Koma ka ga abin da ke ciki

Ambaliya ta sa Mutane Su Ji Waꞌazi

Ambaliya ta sa Mutane Su Ji Waꞌazi

 A shekara ta 2017, Shaidu 12 sun tashi da jirgin ruwa daga yankin Mosquito (Miskito) da ke gabar tekun Nicaragua. Sunan jirginsu shi ne Sturi Yamni. Daya daga cikin masu tukin mai suna Stephen ya ce, “Muna so mu karfafa karamin rukunin Shaidu da ke zama a wani kauye kuma mu taimaka musu yin waꞌazi a yankinsu mai girma sosai.”

 Shaidu 12 ne suka tashi daga yankin Pearl Lagoon suka yi tafiya na kilomita 200 zuwa Río Grande de Matagalpa. Ba su sani ba cewa sunan jirginsu, wanda yake nufin “bishara” a yaren Miskito zai kasance da maꞌana ta musamman ga mutane da suke zama a gabar kogin. Bayan sun yi tafiya na awa 12 ban da wuraren da suka tsaya da dare, Shaidun sun isa yankin La Cruz de Río Grande. Shaidu 6 da ke yankin sun marabci ꞌyanꞌuwan sosai.

 Amma wani balaꞌi ya faru da dare nan. An yi ruwan sama mai karfi sosai da ta sa aka yi ambaliya a Río Grande de Matagalpa. Cikin saꞌoi kadan kogin ya cika makil kuma ya ci gaba da karuwa har kwanaki biyu. Ruwan ya shiga Majamiꞌar Mulki da gidaje da yawa da ke La Cruz. ꞌYanꞌuwa da suka zo waꞌazi sun taimaka wa mutane da ke yankin su kaura daga gidajensu. Yawancinsu sun yi kwana biyu a gidan bene mai hawa biyu na wata Mashaidiya.

Majamiꞌar Mulkin da ke La Cruz da ruwa ya shiga

 A rana ta uku, magajin garin La Cruz ya je ya nemi taimakon Shaidu da suka zo waꞌazi. Tun da yake jirgi Sturi Yamni ne kadai yake da karfin shiga kogin da ya cika makil, magajin yana so matukan jirgin su kai mutane masu aikin agaji don su taimaka wa mutane da ambaliyar ta shafa. Shaidun sun yi farin cikin taimakawa.

 Washegari da safe, Shaidu uku suka kama hanya da masu aikin ba da agaji. Stephen ya ce, “A lokacin ruwan kogin yana ta karuwa. Itatuwan da ambaliyar ta tumbuke sun cika koꞌina a kogin kuma ruwan tana gudu sosai (wato kilomita 18 cikin awa guda). Duk da wannan yanayin, mun je kauyuka uku.

 Shaidu ukun nan sun yi amfani da wannan damar don su karfafa mutanen kauyukan. Sun kuma rarraba Awake na 2017 mai jigo “When Disaster Strikes​—Steps That Can Save Lives.”

 Mutanen kauyen da suke wajen kogin sun ji dadi don yadda Shaidun suka taimaka musu da kuma yadda suka karfafa su da Littafi Mai Tsarki. Wasu a kauyen sun ce: “Shaidun suna da niyyar su taimaka saꞌad da muke fama da balaꞌi.” Wasu kuma sun ce: “Suna kaunar makwabtansu da gaske.” Bayan sun ga yadda Shaidun suka yi kokarin taimaka wa ꞌyanꞌuwansu har ma da wasu mutane, mutane da yawa a kauyen sun soma saurarar waꞌazi.

Daya daga cikin matukan jirgin ruwan mai suna Marco, yana fita daga cikin Sturi Yamni don ya yi wa mutanen kauyen waꞌazi

An faka jirgin ruwa Sturi Yamni a wani kauye cike da ambaliya