Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah Suna da Nasu Littafi Mai Tsarki Dabam?

Shaidun Jehobah Suna da Nasu Littafi Mai Tsarki Dabam?

 Shaidun Jehobah sun yi amfani da juyin Littafi Mai Tsarki da yawa don yin nazari. Amma, mun fi so mu yi amfani da New World Translation of the Holy Scriptures idan akwai shi a yaren da muke yi. Dalilin shi ne, yana da saukin fahimta, yana dauke da sunan Allah kuma babu kuskure.

  •   Sunan Allah. Wasu mafassaran Littafi Mai Tsarki ba sa daukaka Mawallafinsa. Alal misali, wani juyin Littafi Mai Tsarki ya jera sunayen mutane sama da 70 da suka taimaka da fassarar. Amma, wannan juyin bai ambaci sunan Mawallafin Littafi Mai Tsarki ba, wato, Jehobah Allah, ko sau daya!

     Akasin haka, juyin New World Translation yana dauke da sunan Allah a duk wuraren da aka rubuta shi a cikin asalin Littafi Mai Tsarki, kuma ba a ambata sunayen wadanda suka yi fassarar ba.

  •   Babu kuskure. Ba duka juyin Littafi Mai Tsarki ne ke dauke da ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya fada ba. Wani juyin Littafi Mai Tsarki ya fassara Matta 16:24 haka: “Idan kowane mutum yana da nufi shi bi bayana, sai shi yi musun kansa, shi dauki gicciyensa, shi biyo ni.” Masu bautar gumaka sun yi shekaru da yawa suna amfani da gicciye a sujjada kafin Kristi ya zo duniya. A tsakiyar karni na 3 bayan haihuwar Yesu, ’yan coci sun soma yin amfani da gicciye a matsayin gicciyen Kristi. Watakila mafassaran sun yi amfani da ‘gicciye’ a cikin Kalmar Allah don suna ji kamar Yesu ya mutu a kan gicciye. Amma a cikin rubutun asali na Littafi Mai Tsarki an yi amfani da kalmar da idan aka fassara yana nufin “gungumi” maimakon “gicciye.” Shi ya sa New World Translation ya ce: “Sai Yesu ya ce wa almajiransa, ‘Duk mai so ya bi ni, sai ya ki kansa, ya dauki gungumen azabarsa ya bi ni.’”

  •   Saukin fahimta. Fassara mai kyau ita ce wadda ba ta da kuskure kuma tana da saukin fahimta. Ka yi la’akari da wannan misali. A Romawa 12:11, manzo Bulus ya yi amfani da wani furucin da a zahiri yana nufin “zuwa ga ruhun da ke tafasa.” Tun da yake wannan furucin bai da wata ma’ana a Turancin zamani, an fassara ayar a New World Translation yadda za ta zama da saukin ganewa. A wurin an ce Kiristoci su ‘dauki niyya sosai a zukatansu.’

 Kari ga cewa an yi amfani da sunan Allah a cikin New World Translation, babu kuskure a ciki kuma yana da saukin fahimta, sa’an nan ba a sayar da shi. Saboda haka, miliyoyin mutane suna iya karanta Littafi Mai Tsarki a yarensu, har da wadanda ba su da kudin sayan Littafi Mai Tsarki.