Koma ka ga abin da ke ciki

“Abin da Ya Fi Silima Inganci”

“Abin da Ya Fi Silima Inganci”

A kowace shekara, Shaidun Jehobah suna nuna sababbin bidiyoyi da yawa a taronsu na yanki. A yaren Turanci ne ake tsara yawancin bidiyoyin. Ta yaya mutane da suke halartar taron a wasu yare suke fahimtar bidiyoyin da ake gabatarwa? Ana juya yawancin bidiyoyin nan zuwa wasu yaruka. Duk da cewa da Turanci aka yi bidiyon, ana jin muryoyin a yaren da ake so. Wane tasiri ne wadannan bidiyoyi da ake ji cikin yaruka dabam-dabam yake da shi ga mutanen da suka halarci taron?

Sakamakon da Bidiyoyin Suka Jawo

Bari mu yi la’akari da abubuwan da wasu da ba Shaidun Jehobah ba da suka halarci taron a Meziko da kuma Amirka ta Tsakiya suka ce:

  • Wani da ya halarci taron a yaren Popoluca a Jihar Veracruz da ke Meziko ya ce: “Na fahimci fim din sosai har ma ji nake kamar ina cikin ’yan wasan. Ya ratsa zuciya na kwarai da gaske.”

  • Wani da ya halarci taron a yaren Nahuatl, a jihar Nuevo León da ke Meziko, ya ce: “Ji nake kamar ina hira ne da wani babban aboki na a kyauyenmu. Wannan ya fi sauran fina-finai domin na fahimci kome da kome.”

  • Wata da ta halarci taron a yaren Chol, a jihar Tabasco da ke Meziko, ta ce; “Sa’ad da na kalli bidiyoyin a yarenmu, sai na ji kamar da ni ne ’yan wasan suke magana.”

  • Wani da ya halarci taron a yaren Cakchiquel a birnin Sololá da ke Guatemala ya ce: “Kungiyar nan tana so ta taimaka wa mutane su koya game da Allah a yarensu. Babu wata kungiya kamarta!”

Shaidun Jehobah ba sa yin hayar kwanaye masu aikin na’ura ko kuma ’yan wasa, kari ga haka yawancin aikin daukan murya da suke yi suna yin shi ne a kauyuka, ta yaya ake yin aikin kuma ya fita da kyau?

“Aikin Da Ya Fi Kawo Albarka”

A shekarun baya, ofishin Shaidun Jehobah da ke Amirka ta Tsakiya ta gudanar da aikin kofan bidiyoyin taron yanki zuwa yaren Sifanisanci da kuma wasu yaruka 38 da ake yi a kasar. Mutane 2,500 ne suka ba da kansu don su taimaka a wannan aikin. Masu aiki da na’ura da mafassara sun yi aikin saka wa bidiyoyin sauti a ofishin Shaidun Jehobah a kasar da kuma ofisoshin fassara da ake amfani da su a waje, ko kuma wasu wurare da ake amfani da su na dan lokaci. Sun yi amfani da wurare fiye da 20 a kasar Belize da Guatemala da Honduras da Meziko da kuma Panama don wannan aikin.

Ana daukar murya a ofishin Shaidun Jehobah da ke Amirka ta Tsakiya

Ana bukatar kudi da kuma yin aiki tukuru don a iya shirya dakin daukan murya wato studiyo. Ana amfani da abubuwan da za su hana duk wani surutu shiga rekodin din, ana amfani da abin da aka samo a wurin, kamar bargo da kuma katifa.

Yawancin mutane da ake amfani da su wurin daukar muryoyinsu cikin wasu harsuna lallaba rayuwa suke yi kuma suna yin sadaukarwa sosai don su iya zuwa studiyo da ke kusa da su. Wasu yana daukansu awa 14 kafin su isa! Wani mutum da dansa sun taka da kafa kusan awa takwas kafin su isa studiyon.

Wata mai suna Naomi ta saba taimakon iyalinta shirya wuraren daukar murya tun tana karama har ta girma. Ta ce: “Kullum muna dokin ganin cewa lokacin da za a zo aikin daukar murya ya yi muke. Babana yana aiki tukuru ya ga cewa kome ya tafi daidai. A wasu lokutan mamata takan dafa abinci don ta ciyar da mutanen kusan 30.” Yanzu Naomi tana aiki a ofishin fassara a Meziko. Ta kara cewa: “Ina farin ciki sosai don na ba da lokaci na in taimaka wa mutane su ji sakon da ke Littafi Mai Tsaki a yarensu. Wannan shi ne aiki mafi gamsarwa da zan yi.”

Shaidun Jehobah suna taron yanki a kasashe da yawa a duniya kuma kowa zai iya zuwa. Ka duba shafin nan TARON YANKI don karin bayani.