Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mazaje—Ku Tabbatar da Kwanciyar Hankali a Iyalinku

Mazaje—Ku Tabbatar da Kwanciyar Hankali a Iyalinku

MENE NE ya kamata mazaje su yi don su sa matansu su kasance da kwanciyar hankali? Mutane da yawa sun yarda cewa hakkin mazaje shi ne su sa iyalansu su zama masu arziki. Amma, wasu matan aure da suke da kayan duniya da yawa ba su da kwanciyar hankali kuma suna yawan fargaba. Alal misali, Rosa wata ’yar ƙasar Sifen ta ce: “Idan maigidana yana tare da mutanen waje, shi mala’ikan Allah ne, amma idan ya dawo gida, tsabar rashin imani gare shi.” Joy wata ’yar Najeriya ta ce: “A dā, idan ra’ayina ya bambanta da na maigidana a kan wani batu, sai ya ce ‘Dole ne ki yi duk abin da na ce domin ni ne mijinki.’”

Ta yaya namiji zai cika hakkinsa a matsayin maigida mai kula da iyalinsa? Me ya kamata maigida ya yi don iyalinsa ta kasance da kwanciyar hankali, kuma gidansu ya zama wurin “hutawa” ga matarsa?—Ruth 1:9.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊA GAME DA SHUGABANCIN MAZAJE

Ko da yake a gaban Allah tamace da namiji suna da matsayi ɗaya, Littafi Mai Tsarki ya ce kowannensu yana da hakkinsa a cikin iyali. Romawa 7:2 ta ce mace mai aure tana ƙarƙashin ‘shari’ar mijinta.’ Kamar yadda kowace ƙungiya takan naɗa shugaban da zai riƙa tsara ayyukanta, haka ma Allah ya naɗa maigida a matsayin shugaban mace. (1 Korintiyawa 11:3) Mazaje ne ya kamata su ja-goranci iyalansu.

Mazaje, mene ne ya kamata ku yi da ikon da Allah ya ba ku? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya.” (Afisawa 5:25) Ko da yake Yesu Kristi bai yi aure ba, misalin da ya kafa zai iya taimaka maka ka zama mijin kirki. Bari mu ga yadda hakan zai yiwu.

RAYUWAR YESU MISALI NE MAI KYAU GA MAZAJE

Yesu ya ƙarfafa kuma ya taimaka wa mutane. Yesu ya yi alkawari ga dukan waɗanda ake zalunta da waɗanda suke ji da matsaloli cewa: “Ku zo gare ni, . . . ni kuwa in ba ku hutawa.” (Matta 11:28, 29) A kowane lokaci yana taimaka wa mutane da suke shan wahala kuma yana sa su kusaci Jehobah. Shi ya sa mutane da yawa suka zo wurin Yesu domin sun san cewa zai taimake su.

Yadda mazaje za su bi misalin Yesu. Ku taimaka wa matanku da yin wasu aikace-aikacen gida. Matan aure da dama sun yarda da abin da Rosa ta faɗa cewa: “Mijina ya mai da ni baiwarsa kawai.” Akasin wannan maigidan, wani mai suna Kweku da ke jin daɗin aurensa ya ce: “Nakan ce wa matata ta ba ni aikin da zan taimake ta yi. Nakan taimaka mata da ayyukan gida domin ina sonta sosai.”

Yesu ya tausaya wa mutane kuma ya nuna masu sanin yakamata. Wata mata ta sha wuya har tsawon shekaru 12 da wani ciwo mai tsanani. Sa’ad da ta ji cewa Yesu yana da ikon warkar da ita, sai ta ce: “Idan na taɓa ko tufafinsa kaɗai, zan sami lafiya.” Gaskiyarta. Da ta taɓa rigar Yesu sai ta warke farat ɗaya. Mai yiwuwa, wasu a wurin sun ga kamar matar ta yi taurin kai, amma Yesu ya fahimci cewa tana cikin damuwa ne. * Sai ya ce mata: “Ɗiya, . . . ki rabu da azabarki.” Yesu bai kunyatar da ita ba kuma bai tsawata mata ba, ya dai amince cewa ta sha azaba. Ta haka, ya nuna cewa shi mutumi ne mai tausayi.—Markus 5:25-34.

Yadda mazaje za su bi misalin Yesu. Idan matanku suna rashin lafiya, ku bi da su cikin haƙuri da tausayi. Ku ƙoƙarta ku fahimci yanayinsu da kuma ra’ayinsu. Alal misali, Ricardo ya ce: “A duk lokacin da na lura cewa matata ta soma saurin fushi, ina iyakacin ƙoƙari in guji faɗin abin da zai daɗa sa ta fushi.”

Yesu ya tattauna da almajiransa sosai. Yesu ya tattauna da abokansa sosai. Ya ce musu: “Dukan abin da na ji daga wurin Ubana, na sanar muku da su.” (Yohanna 15:15) A gaskiya, akwai lokatan da Yesu ya kasance shi kaɗai don ya yi tunani da kuma addu’a. Amma sau da yawa, ya gaya wa almajiransa abin da ke zuciyarsa. A daren Yesu na ƙarshe kafin a kashe shi, ya gaya musu cewa yana baƙin ciki sosai. (Matta 26:38) Ko a lokacin da waɗannan abokansa suka yi abubuwan da suka ɓata masa rai ma, Yesu bai daina magana da su ba.—Matta 26:40, 41.

Yin tunani a kan misalin Yesu zai taimaka wa mutum ya zama miji da kuma uban kirki

Yadda mazaje za su bi misalin Yesu. Ku riƙa tattaunawa da matanku, ku gaya musu ra’ayinku da kuma yadda kuke ji. Mace tana iya cewa maigidanta yana taɗi sosai da mutane a waje, amma idan ya zo gida sai ya yi gum. Amma ka lura da abin da wata mai suna Ana ta faɗa a kan yadda take ji a duk lokacin da maigidanta ya gaya mata tunaninsa. Ta ce: “Hakan yana tabbatar min cewa yana ƙaunata sosai kuma hakan yana sa in kusace shi.”

Kada ka ƙi yin magana da matarka don ta ɓata maka rai. Wata mata ta ce: “Idan maigidana yana fushi da ni, sai ya ƙi yin magana da ni har na tsawon kwanaki. Yana sa in riƙa tunanin laifin da na yi kuma in ji kamar ni ba kome ba.” Amma Edwin yana ƙoƙari ya bi misalin Yesu. Ya ce: “A duk lokacin da na yi fushi, ba na mai da martani nan da nan, amma ina jira sai lokacin da ya dace kafin mu tattauna matsalar da yadda za mu sasanta.”

Joy, wadda aka yi ƙaulinta a farkon talifin nan ta lura da yadda halin maigidanta ya canja tun lokacin da ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Joy ta ce: “Ya yi gyara sosai a halinsa kuma yana iyakacin ƙoƙarinsa ya bi misalin Yesu a yadda yake ƙaunata.” Ma’aurata da yawa suna amfana daga umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Kai ma za ka so ka amfana? Za ka iya gaya ma wani Mashaidin Jehobah ya zo ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kyauta.

^ sakin layi na 10 A cikin Dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa, yanayin da wannan matar take ciki ya sa ta zama marar tsarki kuma duk wanda ta taɓa, shi ma zai zama marar tsarki.—Levitikus 15:19, 25.