Koma ka ga abin da ke ciki

Anya Shaidun Jehobah Sun Yarda da Tsohon Alkawari Kuwa?

Anya Shaidun Jehobah Sun Yarda da Tsohon Alkawari Kuwa?

 Hakika. Shaidun Jehobah sun yarda da Littafi Mai Tsarki gabaki dayansa cewa “hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne.” (2 Timotawus 3:​16) Wannan shine ake kira Tsohon Alkawari da kuma Sabon Alkawari. Galibi dai, Shaidun Jehobah suna kirar wadannan Nassosin Ibrananci da kuma Nassosin Helenanci. Saboda haka, ba zai zama cewa wani sashen Littafi Mai Tsarki tsoho ne ko sabo ba.

Me ya sa ya kamata Kiristoci su yi amfani da Tsohon Alkawari duk da Sabon Alkawari?

 Kirista manzo Bulus ta wurin ikon ruhu mai tsarki ya rubuta cewa: “Iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu.” (Romawa 15:4) Saboda haka, akwai koyarwa na musamman dominmu cikin Nassosin Ibrananci. Suna gaya mana game da tarihi da shawarwari masu kyau.

  •   Muhimman Tarihi. Nassosin Ibrananci suna dauke da tarihin halitta zuwa faduwar mutum cikin zunubi. Da babu wannan, ba za mu sami amsoshi masu gamsarwa ga irin tambayoyin nan: Daga ina muka fito? Me ya sa mutane ke mutuwa? (Farawa 2:7, 17) Ban da haka, Nassosin Ibrananci na dauke da yadda Jehobah Allah ya bi da mutane da suke farin ciki da kuma wahala irin ta mu.​—Yakub 5:​17.

  •   Shawara mai kyau. Littafin Misalai da na Mai-Wa’azi da suke cikin Nassosin Ibrananci suna dauke da hikima don yin rayuwar kirki. Suna ba da shawara game da rayuwar iyali mai farin ciki (Misalai 15:17), yadda za a daidaita a batun aiki (Misalai 10:4; Mai-Wa’azi 4:6), da kuma yadda matasa za su more kuruciyarsu (Mai-Wa’azi 11:9–​12:1).

 Za mu kuma sami amfani daga yin nazarin Dokar Musa yadda aka rubuta su cikin Torah (Littattafan Littafi Mai Tsarki biyar na farko). Ko da yake Dokar ba tilas ba ne kan Kiristoci a yau, amma tana dauke da muhimman ka’idodi da za su taimaka mana mu yi farin ciki.​—Levitikus 19:18; Kubawar Shari’a 6:​5-7.