Koma ka ga abin da ke ciki

Sun Sami Tikitin Jirgin Sama Dubu Sha Tara Kyauta!

Sun Sami Tikitin Jirgin Sama Dubu Sha Tara Kyauta!

A watan Yuli na 2013 ne Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta aika wasiƙu zuwa ga masu wa’azi a ƙasar waje da kuma wasu masu hidima ta cikakken lokaci na musamman a ƙasashen waje. Hukumar ta bayyana a wasiƙar cewa an yi wani shiri don a taimaka wa waɗanda ke hidima a ƙasashen waje su halarci taron yanki da na ƙasashe da za a yi daga shekara ta 2014 zuwa farkon 2015.

An yi wannan shirin ne don taimaka wa waɗanda ke hidima a wata ƙasa su halarci manyan taro, kuma su ziyarci danginsu da abokansu. Wasiƙar ta ce ƙungiyar Jehobah za ta biya kuɗin tafiyarsu da dawowarsu.

An yi irin waɗannan shirye-shiryen a dā, amma na wannan shekarar ya bambanta. Kwamitin Koyarwa ya kafa wani sabon sashe a hedkwatarmu, wato Sashen Shirya Tafiye-tafiye don kula da wannan shirin.

Ba da daɗewa ba bayan an aika wasiƙar, sai ’yan’uwa suka soma aika saƙo don a tanadar musu da tikitin jirgin sama. A watan Janairu na 2014, saƙonnin da aka aiko sun yi yawa sosai. Sashen shirin tafiye-tafiye sun yi bincike kuma suka samo tsarin tafiye-tafiye wa masu hidima ta cikakken lokaci na musamman a faɗin duniya.

Wasu tsarin tafiye-tafiyen suna da wuya. Masu tafiya daga birnin Reykjavík, a ƙasar Iceland, suna bukata su je Cochabamba, a ƙasar Boliviya. Wasu da ke Nouméa a ƙasar New Caledonia, suna bukata tikitin zuwa Antananarivo, da ke ƙasar Madagascar. Wasu kuma daga Port Moresby a ƙasar Papua New Guinea, sun yi tafiya zuwa birnin Seattle da ke jihar Washington a ƙasar Amirka, wasu kuma daga birnin Ouagadougou da ke ƙasar Burkina Faso za su je Winnipeg a ƙasar Kanada.

’Yan’uwa biyar da ke aiki a Sashen Shirya Tafiye-tafiye sun saya tikitin guda 19,000. Ta yin amfani da kuɗi da ikilisiyoyi suka ba da gudumawar sa don wannan tafiye-tafiye, sun sayi tikitin tafiya kuma suka tura wa kimani mutane 4,300 daga ƙasashe 176.

Mutane sun nuna godiya sosai don wannan tanadin. Wasu ma’aurata da suke hidima a wata ƙasa sun ce: “Yanzu za mu koma inda muke hidima a kudu maso gabashin Asiya. Muna mutukar godiya don yadda aka taimaka mana mu koma ƙasarmu wato, Ingila kuma mu kasance tare da danginmu da muka rabu da su tun shekara biyar. Da a ce ba a taimaka mana ba, da ba mu iya yin wannan tafiyar ba . Saboda haka, muna mutukar godiya ga dukan waɗanda suka sa hakan ya yiwu.”

Wani mai wa’azi a ƙasar waje da ke hidima a Paraguay ya ce: “Ni da matata muna godiya sosai saboda wannan damar halartan taron ƙasashe a New Jersey da ke ƙasar Amirka. A farkon shekara ta 2011, mun soma yin shirin zuwa Amirka don mu ziyarci hedkwatarmu. Mun yi ajiyar kuɗi don haka. Amma a watan Yuni na shekarar, aka ce mu riƙa ziyarar ikilisiyoyin yaren kurame da ke ƙasar Paraguay. Hakan ya ƙunshi tafiye-tafiye sosai. Bayan mun yi tunanin a kan batun, sai muka manta da shirin zuwa Amirka kuma muka sayi mota don mu yi sabon aikin da aka ba mu da kyau. Sa’an nan sai muka sami takardar gayyata zuwa taron ƙasashe. Abin nema ya samu! Mun gode wa Jehobah sosai don alherinsa da ƙaunarsa da ya nuna mana.”

Wasu ma’aurata daga Malawi sun aika imel cewa: “Muna aika ɗan saƙon imel don mu nuna matuƙar godiyarmu! Mun san cewa an yi aiki sosai kuma ba ƙaramin lokaci da kuɗi aka kashe ba wajen tanadar da waɗannan tsarin tafiye-tafiye da yawa. Muna godiya saboda ƙwazonku da kuma karimci da ƙungiyar Jehobah ta nuna mana ta ba mu damar halartar taron ƙasashe da kuma ganin danginmu.”

Waɗanda suke wannan sashen tafiye-tafiye suna jin daɗin aikinsu. Ɗaya daga cikinsu mai suna Mileivi ta ce: “Taimaka wa masu wa’azi a ƙasashen waje su koma gida kuma su ga iyalansu da abokansu gata ne na musamman.” Dorise ta ce: “Hakan ya sa na fahimci cewa ƙungiyar Jehobah tana ƙaunar waɗanda suke hidima a ƙasashen waje.” Mai kula da sashen mai suna Rodney, ya ce: “Kasancewa a cikin masu yin wannan shirin babban gata ne.”

Shaidun Jehobah a faɗin duniya suna jin daɗin ba da gudummawa don waɗannan ’yan’uwa maza da mata da suke hidima ta cikakken lokaci su sami wannan kyautar.