Koma ka ga abin da ke ciki

Sauke Karatun Aji na 138 na Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gileyad

Sauke Karatun Aji na 138 na Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gileyad

A ranar 14 ga Maris, 2015, aji na 138 na Makarantar Gileyad sun sauke karatu a cibiyar koyarwa ta Shaidun Jehobah a Patterson, New York. Mutane 14,000 sun halarci taron, har da wadanda suka kalla a bidiyo. An soma tsarin ayyukan da sautin sababbin wakokinmu guda hudu, wanda dukan mahalartan suka rera daga baya. *

Dan’uwa Geoffrey Jackson, wanda shi memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne mai kujeran taron. A furucinsa na bude taron, ya karfafa daliban su yi amfani da ilimin da suka samu a makarantar wajen koyar da wasu maimakon boye shi.​—2 Timotawus 2:2.

Dan’uwa Jackson ya tattauna misalin da Musa ya kafa mana. Alal misali, tantin Musa ne wurin da al’ummar Isra’ila suke taruwa don ibada. Amma, sa’ad da aka gina mazauni, an kaurar da shi zuwa mazaunin. Watakila ba a yarda Musa ya shiga cikin wani sashe na mazaunin ba, wato Mafi Tsarki domin babban firist ne kadai yake da izinin shigan wurin. Duk da haka, ba mu taba ji an ce Musa ya yi gunaguni ba don wannan gyarar da aka yi. Maimakon haka, ya kasance da aminci kuma ya goyi bayan Haruna a matsayinsa na sabon babban firist. (Fitowa 33:​7-​11; 40:34, 35) Wane darasi ne hakan ya koya mana? Dan’uwa Jackson ya ce: “Ku daraja kowane gatan da aka ba ku, amma kada ku taba boye iliminku.”

“Shin Karar Ganye Za ta Tsoratar da Ku?” Jigon jawabin da Dan’uwa Kenneth Flodin, wanda shi mataimaki ne ga Kwamitin Koyarwa na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya bayar ke nan. Ya ce daliban za su iya fuskantar matsalolin da za su iya tsoratar da su, kamar tsanantawa ko wani aiki mai wuya. Dan’uwa Flodin ya yi amfani da kalmomin da ke littafin Leviticus 26:36 wajen karfafa daliban cewa kada su dauki irin wadannan yanayin kamar ya fi karfinsu, amma su dauke su kamar busasshen ganyaye. Bayan haka, sai ya nanata yadda manzo Bulus ya dogara ga Jehobah kuma yadda hakan ya taimaka masa ya jimre wa kalubale.​—2 Korintiyawa 1:​8, 10.

“Me Kuke Nema?” Jigon jawabin da Dan’uwa Mark Sanderson, wanda shi memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne ya bayar ke nan. Ya tattauna ka’idar da ke littafin Misalai 13:12, da ta ce: “Muradin da ba a biya ba ya kan sa zuciya ta yi ciwo.” Abin bakin ciki ne cewa mutane da dama suna damuwa har su tsufa su mutu domin sun kafa wa kansu makasudin yin arziki wanda watakila ba za su taba samu ba.

A zamanin Yesu, wasu mutane sun yi zaton banza game da Yohanna Mai-baftisma. (Luka 7:​24-​28) Alal misali, watakila sun dauka cewa zai zama shahararren malamin da zai koya musu abubuwan da suke son ji. Idan abin da suka yi zato ke nan, to sun yi kuskure domin Yohanna ya koyar da gaskiya kai tsaye. Watakila wasu sun yi zato cewa zai kasance mai kyakkyawan sifa. Maimakon haka, Yohanna ya saka tufafin talakawa. Amma, mutanen da suke sauraron annabi ba su damu ba domin Yohanna annabi ne kuma shi ya shirya wa Almasihu hanya!​—Yohanna 1:​29.

Dan’uwa Sanderson ya karfafa daliban su yi zato mai kyau. Ya ce, maimakon neman suna ko kuma jin dadi a hidimarsu, su mai da hankali ga yin amfani da iliminsu wajen amfanar wasu. Za su iya yin hakan ta wajen koya wa wasu abubuwan da suka koya a Gileyad da kuma karfafa bangaskiyar ’yan’uwansu da kuma nuna cewa suna kaunarsu sosai. Ya ce: “Ku zama masu tawali’u kuma ku kokarta ku yi nufin Jehobah. Idan kun yi hakan, ba za ku taba yin da-na-sani ba.”

“Ku Ciyar da Mayunwata.” Jigon jawabin da Dan’uwa James Cauthon, wanda shi malami ne a Makarantun Kungiyar Jehobah ya bayar ke nan. Dan’uwa Cauthon ya ce kowa yana so a kaunace shi, a nuna an damu da shi kuma a san da shi. Ko Yesu ma ya bukaci hakan, kuma Jehobah ya biya bukatunsa.​—Matta 3:​16, 17.

Jehobah ya ba mu damar karfafa da kuma taimaka wa wasu da furucinmu kuma yana so mu yi hakan. (Misalai 3:​27) Dan’uwa Cauthon ya ce: “Ku horar da kanmu don ku rika ganin halaye masu kyau na mutane kuma ku rika karfafa su.” Tun da karfafa ’yan’uwanmu zai taimaka musu, to ku san cewa yin hakan yana da muhimmanci.

“Ku Zama Masu Alheri da Babu Kamarsa.” Dan’uwa Mark Noumair, wanda shi mataimaki ne ga Kwamitin Koyarwa ne ya ba da jawabi na gaba a tsarin ayyukan. Dan’uwa Noumair ya yi amfani da misalin manzo Bulus wajen karfafa daliban cewa kada su gamsu sa’ad da suka yi karamin aikin da aka ba su. Maimakon haka, su yi koyi da Bulus ta wajen neman hanyoyin taimaka wa wasu domin abin da zai sa su farin ciki ke nan.​—Filibiyawa 2:​17, 18.

Bulus bai yi sanyin gwiwa ba duk da matsalolin da ya fuskanta. Domin Bulus ya ci gaba da yin iya kokarinsa har lokacin da ya mutu, za a iya cewa ya yi amfani da dukan karfinsa a hidimar Jehobah. Shi ya sa ya ce: “Na gama tseren.” (2 Timotawus 4:​6, 7, Littafi Mai Tsarki) Dan’uwa Noumair ya karfafa daliban su yi koyi da Bulus ta wajen goyon bayan ayyuka na Mulkin Allah da aka ba su.

Labarai. Dan’uwa Michael Burnett, wanda shi ma malami ne a Makarantar Gileyad ya gudanar da tsarin ayyuka na gaba. A wannan tsarin ayyukan, ya sa daliban su sake nuna abin da ya faru sa’ad da suke wa’azi a Patterson.

Sau da yawa, daliban sun sami sakamako mai kyau domin sun nemi zarafin yin wa’azi ga mutane a yaren da suke ji. Alal misali, an gaya wa wani dalibi cewa akwai ’yan Sifanisawa da yawa a yankin da suke so su yi wa’azi. Saboda haka, dalibin ya yi amfani da na’urar JW Language app don koyan wasu kalmomi a yaren Sifen. A ranar, sai ya tarar da wani dan kasar Sifen a kan hanya. Sai dan’uwan ya yi amfani da kalmomin da ya koya a yaren wajen soma tattaunawa da mutumin, a sakamako, ya soma nazari da mutumin da kuma mutane hudu a iyalinsa.

Ganawa. Bayan haka, Dan’uwa William Turner Karami, wanda shi mataimaki ne ga Kwamitin Hidima na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, ya gana da dalibai hudu. Daliban sun fadi labarinsu kafin su zo Gileyad da kuma horarwa da suka samu a makarantar.

Daliban sun fadi abin da suka fi so a makarantar. Alal misali, wani dalibi ya fadi abin da ya koya daga littafin Luka sura 10. Almajirai 70 da Yesu ya tura wa’azi sun yi farin ciki sa’ad da suka sami sakamako mai kyau. Ko da yake Yesu ma ya yi farin ciki, amma ya koya wa almajiransa cewa kada su mai da hankali ainun ga sakamakon da suka samu, amma su yi murna domin Jehobah yana farin ciki don kokarinsu. Hakan ya tuna mana cewa farin ciki na gaske bai dangana ga yanayinmu ba, amma ga samun tagomashin Jehobah.

Dan’uwa Turner ya bayyana Filibiyawa 1:6 kuma ya gaya wa daliban cewa Jehobah ya riga ya “fara kyakkyawan aiki” a kansu kuma Jehobah zai ci gaba da kasancewa tare da su.

“Ku Rika Kallon Jehobah.” Dan’uwa Samuel Herd, wanda shi memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne ya yi jawabi na musamman a taron. Ya ce ba za mu iya ganin Jehobah ba. To yaya zai yiwu mu rika kallonsa?

Hanya daya da za mu iya ganin Jehobah ita ce ta wajen bincike halittunsa, wanda ke koya mana darussa game da shi. Bugu da kari, Jehobah ya sa ‘idanun zuciyarmu su haskaka.’ (Afisawa 1:​18, LMT) Yayin da muke ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki, za mu dada sanin Jehobah. Kuma hakan zai dada sa dangantakarmu da shi ta yi danko.

Ya kamata mu mai da hankali sosai ga Linjila, domin kalmomi da kuma ayyukan Dansa suna taimaka mana mu san Jehobah sosai. Yesu ya yi koyi da halayen Jehobah sosai shi ya sa ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.”​—Yohanna 14:9.

Dan’uwa Herd ya karfafa mahalartan su ga Jehobah ta wajen yin la’akari da misalin Yesu, kuma su yi koyi da abin da suka gani. Alal misali, kamar yadda Yesu ya yi kokari don ya ciyar da wasu, ya kamata mu ma mu yi kokari don mu koya wa wasu abubuwan da muka koya.

Wane sakamako za mu samu idan muna kallon Jehobah? Za mu kasance da gaba gadi kamar wani marubucin zabura da ya ce: “Na sa Ubangiji a gabana kullum: Da shi ke yana ga hannun damana ba zan jijjigu ba.”​—Zabura 16:8.

Kammalawa. Bayan dukan daliban sun karbi takardar shaidar sauke karatu, sai wani cikin daliban ya karanta wata wasika mai dadi da dukansu suka rubuta. Bayan haka, sai Dan’uwa Jackson ya kammala taron ta wajen gaya wa daliban cewa kada su ji cewa ya kamata dukan koyarwarsu ta zama sabo. Yawancin abubuwan da za su koya wa ’yan’uwansu shi ne abubuwan da sun riga sun sani. Dan’uwa Jackson ya kuma nanata muhimmancin kasancewa da tawali’u. Ya ce kada daliban su mai da hankali ga kansu ko koyarwar da aka yi musu a Gileyad, maimakon haka, su mai da hankali ga Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da suke bayyana shi. Maimakon sa wadanda watakila ba za su taba samun damar halartar makarantar Gileyad sanyin gwiwa, su karfafa ’yan’uwansu ta wajen sa su amfana daga abubuwan da suke da su. Dukan mahalartan sun koma gida cike da farin ciki da kuma kudurin taimaka wa ’yan’uwansu.

Freeman da Miriam Abbey

Joel Acebes

Arsen da Alyona Airiiantc

Aynura Allahverdiyeva

Haja da Lalatiana Andriakaja

Dale da Sonia Clarke

Michael da Katrina Davies

Trent Edson

Aleksandr Fomin

Josué François

Juan Giovannelli

Mark da Jill Hollis

Daniel Jovanović

Hugues da Rachel Kabitshwa

Dong-in Kim

Yura Kucherenko

Robert da Samantha Li

Gilles da Christiane Mba

Kyaw da Hka Tawm Naing

Victor da Ami Namba

Ebenezer da Sonnie Neal

David Nwagu

Meray Razzouk

Sóstenes da Ely Rodrigues

Davy Sehoulia

Eki Soba

Simão Sona

Anja Van Looveren

Gwen Williams

K. Abdiel da Armande Worou

^ sakin layi na 2 An aika wa wadanda za su halarci taron sabon wakar a makon da aka yi taron.

^ sakin layi na 32 Ba dukan kasashen aka nuna a taswirar ba.

^ sakin layi na 34 Ba a saka sunayen dukan wadanda suka sauke karatu ba.