku sun rike aminci ga Allahnsu, Jehobah. (Daniyel 1:​3-8) Bayan an koyar da su shekara uku, Sarki Nebukadnezzar ya yaba musu don hikimarsu da iyawarsu, ku ya ce “sun fi dukan masu dabo da masu sihiri wadanda suke cikin mulkinsa har sau goma.” Sai ya nada Daniyel da abokansa su rika hidima a fadar sarki.​—Daniyel 1:​18-20.

 Bayan shekaru da yawa, watakila saꞌad da Daniyel yake shekara 90, an ce ya zo fadar sarki. Sarki Belshazzar da ke sarautar Babila a lokacin ya gaya wa Daniyel ya bayyana maꞌanar rubutun da wani yatsun hannu ya yi a bango. Da taimakon Jehobah, Daniyel ya bayyana cewa Mediya da Fashiya za su ci Babila a yaki. A daren nan, an ci Babila a yaki.​—Daniyel 5:​1, 13-31.

 Saꞌad da Mediya da Fashiya suke sarauta, an nada Daniyel hakimi kuma Sarki Dariyus ya so ya kara masa matsayi. (Daniyel 6:​1-3) Sauran maꞌaikata masu kishin Daniyel sun kulla su kashe shi ta wurin jefa shi cikin ramin zakuna, amma Jehobah ya cece shi. (Daniyel 6:​4-23) A lokacin da Daniyel ya tsufa sosai, wani malaꞌika ya zo ya karfafa shi sau biyu cewa shi “mai daraja ne sosai.”​—Daniyel 10:​11, 19.

 Ka kalli yadda wadannan abubuwa suka faru a wasan kwaikwayo mai sashe biyu mai jigo Daniyel: Mutum Mai Bangaskiya.