Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DEA/G. Dagli Orti/De Agostini via Getty Images

Yadda Huldrych Zwingli Ya Nemi Sanin Gaskiya da ke Cikin Littafi Mai Tsarki

Yadda Huldrych Zwingli Ya Nemi Sanin Gaskiya da ke Cikin Littafi Mai Tsarki

 A yau, yawancin mutane masu zuciyar kirki za su iya bincika ko abin da suka yi imani da shi ya yi daidai da koyarwar Littafi Mai Tsarki ko babu. Amma ba hakan yake ba a farkon karni na 16. Me ya sa? Domin yawancin mutane ba su da Littafi Mai Tsarki kuma ba za su iya karanta shi a yarensu ba. Shi ya sa, kalilan mutane da suke zuwa coci ba sa iya gwada abin da ake koya musu a coci da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Limaman addinai kuma ba su iya taimaka musu ba. Littafin History of the Christian Church ya ce, “Cocin da ke Siwizalan ba su da gaskiya. Limaman jahilai ne masu bin alꞌadu da camfi, da kuma masu lalata.”

 A lokacin nan ne Huldrych Zwingli ya soma neman sanin gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Me ya gano? Ta yaya ya gaya wa mutane abin da ya koya? Mene ne za mu iya koya daga irin rayuwar da ya yi, da kuma imaninsa?

Yadda Zwingli Ya Soma Neman Sanin Gaskiya

 Lokacin da yake shekara 20 da wani abu, Zwingli ya so ya zama firist a cocin Katolika. A lokacin, wajibi ne duk wanda yake so ya zama firist ya sami ilimin falsafa da alꞌadun cocin da kuma koyarwa Shugabannin Coci da ba na Littafi Mai Tsarki ba.

 Ta yaya Zwingli ya gano koyarwar gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki? Saꞌad da yake jamiꞌa a birnin Basel da ke kasar Siwizalan, ya halarci jawaban Thomas Wyttenbach wanda ya ce wasu tsarin dokokin coci a ba su dace ba. Wani marubucin tarihi ya ce, Zwingli “ya koyi daga [Wyttenbach] cewa Kristi ya mutu sau daya tak ba kari don zunubanmu.” (1 Bitrus 3:18) Saꞌad da Zwingli ya fahimci cewa ta fansar Yesu ne kadai za a iya gafarta mana zunubanmu, sai ya ki koyarwa cewa shugabanan coci za su iya gafarta zunubai idan aka ba su kudi. (Ayyukan Manzanni 8:20) Duk da haka, Zwingli ya ci gaba da makaranta kuma ya zama faston Katolika saꞌad da yake dan shekara 22.

 Saꞌad da Zwingli yake dan shekara 20 da wani abu, ya koya wa kansa Grika don ya fahimci asalin yaren da aka rubuta sashen Littafi Mai Tsarki da muke kiran Sabon Alkawari. Ya karanta rubuce-rubucen Erasmus kuma ya koyi cewa Yesu ne mai tsayawa tsakanin Allah da mutane kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki. (1 Timoti 2:⁠5) Hakan ya sa Zwingli ya soma shakkar koyarwar Katolika da suka ce sai ta wurin waliyi ne mutum zai iya yi wa Allah magana.

 Zwingli ya kara kwazo don sanin gaskiya saꞌad da yake dan shekara 30 da wani abu. Amma, yana cikin wadanda suka yi wa sojoji adduꞌoꞌi da hidimomi a lokacin da aka yi yake-yaken a Turai don su mallaki Italiya. A yakin da aka yi a birnin Marignano a shekara ta 1515, ya ga yadda ꞌyan Katolika suka kashe dubban ꞌyan Katolika. Bayan wasu shekaru, Zwingli ya kofa da kuma hadacce Nasossin Helenanci. A shekara ta 1519, ya soma zama a birnin Zurich, kuma wurin ita ce cibiyar siyasa ta kasar Siwizalan. A wurin ne ya amince cewa ya kamata coci su daina koyar da duk wani abin da ba za su iya nuna wurin da yake a Littafi Mai Tsarki ba. Amma, ta yaya zai taimaka wa mutane su amince da abin da ya gano?

“Ba Mu Taba Jin Irin Wannan Waꞌazin Ba”

 Zwingli ya gaskata cewa mutane za su ki koyarwar karya idan suka ji koyarwa ta gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, saꞌad da ya zama firist a wani sanannen cocin Grossmünster da ke Zurich, sai ya soma wani waꞌazi dabam da ya ba mutane mamaki. Bai kara karanta wani littafin b da aka rubuta a yaren Latin da limamai suke maimaitawa shekara da shekaru ba. Maimakon haka, ya yi waꞌazi da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki daga farko har karshe. Yakan yi amfani da wasu ayoyi don ya bayyana Littafi Mai Tsarki maimakon ya yi amfani da abin da limaman coci suke fada don ya yi hakan. Ya yi hakan ta wajen yin amfani da ayoyin Littafi Mai Tsarki da suke da saukin fahimta don ya bayyana masu wuya.​—⁠2 Timoti 3:⁠16.

Sergio Azenha/Alamy Stock Photo

Cocin Grossmünster da ke Zurich

 Yayin da Zwingli yake waꞌazi, yakan nuna wa mutane cewa Littafi Mai Tsarki yana da amfani a rayuwarsu na yau da kullum. Ya koyar da yadda za a bi kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki game da dabiꞌa mai kyau. Ya bayyana cewa bai dace ba a yi wa Maryamu mamar Yesu sujada. Kari ga haka, ya haramta yin amfani da waliyi wajen yin adduꞌa ko a biya limamai don su gafarta zunubai ko kuma yadda limamai suke lalata. Yaya mutane suka ji game da wannan waꞌazi? Bayan jawabinsa na farko, wasu sun ce: “Ba mu taba jin irin wannan waꞌazin ba.” Wani dan tarihi ya rubuta game da Katolikawa masu sauraron Zwingli cewa: “Wadanda suka daina zuwan coci don sun tsani halaye da lalata na limaman suka dawo.”

 A shekara ta 1522, limamai sun yi kokari su sa ꞌyan siyasa da ke birnin Zurich su sa mutane su daina yin kome da zai saba wa koyarwar coci. Shi ya sa suka hukunta Zwingli da laifin ta da zaune tsaye. Don ba ya so ya bar bin abubuwan da ya gano, sai ya daina aikin firist na Katolika.

Mene ne Zwingli Ya Yi?

 Zwingli ya ci gaba da waꞌazi da kwazo ko da yake ya daina aikin firist, kuma ya ci gaba da gaya wa mutane abin da ya yi imani da shi. Mutane da yawa sun san shi don waꞌazi da yake yi, kuma hakan ya sa ꞌyan siyasa da ke Zurich sun saurare shi. Don ya san ꞌyan siyasa da yawa, ya yi kokari ya sa a canja tsarin koyarwar addini a Zurich. Alal misali, a shekara 1523, Zwingli ya gaya wa hukumomin kafa dokoki su hana duk koyarwar addini da ba ya cikin Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 1524, ya gaya musu a hana bautar gumaka. Hukumomi tare da fastoci da limamai a yankin da kuma mutanen suka halaka bagadai da gumakai da kuma sifofi da yawa. Littafin nan Zwingli​—⁠God’s Armed Prophet ya ce: “Ban da lokacin da sojojin Vikings suka farfashe gidajen addini, ba a taba gani yadda aka halaka cococi da yawa kamar a lokacin Zwingli ba. A shekara ta 1525, ya sa hukumomi su mai da gidajen coci zuwa asibitoci kuma a bar maza da mata da suke hidima a coci su yi aure. Kari ga haka, Zwingli ya ce su daina yin Mass yadda suke yi amma su ci jibin maraice na Ubangiji bisa yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki. (1 Korintiyawa 11:​23-25) ꞌYan tarihi sun ce abubuwan da Zwingli ya yi sun kawo hadin kai tsakanin ꞌyan siyasa da addini na Zurich. Kuma hakan ya sa aka yi gyare-gyare a addinai kuma aka kafa sabon cocin Farostatan.

Juyin Littafi Mai Tsarki na Zurich na shekara ta 1536 da ke Hedkwatar Shaidun Jehobah a Warwick, jiyar New York

 Aiki mafi muhimmanci da Zwingli ya yi shi ne fassara Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 1520 zuwa 1529, ya yi aiki tare da wani rukunin masana da suke amfani da Ibrananci da Helenanci na asali da Greek Septuagint da kuma Latin Vulgate. Yadda suka aikin yana da sauki. Sukan karanta kowace aya daga ainihin yaren da kuma wasu fassara masu kyau. Sai su tattauna abin da ayar take nufi kuma su rubuta abin da suka gano. Sun bayyana da kuma fassara Kalmar Allah, hakan ya sa aka samu littafi daya da ake kiran Littafi Mai Tsarki na Zurich a shekara ta 1531.

 Ko da yake Zwingli mai son gaskiya ne, yana masa wuya ya amince da raꞌayin wasu kuma yana da fushi. Alal misali, a shekara ta 1525, ya saka hannu wajen hukunta wadanda ba su amince da yi wa jarirai baftisma ba. Saꞌad da kotu ta yanke hukuncin kisa ga wadanda suka ci gaba da kin yi wa jarirai baftisma, bai hana su. Kari ga haka, ya yi amfani da karfin soja don ya tilasta wa mutane su amince da sabbin koyarwa. Amma, yankuna da dama a Siwizalan da su ꞌyan Katolika ne sun ki bin raꞌayinsa. Hakan ya sa aka soma yaki. Zwingli ya shiga filin daga tare da sojoji daga Zurich kuma a lokacin ne aka kashe shi saꞌad da yake shekera 47.

Abin da Zwingli Ya Yi

 Babu shakka abubuwan da Huldrych Zwingli ya yi ya kawo canji, ko da yake ba a san da shi sosai ba kamar su Martin Luther da John Calvin da suka yi canje-canje a cocin Farostatan. Zwingli ya ki koyarwar Cocin Katolika ba kamar Luther ba kuma abin da ya yi ya sa ya yi wa mutane sauki su amince da koyarwar Calvin. Shi ya sa aka ce shi ne mutumi na uku da ya yi canje-canje sosai.

 Abubuwan da Zwingli ya yi yana da sakamako mai kyau da marar kyau. Don ya yada raꞌayinsa, ya saka hannu a siyasa da kuma yaki. Ta yin hakan, bai bi misalin Yesu Kristi da ya ki saka hannu a siyasa kuma ya koya wa almajiransa su kaunaci makiyansu, kada su kashe su.​—⁠Matiyu 5:​43, 44; Yohanna 6:​14, 15.

 Duk da haka, Zwingli ya karanta Littafi Mai Tsarki sosai, kuma ya kudiri niyya ya gaya wa mutane abin da ya koya. Ya gano koyarwar Littafi Mai Tsarki da yawa kuma ya taimaka wa mutane da dama su yi hakan.

a Dokokin da shugabanan coci suka kafa don a rage ko kawar da hukuncin da za a yi wa mutane a gidan azaba saꞌad suka mutu.

b Wani littafi da ke dauke da ayoyin Littafi Mai Tsarki da ake karantawa a cikin shekara daya.