Koma ka ga abin da ke ciki

An Dauka Cewa Ni Ne Faston

An Dauka Cewa Ni Ne Faston

 Osman da matarsa da kuma diyarsa na wa’azi da amalanke a wajen wani makabarta a kasar Chile. Ba zato, sai ga jama’a da yawa masu raka gawa sun iso suna kadai-kadai. Sai wasu a cikinsu suka dauka Osman wani Fastonsu ne, sai suka yi kusa da shi suka rungume shi suka ce, “Mun gode da ka iso nan da wuri, Fasto, da ma kai muke jira!”

 Ko da yake Osman ya yi kokari ya yi masu bayani, amma jama’a na surutu kuma hakan ya sa ba su fahimce shi ba. Bayan yan mintoci da jama’a suka shiga cikin makabarta, sai wasu su suka dawo wurin shi suka ce masa, “Fasto, muna jiranka a cikin makabartar.”

 Da mutanen suka rage surutun, sai Osman ya sami damar gaya musu ko wane ne shi da kuma dalilin da yasa yake wurin. Bayan mutanen sun nuna fushinsu domin fastonsu bai zo ba, sai suka roke Osman suka ce: “Za ka iya shigowa ka yi wata karamin jawabi daga Littafi Mai Tsarki don mutanen da suka taru a makabartar?” Sai Osman ya amince ya yi hakan.

 Sa’ad da suke hanyar zuwa wurin da aka haka kabarin, sai Osman ya yi masu tambayoyi game da mamacin, kuma ya yi tunanin nassosin da za su amfane mutanen. Da ya isa bakin kabari, sai ya gabatar da kansa wa jama’a kuma ya yi masu bayani cewa a matsayinsa na Mashaidin Jehobah, yana shelar bishara ga mutane.

 Sai ya yi amfani Ru’ya ta Yohanna 21:​3, 4 da Yohanna 5:​28, 29 kuma ya yi bayyana cewa Allah bai halicci mutane don su rika mutuwa ba. Ya ce nan ba da dadewa ba Allah zai ta da matattu kuma za su samu damar yin rayuwa a duniya har abada. Da Osman ya kammala jawabin, sai mutane da yawa suka rungume shi suna murna kuma suka yi masa godiya domin wa’azin “sakon Jehobah” da ya yi musu. Sai ya koma wurin Amalanken wa’azin.

 Da aka gama jana’izar, wasu a cikin masu makoki suka zo wurin amalanken wa’azi, suka tambaye Osman da iyalinsa tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki. Bayan sun dau lokaci suna tattaunawa, sai suka karbi kusan duka mujallu da ke amalanken wa’azin.