Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Za Mu Iya Faranta wa Allah Rai Kuwa?

Za Mu Iya Faranta wa Allah Rai Kuwa?

Ka taɓa karanta labarin wasu da aka yaba musu sosai a Littafi Mai Tsarki kuma ka ce wa kanka, ‘Ba zan iya zama kamar waɗannan mutanen ba!’ Kana iya cewa, ‘Ni ba kamili da kuma mai adalci ba ne kuma ba na yin abin da ya dace a koyaushe.’

Ayuba “kamili ne mai-adalci” kuma.—Ayuba 1:1

Littafi Mai Tsarki ya ce Ayuba “kamili ne mai-adalci” kuma. (Ayuba 1:1) Ya kuma ce Lutu “mai-adalci” ne. (2 Bitrus 2:8) Kuma ya ce Dauda ya “yi abin da ke daidai” a idanun Allah. (1 Sarakuna 14:8) Amma bari mu tattauna wasu abubuwa game da rayuwar waɗannan mutanen. Za mu ga cewa sun yi (1) kura-kurai, (2) za mu iya koyan darussa daga wurinsu, kuma (3) zai yiwu ’yan Adam ajizai su faranta wa Allah rai.

SUN YI KURA-KURAI

‘[Allah] ya ceci Lutu adali, wanda fajircin kangararru ya bakinta masa rai ƙwarai.’—2 Bitrus 2:7

Ayuba ya fuskanci matsaloli dabam-dabam kuma ya ji kamar ana masa rashin adalci. Saboda haka, ya kasance da ra’ayi marar kyau domin ya yi zato cewa Allah bai damu ko shi mai adalci ne ko marar adalci ba. (Ayuba 9:20-22) Ayuba ya tabbata sosai cewa shi mai adalci ne har ya soma ji kamar ya fi Allah adalci.Ayuba 32:1, 2; 35:1, 2.

Lutu ya yi jinkirin yanke shawarar da ta dace. Lalatar mutanen Saduma da Gwamarata ta sa shi baƙin ciki sosai har “ya azabtar da ransa mai-adalci” domin ayyukansu. (2 Bitrus 2:8) Allah ya gaya wa Lutu cewa yana so ya halaka biranen kuma ya ba shi da iyalinsa damar tsere wa halakar. Shin Lutu ya bar birnin da gaggawa kuwa? A’a. Ya yi jinkiri a wannan lokacin. Har sai da mala’ikan da aka tura wajensu ya kama hannunsu kuma ya fitar da su daga birnin.—Farawa 19:15, 16.

Dauda ‘ya bi [Allah] da dukan zuciyarsa, domin ya yi abin da ke daidai a idanun [Allah] kaɗai.’—1 Sarakuna 14:8

Dauda ya taɓa kasancewa da rashin kamun kai kuma hakan ya sa ya yi zina da matar wani. Abin baƙin ciki, ya kashe mijin matar garin neman ya rufe wa kansa asiri. (2 Sama’ila, sura ta 11) Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “bai ji daɗin mugun abin da Dauda ya yi ba.”—2 Sama’ila 11:27.

Ayuba da Lutu da kuma Dauda sun yi kura-kurai, wasu masu tsanani ne sosai. Amma za mu tattauna yadda suka nuna cewa suna so su bauta wa Allah da aminci da kuma zuciya ɗaya. Sun kasance a shirye su nuna cewa laifin da suka yi bai dace ba kuma su yi gyara a inda suke bukatar yin hakan. Shi ya sa Allah ya amince da su kuma Littafi Mai Tsarki ya ce su amintattu ne.

WANE DARASI NE ZA MU IYA KOYA?

Babu yadda za mu guji yin kura-kurai domin mu ajizai ne. (Romawa 3:23) Amma idan hakan ya faru, muna bukatar mu nuna cewa muna da-na-sani kuma muna so mu yi gyara.

Ta yaya Ayuba da Lutu da kuma Dauda suka yi gyara? Ayuba mutumi ne mai aminci. Sa’ad da Allah ya yi wa Ayuba gyara, ya amince da hakan kuma ya yi da-na-sani don abubuwan da ya faɗa. (Ayuba 42:6) Allah ya tsani lalatar da mutanen Saduma da Gwamarata suke yi, Lutu ma haka. Matsalarsa kawai ita ce jinkirin da ya yi. Daga baya ya fita daga birnin kuma ba a halaka shi ba. Lutu ya yi biyayya ta wajen ƙin juya baya don ya kalli abubuwan da ya bari. Ko da yake Dauda ya yi laifi mai tsanani ta wajen taka dokar Allah, ya tuba kuma ya nemi gafara. Hakan ya nuna cewa yana ƙaunar Allah sosai.—Zabura ta 51.

Yadda Allah ya bi da waɗannan mutanen ya yi daidai da ra’ayinsa game da ’yan Adam ajizai. Allah “ya san abin da aka yi mu da shi, yakan tuna, da ƙura aka yi mu.” (Zabura 103:14, Littafi Mai Tsarki) Idan Allah ya san cewa ba zai yiwu mu guji yin kura-kurai ba, to, wane ra’ayi ne yake so mu kasance da shi?

Allah “ya san abin da aka yi mu da shi, yakan tuna, da ƙura aka yi mu.”—Zabura 103:14

TA YAYA MUTANE AJIZAI ZA SU IYA FARANTA WA ALLAH RAI?

Shawarar da Dauda ya ba ɗansa Sulemanu ta nuna abin da ya kamata mu yi don mu faranta wa Allah rai. Dauda ya ce: “Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na [ubanka], ka bauta masa da zuciya ɗaya.” (1 Labarbaru 28:9, LMT) Mene ne furucin nan zuciya ɗaya yake nufi? Yana nufin zuciyar da ke ƙaunar Allah kuma ke son yin nufinsa. Ba ya nufin kamiltacciyar zuciya, amma zuciyar da ke marmarin bauta wa Allah cikin aminci kuma take a shirye ta yi gyare-gyare. Allah ya kira Ayuba “kamili,” Lutu “mai-adalci” kuma Dauda mutumin da ke yin “abin da ke daidai” a idanun Allah a koyaushe domin sun ƙaunace shi kuma sun yi ɗokin yin biyayya gare shi. Ko da yake sun yi kura-kurai, amma sun yi abubuwan da suka faranta wa Allah rai.

Zuciya ɗaya tana nufin zuciyar da ke ƙaunar Allah kuma ke son yin nufinsa

Saboda haka, idan mun yi tunanin banza ko mun yi wani abu da daga baya muka san cewa bai dace ba, ya kamata mu yi la’akari da misalan da muka tattauna a wannan talifin. Allah ya san cewa mu ajizai ne. Amma yana so mu ƙaunace shi kuma mu ƙoƙarta don mu yi masa biyayya. Idan muna bauta wa Allah da zuciya ɗaya, za mu iya kasance da gaba gaɗi cewa mu ma za mu iya faranta masa rai.