Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Yin Wasu Bukukuwa?

Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Yin Wasu Bukukuwa?

 Ta yaya Shaidun Jehobah suke sanin bukukuwan da suka cancanta?

 Shaidun Jehobah suna bincika Littafi Mai Tsarki kafin su tsayar da shawara ko ya cancanta su sa hannu a wani bikin hutu. Wasu bukukuwan suna taka ka’idodin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, Shaidun Jehobah ba sa yin irin wadannan bukukuwa. A batun wasu bukukuwan kuma, kowanne Mashaidi ne zai tsai da shawarar da zai bi, amma zai yi kokari ya ga cewa ba shi da wani abin “shakka ko wani abin damuwa a gaban Allah da mutane.”​—Ayyukan Manzanni 24:16.

 Ga wasu tambayoyin da Shaidun Jehobah suke wa kansu kafin su tsai da shawara ko ya cancanta su sa yi wani biki. a

  •   Yin bikin hutu yana taka ka’idodin Littafi Mai Tsarki ne?

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ku ware kanku daga gare su, in ji Ubangiji. Kada ku hada kanku da wani abu mai kazanta.”​—2 Korintiyawa 6:​15-17.

     Domin su ware kansu daga koyarwa da ba ta jitu da Littafi Mai Tsarki ba, Shaidun Jehobah ba sa yin bukukuwan da ke da wannan abubuwan.

     Bukukuwa da suke da alaka ko kuma bauta wa allolin karya. Yesu ya ce: “Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta masa.” (Matiyu 4:10) Saboda haka, Shaidun Jehobah ba sa yin bikin Krisimeti da Easter da May Day, domin wadannan bukukuwan suna da alaka da bauta wa allolin karya, ba Jehobah ba. Kari ga haka, Shaidun Jehobah ba sa yin bukukuwa kamar.

    •  Bikin Kwanzaa. Littafin nan Encyclopedia of Black Studies ya ce: An samo sunan nan Kwanzaa daga “yaren Swahili, wato matunda ya kwanza wanda yake nufin ‘ ’ya’yan fari.’ Hakan ya nuna cewa wannan bikin na da alaka da bikin girbi na farko a tarihi Afirka.” Ko da yake wasu suna ganin cewa bikin Kwanzaa ba bikin addini ba ne, littafin nan Encyclopedia of African Religion ya kwatanta bikin da bikin da ake yi a Afirka wanda ake mika amfanin gona na farko ga “alloli da kuma kakanne domin a gode masu.” Haka bikin Kwanzaa wanda ake yi a Amirka take. Ana yin ta ne don nuna godiya rai da kakanne suka ba da.

      Bikin Kwanzaa

    •  Bikin Mid-Autumn Festival. Littafi nan Holidays, Festivals, and Celebrations of the World Dictionary ya ce: “Wannan biki ne na girmama allahiyar wata. Kari ga haka, littafi nan Religions of the World​—A Comprehensive Encyclopedia of Beliefs and Practices ya ce: “Bikin ya kunshi tsafi da bauta wa allahiya.”

    •  Bikin Nauruz (Nowruz). Littafin nan United Nations Educational, Scientific and Cultural Organization ya ce: “Wannan bikin ya samo asali ne daga addinin Zoroastria. A zamanin dā, ranar da ake bikin tana cikin tsarkakkun ranaku a kalandar addinin Zoroastria. . . . A addinin, ana yin wannan bikin ne da rana a lokacin Nowruz don a marabci Ruhun Rana wato [Rapithwin] da ya dawo bayan, Ruhun Hunturu ya kore shi zuwa karkashin kasa a lokacin sanyi.”

    •  Bikin Shab-e Yalda. Littafin nan Sufism in the Secret History of Persia ya ce wannan biki na da ke yi a watan Disamba ya “kunshi bauta wa Mithra,” wato allahn haske. Kuma ana ce bikin na da alaka da bautar allahn rana na Roma da Girka. b

    •  Bikin nuna godiya. Kamar bikin kwanzaa, wannan bikin na da alaka da bikin girbi da ke yi a dā da ke girmama alloli dabam-dabam. Littafi nan A Great and Godly Adventure​​—The Pilgrims and the Myth of the First Thanksgiving ya ce: “Da shigewar lokaci, sai Kiristoci suka soma yin wadannan bukukuwan.”

     Bukukuwan da suka kunshi camfi ko kuma gaskata da yin sa’a. Littafi Mai Tsarki ya ce wadanda suke yin sujada ga allolin sa’a. Suna cikin wadanda suka “ki Yahweh.” (Ishaya 65:11) Shi ya sa Shaidun Jehobah ba sa yin wadannan bukukuwan.

    •  Bikin Ivan Kupala. Littafin nan A to Z of Belarus ya ce: “Mutane sun yi imani cewa a lokacin wannan bikin [Ivan Kupala] ana iya samun ikon yin sihiri sosai kuma kana iya samun wannan ikon yin sihiri idan kana da gaba gadi kuma ka yi sa’a. Asali wannan bikin arna ne da ake yi a lokacin da aka soma zafi. Amma kundin nan Encyclopedia of Contemporary Russian Culture, ya ce “bayan arna sun zama Kiristoci, sai aka hada bikin Ivan Kupala da bikin tuna ranar haihuwar Yohanna mai baftisma.”

    •  Bikin Lunar New Year (bikin sabuwar shekara na mutanen Sin ko Koriya). Littafin nan Mooncakes and Hungry Ghosts​​—Festivals of China ya nuna cewa: “A wannan lokacin a shekara, abin da ya fi muhimmanci ga iyalai, abokai da dangi shi ne su samu sa’a. Kari ga haka za su girmama alloli da ruhohi, su je wurin allolin don su sami sa’a a shekara mai zuwa. A kundin nan Encyclopedia of New Year’s Holidays Worldwide an nuna cewa bikin sabuwar shekara na Koriya “ya kunshi bauta wa kakanni da yin bukukuwa don su kori aljanu. Ban da haka, hakan zai sa su sami sa’a a sabuwar shekara kuma su yi duba don su san abubuwan da za su cim ma a shekarar.”

      Bikin Chinese New Year

     Bukukuwa da ake yi don an yi imani cewa kurwa ba ta mutuwa. Baibul ya ce kurwa tana mutuwa. (Ezekiyel 18:4) Saboda haka, Shaidun Jehobah ba sa yin bukukuwa da aka ambata a gaba da ke daukaka koyarwa cewa kurwa ba ta mutuwa.

    •  All Souls’ Day (Ranar Matattu). Kundin nan New Catholic Encyclopedia ya bayyana cewa wannan rana ne “da ake tunawa da dukan matattu. Tun daga wajen shekara ta 500 zuwa wajen shekara ta 1500, an yi imani cewa kurwa da ke a wani wuri da ake kira purgatori suna fitowa a wannan ranar a matsayin fatalwa da mayu da kwadi da dai sauransu don su cutar da mutanen da suka bata musu rai a dā.”

    •  Bikin Qingming Festival and Hungry Ghost Festival. Ana yi wadannan bukukuwa guda biyu don a girmama kakanni. Littafin nan Celebrating Life Customs Around the World​​—From Baby Showers to Funerals ya ce a lokacin wannan bikin “ana kona abinci da abin sha da kudi don a tabbata cewa matattu ba za su ji yunwa ba ko su ji kishin ruwa ko kuma su rasa kudi.” Littafin ya kara cewa “a watan da ake bikin Hungry Ghost musamman a daren da watan ta yi haske sosai, masu yin bikin sun yi imani cewa a daren dangantaka da ke tsakanin matattu da masu rai yana da danko. Saboda haka, yana da muhimmanci su faranta ran matattu kuma su girmama kakanni.”

    •  Bikin Chuseok. Littafin nan The Korean Tradition of Religion, Society, and Ethics ya ce: A wannan bikin, “ana mika wa matattu abinci da giya.” Suna yin wannan bikin domin sun “yi imani cewa kurwa tana ci gaba da rayuwa bayan da mutum ya mutu.”

     Bukukuwa da ke da alaka da kunigyar asiri. Baibul ya ce: “Mai duba, ko mai maita, ko mai dabo, ko mai sihiri, ko boka, ko mai sha’ani da ruhohi, ko mai hada kai da ruhohin matattu ba. . . . wadannan abubuwa ya zama abin kyama ne ga Yahweh.” (Maimaitawar Shari’a 18:​10-12) Domin Shaidun Jehobah su guji saka hannu a sihiri har da yin duba ba sa yin bikin Halloween ku kuwa wadannan bukukuwa:

    •  Bikin Sinhala and Tamil New Year. Kundin Encyclopedia of Sri Lanka ya nuna cewa “Abubuwan da ake yi a wannan bikin sun kunshi . . . yin hadaya a daidai lokacin da masu duba suka gaya musu don yin sa’a.”

    •  Bikin Songkran. Kundin Food, Feasts, and Faith​​—An Encyclopedia of Food Culture in World Religions ya ce, an samo sunan wannan bikin mutanen Asiya “daga kalmar Sanskrit . .  da ke nufin ‘zagaya’ ko ‘canji,’ kuma bikin na nuna zagayawar rana a sarari.

     Bukukuwa da ke da alaka da ibada a zamanin Musa, kuma an daina su bayan mutuwar Yesu. Baibul ya ce: “Almasihu shi ne cikamakin Koyarwar Musa.” (Romawa 10:4) Har ila, Kiristoci suna amfana daga ka’idodin dokar da aka ba da ta hannun Musa da aka ba wa Isra’ilawa a dā. Amma ba sa yin bukukuwan, musamman bukukuwa da ta nuna zuwan Almasihu don Kiristoci sun yi imani cewa ya riga ya zo. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wadannan abubuwa kamar hoto ne kawai na abin da zai zo, amma Almasihu shi ne ainihin abin.” (Kolosiyawa 2:17) Saboda haka, tun da wasu bukukuwan sun kunshi al’adun da Baibul bai amince da su ba, bukukuwan da aka lissafta a kasa suna cikin wadanda Shaidun Jehobah ba sa yi.

    •  Bikin Hanukkah. Ana yin wannan bikin ne don sake kebe haikalin Yahudawa a Urushalima. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ga shi, Almasihu ya riga ya zo a matsayin Babban Firist na al’amura masu kyau waɗanda suke akwai yanzu. Ya kuma shiga cikin tenti mafi girma kuma mafi kyau, wadda ba mutum ne ya gina ba, wato ba irin ta wannan halitta ba.” (Ibraniyawa 9:11) Ga Kiristoci, wannan haikalin ya sauya wanda ke a Urushalima.

    •  Bikin Rosh Hashanah. Wannan ne rana ta farko a kalandar Yahudawa. A zamanin dā, ana yin hadayu ga Allah a lokacin bikin. (Littafin Ƙidaya 29:​1-6) Amma Yesu Kristi ya “hana yin hadaya da baye-baye” domin yin hakan ba shi da amfani a gaban Allah.​—Daniyel 9:​26, 27.

  •   Shin bikin hutu yana sa addinai cudanya da juna?

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Mene ne ya haɗa masu bi da marasa bi?” Mene ne ya haɗa haikalin Allah da gidan tsafi?​—2 Korintiyawa 6:​15-17.

     Shaidun Jehobah suna yin iya kokarinsu don su yi zaman lafiya da makwabtansu. Kari ga haka, sun san cewa kowa yana da ’yancin zaban abin da zai yi imani da shi kuma suna daraja wannan zabin. Amma suna guje wa yin cudanya da wasu addinai ta yin wadannan abubuwan:

     Bukukuwa da ke daukaka shugabannin addinai ko taro da ke inganta tarayya na addinai dabam-dabam. Allah ya ba wa ’ya’yan Isra’lawa Kasar Alkawari kuma mutanen wurin suna bin addinai dabam-dabam. Ya ce: “Ba za ku ɗaura yarjejeniya tare da su ba, ko da allolinsu. . . . Idan kun . . . yi wa allolinsu sujada, ba shakka zai zama muku tarko.” (Fitowa 23:​32, 33) Saboda haka, Shaidun Jehobah yin bukukuwan hutu kamar wadannan.

    •  Bikin Loy Krathong. Littafi nan Encyclopedia of Buddhism ya nuna cewa a lokacin wannan bikin da ke yi a kasar Thailand, “mutane suna yin kwano da ganye su saka kyandir ko turaren wuta kuma su saka shi a kogi. Sun yi imani cewa yin hakan na dauke rashin sa’a. Ana yin wannan bikin ne don tunawa da misalin da Buddha ya kafa.”

    •  Bikin National Repentance Day. An yi kaulin abin da wani ma’aikacin gwamnati ya fada a jaridar The National na kasar Papua New Guinean newspaper game da wannan biki. Ya ce: “Wadanda suke yin wannan bikin sun amince da koyarwar Krista. Ƙari ga haka, yin bikin yana sa a inganta yadda ake bin ka’idodin Kristi a kasar.

    •  Vesak. Littafi nan Holidays, Festivals, and Celebrations of the World Dictionary ya bayyana cewa “wannan bikin shi ne mafi tsarki a cikin dukan ranaku masu tsarki na mabiyan Buddha. A ranar, suna tuna haihuwar Buddha, da hikimarsa, da mutuwarsa ko kuma shiga yanayin Nirvana.”

      Bikin Vesak

     Bukukuwa da ke bisa ga al’adun mutane da Baibul bai amince da su ba. Yesu ya gaya wa malaman addini cewa: “Saboda al’adarku, kun mai da maganar Allah banza.” Ƙari ga haka, ya dada gaya musu cewa suna yin koyarwar banza domin “suna koyar da dokokin mutane a matsayin kalmar Allah.” (Matiyu 15:​6, 9) Domin bin wannan gargadin, akwai bukukuwa da yawa da Shaidun Jehobah ba sa yi.

    •  Bikin Epiphany (Three Kings’ Day, Timkat, Los Reyes Magos). Masu yin wannan bikin na tunawa ne da masana taurari guda uku da suka ziyarci Yesu ko kuma suna tunawa ne da baftismar Yesu. Littafi nan The Christmas Encyclopedia ya bayyana cewa, “wannan bikin da Kiristoci ke yi ya samo asali ne daga bukukuwan da arna ke yi don girmama allolin kogi da rafi da kuma tafki.” Kari ga haka, littafin nan Encyclopedia of Society and Culture in the Ancient World ya ce bikin Timkat “ya samo asali ne daga al’adun gargajiya.”

    •  Bikin Feast of the Assumption of the Virgin Mary. Masu yin bikin sun yi imani cewa Maryamu ta tafi sama da jikinta na zahiri. Littafin nan Religion and Society​​—Encyclopedia of Fundamentalism ya ce: “Kiristoci a karni na farko ba sa su da irin wannan imanin kuma ba a ambata hakan a Baibul ba.”

    •  Bikin Feast of the Immaculate Conception. Littafin nan New Catholic Encyclopedia ya ce: “Baibul bai koyar cewa an haifi Maryamu ba tare da zunubi ba. . . . Cocin Katolika ne suka kirkiro wannan.”

    •  Bikin Lent. Littafin nan New Catholic Encyclopedia ya bayyana cewa “an soma wannan bikin ne karni hudu da suka shige” wato fiye da shekaru 200 da suka shige, bayan an kammala Littafi Mai Tsarki. Littafin ya dada cewa, “a ranar wannan bikin ana shafa ma masu aminci toka a goshinsu, an soma wannan bikin ne tun daga lokacin da aka yi taron Synod na Benevento a shekara ta 1091.

    •  Bikin Meskel (ko Maskal). Littafin nan Encyclopedia of Society and Culture in the Medieval World ya yi bayyana game da wannan biki da ake yi a kasar Habasha, ya ce: “Sa’ad da aka samu Ainihin Giciye (wato giciyen da aka kashe Yesu a kai), akan hura wuta da yin rawa ana zagaya wutar.” Shaidun Jehobah ba sa amfani da giciye a bautarsu.

  •   Shin bikin na daukaka mutum, kungiya ko kuwa alamar kasar?

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “In ji Yahweh, la’ananne ne mutumin da yake dogara ga dan Adam, wanda ya sa zuciyarsa a kan karfin jiki, wanda zuciyarsa ta juya wa Yahweh baya.”​—Irmiya 17:5.

     Ko da yake suna kaunar mutane, da kuma yin masu addu’a, Shaidun Jehobah ba sa yin wadannan bukukuwa:

     Bikin hutu da ke daukaka sarki ko wani fitaccen mutum. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku daina dogara ga ’yan Adam, wanda kwanakinsu kaɗan ne kawai. Ina amfanin dogara gare su?” (Ishaya 2:22) Saboda haka, Shaidun Jehobah ba sa yin bikin tunawa da ranar haihuwar kowanne sarki.

     Bikin daukaka tutar kasa. Shaidun Jehobah ba sa yin bikin Flag Day. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Mu kiyaye kanmu daga bin allolin ƙarya.’ (1 Yohanna 5:21) Mutane a yau ba sa gani cewa tuta gunki ne. Wani marubuci mai suna Carlton J. Hayes ya ce: “Babban alamar kishin kasa da kuma bauta wa kasa ita ce tuta.”

     Hutu ko bukukuwa da ke daukaka waliyi. Me ya faru sa’ad da wani mai tsoron Allah ya yi wa manzo Bitrus sujada? Baibul ya ce: “Bitrus ya sa ya tashi ya ce, “Tashi, ai, ni ma mutum ne.” (Ayyukan Manzanni 10:​25, 26) Da yake manzo Bitrus da wasu manzanni ba su amince a daukaka su ko yi musu sujada ba, Shaidun Jehobah ba sa yin taro ko kuma bikin da ke daukaka wadanda ake gani cewa waliyai. Ba sa yin wadannan bukukuwan:

    •  Bikin All Saints’ Day. Littafin nan New Catholic Encyclopedia ya ce: “Ana wannan bikin ne don a daukaka waliyai . . . Ba a san asalin wannan bikin ba.”

    •  Bikin Fiesta of our Lady of Guadalupe. Littafi nan The Greenwood Encyclopedia of Latino Literature ya bayyana cewa ana yin wannan bikin ne don “daukaka waliyar da ke kāre kasar Meziko,” wasu sun gaskata cewa wannan waliyar Maryamu mahaifiyar Yesu ce. An ce ta taba bayyana ga wani talaka a shekara ta 1531.

      Bikin Fiesta of Our Lady of Guadalupe

    •  Bikin Name Day. Littafi nan Celebrating Life Customs Around the World​—From Baby Showers to Funerals ya ce: “Wannan bikin ne da ake yi a ranar waliyi da aka haifi yaron ko aka yi masa baftisma ko kuma a lokacin da yake tabbatar wa kowa cewa ya yi imani da koyarwar coci. A wannan lokacin, mutane na yin abubuwan ibada.”

     Bikin siyasa ko kungiyoyi. Baibul ya ce: “Ya fi kyau a nemi wurin ɓuya cikin Yahweh, da a dogara ga mutum.” (Zabura 118:​8, 9) Don su guji nuna cewa suna dogara ga ’yan Adam maimakon Allah don magance matsalolin duniya, Shaidun Jehobah ba sa yin bukukuwan Youth Day ko kuma Women’s Day da ke goyon bayan ’yan siyasa ko kuma kungiyoyi. Kari ga haka, ba yin bikin samun ’yanci da wasu bukukuwa kamar hakan. A maimakon haka, sun dogara ne ga Mulkin Allah don magance matsalar nuna bambancin launin fata da rashin daidaituwa.​—Romawa 2:11; 8:21.

  •   Shin bikin na daukaka wani kasa ko kabila fiye da wasu?

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Lallai, na gane Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karbar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.”​—Ayyukan Manzanni 10:​34, 35.

     Ko da yake yawanci Shaidun Jehobah suna son kasarsu, amma suna guje wa bukukuwa da ke daukaka wata kasa ko kabila fiye da wata kamar yadda aka kwatanta a nan.

     Biki da ke girmama sojoji. Maimako ya goyi bayan yaki, Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Ku kaunaci wadanda ba sa kaunarku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a.” (Matiyu 5:44) Shi ya sa Shaidun Jehobah ba sa yin bikin da ke girmama sojoji, da kuma bukukuwa kamar su:

    •  Bikin Anzac day. Littafin nan Historical Dictionary of Australia ya ce: “Ranar Anzac, rana ce na tunawa da sojojin kasar Ostareliya da Niyu Zilan da kuma tunawa da wadanda aka kashe su a yaki.”

    •  Bikin Veterans Day (Remembrance Day, Remembrance Sunday, ko kuma Memorial Day). Littafin nan Encyclopædia Britannica ya ce: “Wannan bikin na girmama tsoffin sojoji da kuma wadanda aka kashe su a yakin kasar.”

     Bikin tunawa da ranar samun ’yancin kasa. Game da almajiransa Yesu ya ce: “Su ba na duniya ba ne kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yohanna 17:16) Ko da yake suna jin dadin koya game da tarihin kasarsu, Shaidun Jehobah ba sa yin wadannan bukukuwan.

    •  Bikin Australia Day. Littafi nan Worldmark Encyclopedia of Cultures and Daily Life ya ce: “Wannan bikin na tunawa ne da ranar da sojojin Turai suka daga tuta kuma suka bayyana cewa Ostareliya ta samu yanci a shekara ta 1788.”

    •  Bikin Guy Fawkes Day. Littafin nan A Dictionary of English Folklore ya ce: “Wannan ranar tunawa ne da lokacin da ’yan Guy Fawkes tare da wasu ’yan Katolika suka yi yunkurin halaka Sarki James na 1 da kuma Majalisar Dokokin kasar Ingila da bam a shekara ta 1605.”

    •  Bikin Independence Day. Kamus din Merriam-Webster’s Unabridged Dictionary ya ce: “A kasashe da yawa, wannan rana ce da aka kebe don yin bikin samun ’yancin kasa.”

  •   Shin ana lalata a ranar bikin?

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kun riga kun bata lokaci sosai a kan zaman da kuka yi a dā, wato zama iri wanda marasa sanin Allah suke jin dadinsa, wato neman jin dadi na rashin kunya, da sha’awa iri-iri ta jiki, da buguwa, da bukukuwan shaye-shaye, da fitar shan iska ta lalata, har da bautar gumaka, abin kyama ne.”​—1 Bitrus 4:3.

     Saboda haka, Shaidun Jehobah suna guje wa bukukuwa da ake shaye-shaye da bukukuwa rashin kunya. Shaidun Jehobah suna jin dadin shakatawa da abokai, kuma in za su sha giya, sukan daidai. Suna yin iya kokarinsu don su bi umurnin Littafi Mai Tsarki cewa: “Duk abin da kuke yi, ko kuke ci, ko kuke sha, ku yi kome saboda daukakar Allah.”​—1 Korintiyawa 10:31.

     Saboda haka, Shaidun Jehobah ba sa yin bukukuwa da ke inganta rashin kunya da Littafi Mai Tsarki ya ce a guje wa. Hakan ya kunshi bikin Yahudawa da ake kira Purim. Bikin Purim na tunawa da ’yancin da Yahudawa suka samu a karni na biyar kafin haihuwar Yesu ne. Littafin nan Essential Judaism ya ce: “Ana iya kwatanta wannan bikin da bikin Mardi Gras.” Littafin ya dada cewa: “Bikin ya kunshi saka kayan mata da shaye-shaye da surutai da dai sauran su.”

 Shaidun Jehobah da ba sa yin wasu bukukuwa suna son iyalinsu kuwa?

 E. Littafi Mai Tsarki na koya wa mutane su kaunaci iyalinsu da kuma daraja su ko da addininsu ya bambanta. (1 Bitrus 3:​1, 2, 7) Idan Mashaidin Jehobah ya daina yin wasu bukukuwa, wasu a iyalinsa ko danginsa suna iya yin fushi ko bakin ciki ko kuma su ji kamar ya ci amanarsu. Saboda haka, Shaidun Jehobah suna yin iya kokarinsu don su nuna wa danginsu cewa suna kaunar su. Kari ga haka, suna kuma bayyana masu dalilan da ya sa suka yanke wannan shawarar, kuma suna ziyartar danginsu a wasu lokuta dabam.

 Shaidun Jehobah suna gaya wa wasu kada su yi wasu bukukuwa ne?

 A’a. Sun yi imani cewa kowanne mutum zai yanke nasa shawarar. (Joshua 24:15) Shaidun Jehobah suna daraja mutane, ko da addininsu ya bambanta.​—1 Bitrus 3:​1, 2, 7.

a A wannan talifin, ba a lissafta bukukuwa da Shaidun Jehobah suke bukatar guje wa ba, kuma ba a ambata dukan ka’idodin Littafi Mai Tsarki da suka hana yin wasu bukukuwa ba.

b Mithra, Mithraism, Christmas Day & Yalda, by K. E. Eduljee, shafuffuka 31-33.