Koma ka ga abin da ke ciki

Ta’azantar da Kuma Karfafa Tsofaffi

Ta’azantar da Kuma Karfafa Tsofaffi

Tsofaffin sai karuwa suke yi a kasar Australiya, kamar yadda yake a kasashe da yawa. A kan kai wasu tsofaffin a ajiye su a gidajen da ake kula da tsofaffi. Akwai masu aiki a wurin da ke kula da tsofaffin da kuma bukatunsu na kullum.

Babu shakka, ba kulawa da lafiyar jikinsu ne kawai tsofaffi da yawa da ke zama a irin wuraren nan ke bukata ba. A wasu lokuta sukan ji kadaici, ko ma su ji kamar ba su da wani. Shaidun Jehobah suna karfafa da kuma ta’azantar da tsofaffin nan yayin da suke ziyartar irin gidajen tsofaffin nan biyu a Portland, wani gari a Victoria a Australiya.

An Shirya Jawabai Daga Littafi Mai Tsarki Musamman Saboda Gidajen da ake Kula da Tsofaffi

Shaidun Jehobah da ke wurin suna zuwa su tattauna darussa daga Littafi Mai Tsarki, kamar wani labari a rayuwar Yesu tare da tsofaffin. Wani dan’uwa mai suna Jason ya ce: “Mukan karanta wani wuri daga cikin Littafi Mai Tsarki tare da tsofaffin, sai kuma mu tattauna labarin da su.” Da yake yawancinsu suna fama da rashin lafiya, Shaidun suna karfafa su da kuma ta’azantar da su ta wurin tattauna alkawarin da Allah ya yi cewa zai cire cuta da kuma mutuwa.

Wani cikin Shaidun mai suna Tony ya ce: “Mun soma ne da kai masu ziyara na rabin awa, amma tsofafin sun ce a kara lokacin. Saboda haka, muna yin awa daya a wurin, ko da yake wata cikin tsofaffin ta ce tana son su yi awa biyu!” Da yake wasu cikin tsofaffin ba sa gani, wasu kuma ba sa iya barin wurin kwanciyarsu ko kuma rike wani abu da hannayensu, Shaidun suna taimaka musu sa’ad da suke tattaunawa da su kuma suna karfafa su su yi kalamai.

A duk lokacin da Shaidun suka kai ziyarar, sukan rera wakokin yabo ga Allah tare da tsofaffin, sau da yawa tsofaffin sukan ce a ci gaba da rera wakokin. * Daya daga cikin tsofaffin mai suna John, ya ce: “Muna jin dadin wakokinku. Yana taimaka mana mu san Allah kuma mu daraja shi.” Wata tsohuwa mai suna Judith makauniya ce, amma ta haddace duk kalmomin wakokin da ta fi so!

Shaidun Jehobah suna kulawa da lafiyar kowanne cikin tsofaffin. Wani mai suna Brian da ke aiki ba da kai a wurin ya ce idan wani bai da lafiya cikin tsofaffin, Shaidun sukan je wurinsu a dakinsu. “Mukan yi hira da su kuma mu ga yadda suke ji. A wasu lokuta ma, mukan dawo wata rana dabam don mu ga yadda marar lafiyar ya sami sauki.”

“Allah Ne Ya Turo Ku Wurinmu”

Gidajen kula da tsofaffi da yawa suna jin dadin irin ziyarar nan. Wani mai suna Peter ya ce: “Marmari nake yi kullum” don wannan tattaunawar kowane mako. Judith takan ce wa mai kula da ita: “Yau fa ranar Laraba ce!” Don Allah ki shirya ni don in hallarci nazarin Littafi Mai Tsarki. Ba na son in makara.

Tsofaffin suna jin dadin abin da suke koya sosai, kuma hakan ya sa sun fi kusa da Allah fiye da da. Bayan sun tattauna wata koyarwa da Yesu ya yi, sai wani mai suna Robert ya ce: “Ban taba fahimtar wurin nan cikin Littafi Mai Tsarki ba. Amma yanzu na gane!” Wani ma mai suna David ya koyi muhimmancin yin addu’a, kuma ya ce: “Addu’a ya taimaka mini in kulla dangantaka na kud da kud da Allah kuma hakan ya sa na san shi sosai yanzu.”

Tsofaffin na farin cikin sanin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce Allah zai yi a nan gaba. Wata tsohuwa mai suna Lynette ta ce wa Shaidun, “mun gode sosai da kuke ta’azantar da mu da kalmomin Littafi Mai Tsarki.” Wata tsohuwar kuma ta ce: “Allah ne ya turo ku wurinmu!”

Margaret ta ji dadin ziyarar da ake yi musu sosai, hakan ya sa tana halartar taron Shaidun Jehobah a Majami’ar Mulki da ke kusa da su. Hakan bai kasance mata da sauki ba domin rashin lafiya kuma ba ta iya tafiya sosai. Ta ce: “Kun taimaka mana mu kasance da bege a rayuwa.”

‘Abin da KuKe Yi Yana da Kyau Sosai’

Masu aiki a gidajen da ake kula da tsofaffin ma suna jin dadin ziyarar da Shaidun suke yi. Wata cikin Shaidun mai suna Anna ta ce: “Wadanda ke aiki a gidajen da ake kula da tsofaffi suna karfafa tsofaffin su rika halartar tattaunawar da ake yi domin sun ga cewa sai murna tsofaffin ke yi duk lokacin da suka halarci taron.” Brian da aka ambata dazu ya dada da cewa: “Ma’aikatan suna marabtar Shaidun Jehobah din kuma suna nuna masu hadin kai. Suna yin duk iya kokarin son su taimaka.”

Iyalan tsofaffin suna murna sosai ganin cewa tsofaffinsu na jin dadin tattaunawar da ake yi da su. Diyar wata daga cikin tsofaffin ta yaba wa Shaidun, ta ce: “Abin da kuke yi wa mahaifiyata yana da kyau sosai.”

^ sakin layi na 7 An canja sunayen tsofaffin.