Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Ma’anar Kalmar Nan Annabci?

Mene ne Ma’anar Kalmar Nan Annabci?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Annabci yana nufin sako daga wurin Allah ko kuma wahayi. Littafi Mai Tsarki ya ce abin da annabawa suka fada ya fito “daga wurin Allah” ne domin ‘ruhu mai tsarki ne ya motsa su.’ (2 Bitrus 1:20, 21). Saboda haka, ana kiran duk wanda Allah yake amfani da shi wajen aika sakonsa annabi.—Ayyukan Manzanni 3:18.

Ta yaya annabawa suke samun sako daga Allah?

 Ga wasu hanyoyin da Allah yake amfani da su wajen ba wa annabawansa sako:

  •   Rubutu. Allah ne ya rubuta Dokoki Goma da ya ba wa Musa.—Fitowa 31:18.

  •   agana ta bakin mala’iku. Alal misali, Allah ya yi amfani da mala’ika ya gaya wa Musa abin da zai gaya wa Fir’auna. (Fitowa 3:2-4, 10) Idan Allah yana so a yi amfani da wasu kalmomi na musamman, yana sa mala’ikunsa su furta wadannan kalmomin domin annabin ya rubuta furucin daidai yadda mala’ikan ya gaya masa, alal misalai a lokacin da ya gaya wa Musa cewa: “Ka rubuta dukan wadannan kalmomi, [domin] bisa ga wadannan kalmomi ne na daura yarjejeniya da kai da kuma jama’ar Isra’ila.”—Fitowa 34:27, a Littafi Mai Tsarki, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.

  •   Wahayi. A wasu lokuta akan saukar wa annabi da wahayi sa’ad da yake cikin hankalinsa. (Ishaya 1:1; Habakkuk 1:1) Wani lokaci ma sai wanda ake saukar wa wahayin ya ga kamar abin yana faruwa ne a zahiri. (Luka 9:28-36; Ru’ya ta Yohanna 1:10-17) Kari ga haka, Allah yakan saukar wa mutum da wahayi a lokacin da mutumin ya fita daga cikin hayyacinsa. (Ayyukan Manzanni 10:10, 11; 22:17-21) Allah yana kuma iya saukar da wahayi ta mafarki.—Daniyel 7:1; Ayyukan Manzanni 16:9, 10.

  •   Allah yana sa su yi tunanin abin da yake so su rubuta. Allah yana ba annabawansa sako kuma ya sa su yi tunanin yadda za su idar da sakon. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah” ne. (2 Timotawus 3:16) Ruhu mai tsarki ne yake motsa bayin Allah su rubuta abin da ke Littafi Mai Tsarki, kuma ko da yake annabin ne ya zabi kalmomin da ya yi amfani da su, sakon ya fito daga wurin Allah ne.—2 Sama’ila 23:1, 2.

Shin annabci ya kunshi fadin abin da zai faru nan gaba ne kawai?

 A’a, ba fadan abin da zai faru nan gaba ne kawai annabcin Littafi Mai Tsarki ya kunsa ba. Amma yawancin sakonnin da Allah yake bayarwa sun shafi abin da zai faru nan gaba ne. Alal misali, annabawa suna yawan yi wa al’ummar Isra’ila kashedi game da sakamakon rashin biyayyar da suke yi. Akan gaya musu albarkar da za su samu idan suka yi biyayya da kuma bala’in da zai same su idan suka yi rashin biyayya. (Irmiya 25:4-6) A karshe dai, abin da Isra’ilawan suka zaba shi ne yake faruwa da su.—Kubawar Shari’a 30:19, 20.

Misalan wasu annabci da ba su kunshi fadin abin da zai faru nan gaba ba

  •   Isra’ilawa sun taba rokan Allah ya taimaka musu, amma ya ce wa annabinsa ya je ya gaya musu cewa, ba zai taimaka musu ba da yake ba sa bin dokokinsa.—Alkalawa 6:6-10.

  •   Sa’ad da Yesu yake yi wa wata mata Ba-samariya magana, ya gaya mata abubuwan da ta yi a dā, kuma babu shakka, Allah ne ya nuna masa hakan ta wahayi. Nan take sai ta fahimci cewa shi annabi ne, ko da yake bai gaya mata wani abin da zai faru a nan gaba ba.—Yohanna 4:17-19.

  •   Sa’ad da makiyan Yesu suke gana masa azaba, wasu a cikinsu suka rufe masa ido kuma wani ya buge shi sai suka ce: “Yi mana annabci, wane ne ya buge ka?” Sun yi hakan ne ba don ya gaya musu abin da zai faru a nan gaba ba, amma suna so ne ya yi amfani da ikon Allah ya gaya musu wanda ya buge shi.—Luka 22:63, 64.

a Ko da yake mutum zai ji kamar Allah ne da kansa yake wa Musa magana, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mala’ika ne Allah ya turo don ya gaya wa Musa abin da zai rubuta.—Ayyukan Manzanni 7:53; Galatiyawa 3:19.