Koma ka ga abin da ke ciki

“Na Yi Ta Jira Shaidun Jehobah Su Kira Ni”

“Na Yi Ta Jira Shaidun Jehobah Su Kira Ni”

 Ed da matarsa Jennie sun gwada yin waꞌazi ta waya a shekara ta 2010. a Jennie ta ce: “Ba na son yin hakan sam, na gaya wa maigidana cewa ‘ba zan sake yin hakan kuma ba!’ ” Hakan ma maigidan yake ji. Ya ce: “Ba na so a rika min tala ta waya, don haka, ba na so mutane su ga kamar tala muke yi ta waya idan mu kira mu yi waꞌazi.”

 Sai aka soma annobar korona, kuma Shaidun Jehobah suka daina waꞌazi gida-gida. Amma sun ci gaba da yin waꞌazi ta wajen rubuta wa mutane wasika da kiran su ta waya. Sun yi hakan don suna bin umurnin Yesu cewa a yi waꞌazi. (Matiyu 24:14; 28:​19, 20) A lokacin, ana taron ikilisiya da taron fita waꞌazi ta hanyar bidiyo. A irin wannan taron ne Ed ya yi kokari ya yi sake waꞌazi ta waya. Yaya ya ji saꞌad da yake so ya yi waꞌazinsa na farko ta waya? Ya ce: “Na yi adduꞌa Jehobah ya taimaka mini don na ji tsoro sosai! Bayan hakan, na yi kiran sai na hadu da wani mai suna Tyrone.” b

 Tyrone da matarsa Edith suna zama a wani kauye a jihar Kentucky da ke Amirka. Tyrone yana da shekara 83 kuma ba ya gani sosai. Duk da haka, ya yarda Ed ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Yakan karanta littafin da yake nazarinsa da gilashi da ke sa rubutun girma kuma Ed ya soma nazari da shi a kai a kai ta waya.

 Bayan wata guda, sai Tyrone da Edith suka soma halartan taron ikilisiya. Amma domin ba su da intane, sukan halarci taron ta waya. Mene ya sa Edith ta so ta yi nazari?

 Saꞌad da ake nazari da Tyrone, Ed da Jennie sukan ji Edith tana gaya wa mijinta amsoshin da kuma bude nasossi a Littafi Mai Tsarki. Amma ita da kanta ba ta so a yi nazari da ita. Jennie ya ce, “Ta muryata mun lura cewa, akwai abin da ke daminta, amma ni da mijina ba mu san abin da ke daminta ba.”

Ed da Jennie suna waꞌazi ta waya

 Wata rana, Jennie ta ce bari ta tambaye Edith abin da ke daminta. Saboda haka, a lokacin da ya dace Jennie ta ce mijinta ya ba ta waya ta yi magana da Edith. Jennie ta ce, “Tyrone, na ji muryar matarka a wurin kumaina so ta karanta wani nassi ko kuma ta yi kalami.”

 Bayan da Edith ta dan dakata, sai ta yi magana ta waya. Saꞌan nan ta soma magana a hankali yadda take yi, ta ce, “Dama ina so in yi magana da ke, ni Mashaidiya ce. Na yi shekara 40 ba na zuwa waꞌazi da taro.”

 Jennie ta yi mamaki. Sai ta ce, “Ke ꞌyarꞌuwata ce” kuma su biyun suka fashe da kuka.

 Ba da dadewa ba, Ed ta ba Edith kasidar nan Ka Komo ga Jehobah. Bayan wasu makonni, Ed da Jennie sun lura cewa Edith ta canja. Ed ya ce, “Da farko, mun lura cewa tana bakin ciki sosai. Amma yanzu daga muryarta za ka ga cewa tana farin ciki.” Edith ta soma samun ci gaba a bautarta ga Jehobah, kuma yanzu tana jin dadin yin ayyukan ibada. Mijinta ya yi baftisma a watan Yuli 2022.

 Saꞌad da Ed ya tuna yadda yake ji a dā game da yin waꞌazi ta waya, sai ya tuna da tattaunawa da ya yi da Tyrone. Bayan da Ed ya karanta wa Tyrone Yohanna 6:44 kuma ya bayyana masa cewa Jehobah ne yake sa mutane su koyi gaskiya, sai Tyrone ya yarda kuma ya dada cewa: “Na yi ta jira Shaidun Jehobah su kira ni.” Jennie tana farin ciki cewa ita da mijinta sun kasance da karfin zuciya su yi waꞌazi ta waya. Ta ce, “Jehobah yana yi mana albarka saꞌad da muka yi kokari mu yi wani abu mai wuya a hidimarmu.”

a Shaidun Jehobah suna yin hidimarsu bisa ga dokar kāre bayanan mutum.

b An canja sunayen.