Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah Masu Goyon Bayan Addinin Yahudawa Ne?

Shaidun Jehobah Masu Goyon Bayan Addinin Yahudawa Ne?

 A’a, ko kaɗan. Shaidun Jehobah Kiristoci ne da suka gaskata da abin da ke cikin Nassosi. Ko da yake wasu addinai suna koyar da cewa taruwan da Yahudawa ke yi a Falasɗinu yana bisa annabcin Nassi ne, Shaidun Jehovah ba su ganinsa haka. Ba su gaskata cewa Nassosi sun annabta aukuwan da ke faruwa a cikin siyasa ba. Hakazalika, Nassosi ba sa ɗaukaka wani gwamnatin ɗan Adam ko kuma wani ƙabila ko rukuni fiye da wani ba. Hasumiyar Tsaro, jaridar Shaidun Jehobah, ya faɗi da gaba gaɗi cewa: “Nassi bai goyi bayan siyasar da addinin Yahudawa ke sa hannu ciki ba.

 Encyclopædia Britannica ya kwatanta addinin Yahudawa cewa “tsarin Yahudawa masu wariyar ƙabila da ainihin burinsu domin su goyi bayan ƙasarsu ce ta Falasɗinu.” Tushensa dai na addini ne da kuma siyasa. Shaidun Jehobah ba sa goyon bayan koyarwar addinin Yahudawa, kuma suna tsaya da tsaka tsakanci a zancen siyasarsu.

 Ƙungiyar Shaidun Jehobah dai addini ce kawai kuma ba ta goyon bayan wani tsarin siyasa, har da na tsarin Yahudawa ma. Yadda Shaidun Jehobah suka kasance da tsaka-tsakanci yana rubuce, maimakon su karya tsaka-tsakancinsu, a wasu ƙasashe Shaidun sun sha tsanani sosai. Mun tabbata cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai kawo salama madawwamiya a duniyar nan; babu wata gwamnatin ’ɗan Adam ko rukuni da zai iya kawo hakan.

 Ƙa’ida ta ƙwarai da Shaidun Jehobah suke da shi, shi ne a duk inda suke, suna biyayya da dokokin gwamnati. Ba sa tawaye da ikon gwamnati ko kuma sa hannu cikin faɗace-faɗace na ƙasa.