Koma ka ga abin da ke ciki

Asalin Halloween, Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya ce Game da Shi?

Asalin Halloween, Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya ce Game da Shi?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki bai ambaci Halloween ba. Amma, tushensa da al’adunsa na yau suna nuna cewa bukukkuwa ne da ke suka fito daga koyarwar karya game da matattu da iskoki, ko kuma aljannu.—Duba Littafin “Halloween history and customs.”

 Littafi Mai Tsarki ya yi gargadi cewa: “Kada a tarar da wani daga cikinku . . . mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.” (Kubawar Shari’a 18:10-​12, Littafi Mai Tsarki) Ko da yake wasu suna ganin cewa Halloween bai da wani lahani, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa abubuwan da ake yi game da shi ba su dace ba. A 1 Korintiyawa 10:20, 21, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba ni so fa ku yi zumunta da aljanu. Ba ku da iko ku sha kokon Ubangiji duk da na aljanu.”

Asalin Halloween da al’adunsa

  1.   Samhain: Littafin nan The World Book Encyclopedia ya ce an samo tushen Halloween daga “wannan bikin arna da ’yan Celtic suke yi shekaru 2000 da suka shige. ’Yan Celtic sun yi imani da cewa a lokacin wannan bikin, matattu suna sha’ani da mutane har kuma cewa matattu suna iya ziyarar mutane ma.” Amma Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa “matattu ba su san kome ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Hakan ya nuna cewa ba za su iya sha’ani da mutane ba.

  2.   Kayan ado da alewa, da dabarun Halloween: Littafin nan Halloween​—An American Holiday, An American History, ya ce wasu ’yan Celtic suna yafa tufafi masu tsoratar da mutane da zai sa su yi kama da aljannu don kada iskoki su taba su. Wasu kuma suna ba da kyautar alewa ga iskoki don neman rahama. A kasar Turai, limaman cocin Katolika sun soma yin wannan bikin ta wajen sa ’yan cocinsu su yafa tufafi masu tsoratar da mutane kuma su bi gidajen mutane suna addu’ar kāriya daga iskoki suna kuma bara. Amma Littafi Mai Tsarki ya haramta hada al’adun addinan karya da bautar Allah.​—2 Korintiyawa 6:17.

  3.   Fatalwoyi da aljannu da kuma mayu: Duk wadannan suna cikin duniyar mugayen iskoki. (Halloween Trivia) Littafi Mai Tsarki ya ce mu guje wa iskoki, kada mu daukaka su.​—Afisawa 6:​12.

  4.   Kabewar bikin Halloween: A kasar Britaniya a dā, “masu bara sukan bi mutane a gidajensu suna rokon abinci don su yi musu addu’ar kāriya daga iskoki” kuma su rike “wutar da aka saka cikin albasa da aka huda wanda yake nufin rayuka da aka tsare cikin lahira.” (Halloween​—From Pagan Ritual to Party Night) Wasu sun ce ana amfani da wutar don korin iskoki. A shekarun 1800 a Amirka ta Arewa, an fi yin amfani da kabewa maimakon albasa don akwai kabewa da yawa kuma yana da saukin hudawa. Wannan al’adar da koyarwa karya na kurwa marar mutuwa da lahira da kuma addu’a don matattu ba sa cikin Littafi Mai Tsarki.—Ezekiel 18:4.