Koma ka ga abin da ke ciki

Sun Tsaya Don Su Taimaka

Sun Tsaya Don Su Taimaka

 Bob yana tukin misalin kilomita dari a awa guda a cikin sanyi a yankin Alberta da ke Kanada, sai tayar baya na motarsa ta fashe. Da farko Bob bai san abin da ya faru ba kuma ya ci gaba da yin tukinsa domin kilomita biyar ne ya rage ya isa gidansa.

 A wasikar da Bob ya tura ga Majami’ar Mulkin na Shaidun Jehobah da ke wurin, ya bayyana abin da ya faru. Ya ce: “Wasu matasa guda biyar a cikin motarsu sun tsaya kusa da motata kuma suka gaya mini cewa tayar motata ta fashe. Dukanmu muka faka motocinmu kuma matasan suka ce za su taimaka mini su canja tayar. Ban san ko ina da jak da kuma wata taya mai kyau a cikin motata ba. Sa’ad da nake zaune a gefen hanya a kan kujerata ta guragu, matasan sun shiga karkashin motata suka fito da dayan tayar da jak kuma suka canja mini tayar. Sun yi hakan duk da cewa ana sanyi kuma dusar kankara tana zubowa. Matasan sun saka tufafi masu kyau amma sun taimaka mini da canja tayar motata kuma hakan ya sa na iya tuka motar. Ni kadai ba zan iya yin wannan aikin ba.

 “Ina godiya sosai ga wadannan matasa biyar don yadda suka taimaka mini. Suna kan hanyar ne domin suna zuwa gidajen mutane su yi wa’azi. Hakika, wadannan matasan suna yin abin da suke wa’azi a kai. Da a ce ba su taimaka mini ba, da na bata lokaci kuma na sha wuya sosai, ina yi musu mutukar godiya. Ban san cewa za a iya samun matasa masu halin kirki kamar haka a hanya ba, kamar dai Allah ne ya turo su!”