Koma ka ga abin da ke ciki

Abin da Zai Taimaka wa Ma’aikatan Asibiti da Aiki Ya Yi Musu Yawa

Abin da Zai Taimaka wa Ma’aikatan Asibiti da Aiki Ya Yi Musu Yawa

 Wani mai suna Bryn, wanda yake zama a jihar North Carolina, a Amirka, yana yin hidima da Kwamitin Hulda da Asibitoci. Kwamitin yana hada kai da asibitoci wajen kula da Shaidun Jehobah da suke jinya.

 A lokacin annobar korona, asibitoci da yawa sun ki barin masu ziyara su shiga saboda annobar. Bryn ya kira darektan da ke shirya yadda malaman addinai za su ba da karfafa ga masu jinya, don a bar shi ya karfafa Shaidun Jehobah da ke rashin lafiya.

 Amma mataimakin darektan ne Bryn ya sami damar yin magana da shi. Da yake ya san cewa ba za a yarda ya shiga asibitin ba, sai ya tambaya ko za a iya ba da lambar wayarsa ga Shaidun Jehobah da ke jinya don su kira shi ya kuma karfafa su. Sai aka yarda masa.

 Bayan hakan, Bryn ya soma tunanin yadda zai taimaka wa ma’aikatan asibitin. Ya gaya wa mataimakin darektan cewa yana son aikin da ma’aikatan suke yi a asibitin kuma yana fatan suna cikin koshin lafiya. Ya dada da cewa ya karanta yadda mutane a ko’ina, musamman ma’aikatan asibitoci, suke cikin damuwa kuma suna fama da yawan aiki saboda annobar.

 Mataimakin darektan ya yarda cewa annobar korona ta sa ma’aikatan asibitin a cikin yanayi mai wuya.

 Sai Bryn ya ce masa: “Dandalinmu yana dauke da bayanai da za su iya taimaka wa mutane da ke cikin damuwa saboda fama da yawan aiki. Idan ka shiga dandalin jw.org a Turanci kuma ka rubuta ‘stress’ a inda aka rubuta ‘Search’, za ka sami talifofin da za su taimaka wa ma’aikatanka.”

 Yayin da suke magana, sai mataimakin darektan ya shiga dandalin jw.org kuma ya rubuta “stress” a inda aka rubuta “Search.” Da ya ga talifofin da aka rubuta a kan batun sai ya ce, “Madalla! Zan nuna wa darekta. Wadannan talifofin za su amfani ma’aikatanmu da ma wasu. Zan buga talifofin a kan falle kuma in rarraba musu.”

 Bayan ’yan makonni, Bryn ya yi magana da darektan kuma darektan ya ce sun riga sun shiga dandalin, har sun buga talifofi a kan batun da ma wasu batutuwa makamancinsa. Sun rarraba talifofin ga nas-nas da kuma wasu ma’aikatan asibitin.

 Bryn ya ce: “Darektan ya yi min godiya don aikin da muke yi da kuma don talifofin, kuma ya ce an rubuta talifofin da kyau sosai. Ya kara da cewa talifofin sun taimaka musu sosai.”