Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ya Kamata Ka Ji Tsoron Ƙarshen Duniya?

Ya Kamata Ka Ji Tsoron Ƙarshen Duniya?

Yaya ka ji game da rana ta 21 ga Disamba, 2012, wato, ranar da mutane da yawa suka ce za a yi gagarumin canji a duniya baki ɗaya? Mai yiwuwa hankalinka ya kwanta ko ka yi baƙin ciki, ko kuma ka fid da rai a kan duk wani zancen da ake yi game da ƙarshen duniya. Shin, wannan ɗaya ne cikin annabci da yawa da ake yi game da ƙarshen duniya da ba za su taɓa cika ba?

Mene ne kake gani zai faru a “ƙarewar” duniya? (Matta 24:3, Littafi Mai Tsarki) Wasu suna ganin cewa duniya za ta ƙone kurmus kuma hakan na ba su tsoro. Wasu kuma suna marmarin ganin abin da zai faru a ƙarshen duniya. A wani ɓangaren kuma, mutane da yawa sun gaji da jin labarai game da ƙarshen duniya don hakan ya ƙi zuwa a lokacin da suka zata. Shin, mutane sun san cewa waɗannan labaran da ake yaɗawa game da ƙarshen duniya ƙage ne kuwa?

Wataƙila za ka yi mamakin sanin ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ƙarshen duniya. Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbacin da zai sa mu kasance da bege game da ƙarshen duniya. Ƙari ga hakan, ya bayyana cewa wasu za su gaji da jira don suna ganin cewa ƙarshen ya ƙi zuwa a lokacin da suke tsammani. Don Allah, ka yi la’akari da amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya bayar game da tambayoyin da mutane suke yi dangane da ƙarshen duniya.

 Za a ƙone duniya da wuta ne?

AMSAR DA LITTAFI MAI TSARKI YA BAYAR: [Allah] ya kafa tussan duniya, domin kada ta jijjigu har abada.”—ZABURA 104:5.

Ba za a halaka duniya da wuta ko ta wata hanya dabam ba. Akasin haka, Littafi Mai Tsarki ya ce duniyar nan ita ce inda ’yan Adam za su kasance har abada. Zabura ta ce: “[Allah] ya bada duniya ga yan Adam.”—Zabura 115:16; Ishaya 45:18.

Bayan Allah ya halicci duniya, sai ya ce tana da “kyau ƙwarai,” kuma har zuwa yau, ra’ayinsa bai canja ba. (Farawa 1:31) Saboda haka, Allah ba zai halaka duniya ba amma zai ɗauki matakin da ya dace don duniya ta kasance har abada. Ya yi alkawari cewa zai “hallaka waɗanda ke hallaka duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 11:18.

Wataƙila, za ka ga kamar abin da aka rubuta a 2 Bitrus 3:7 ya nuna cewa za a hallaka duniya da wuta. Ayar ta ce: “Sammai da suke yanzu, da duniya kuma kanta . . . an tanaje su domin wuta.” Shin, wannan ayar ta nuna cewa za a ƙone wannan duniyar da wuta ne? Abin da za ka yi la’akari da shi a nan shi ne, a wani lokaci, Littafi Mai Tsarki yakan yi amfani da kalmomin nan, “sammai” da “duniya” da kuma “wuta” a alamance. Alal misali, a Farawa 11:1, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan duniya fa harshenta ɗaya ne, magana ɗaya ce kuma.” A nan, Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan, “duniya” wajen kwatanta mutane.

Kuma idan muka bincika mahallin 2 Bitrus 3:7 da kyau, za mu ga cewa an yi amfani da sammai da duniya da kuma wuta a alamance ne. Ayoyi na 5 da 6 sun nuna alaƙar da ke tsakanin rigyawar da ta faru a zamanin Nuhu da halakar da za ta faru a ƙarshen duniya. Allah ya halaka duniyar wancan zamanin, amma bai halaka doron ƙasar ba. Saboda da haka, “duniya” da Littafi Mai Tsarki ya ce an halaka yana nufin miyagun mutane da suka yi rayuwa a zamanin Nuhu ne. (Farawa 6:11) Ƙari ga haka, rigyawar ta halaka “sammai” na dā, wato, masu mulki na zamanin. Hakazalika, 2 Bitrus 3:7 ta annabta cewa za a halaka miyagun mutane da kuma masu mulki na wannan zamani gaba ɗaya, kuma ba za a sake ganin alamar su ba.

Mene ne zai faru a ƙarshen duniya?

AMSAR DA LITTAFI MAI TSARKI YA BAYAR: “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”—1 YOHANNA 2:17.

“Duniya” da aka ambata a nan cewa za ta wuce tana nufin mutanen da ba sa rayuwar da ta jitu da nufin Allah, ba doron ƙasa ba ne. Za a iya kwatanta wannan da yadda likitar fiɗa yakan yi wa  marar lafiya aiki saboda ya cire inda cutar kansa take a jikin marar lafiya don ya sami lafiya. Hakan ma Allah zai cire ko “datse” miyagu don nagargarun mutane su ji daɗin zama a duniya. (Zabura 37:9) Idan muka yi la’akari da wannan, za mu ga cewa “ƙarshen duniya” abu ne mai ban sha’awa.

Irin wannan kyakkyawan ra’ayi ne ya sa wasu juyin Littafi Mai Tsarki suka fassara “ƙarshen duniya” a matsayin “cikar zamani.” (Matta 24:3) Ka yi la’akari da wannan: idan har ’yan Adam da kuma duniyar da kanta za su tsira sa’ad da ƙarshen ya zo, za a yi wani sabon zamani ke nan, ko ba haka ba? Hakika, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da “zamani mai-zuwa.”—Luka 18:30.

Yesu ya kira wannan zamani mai zuwa “sabon zamani.” A lokacin, Yesu zai mai da ’yan Adam kamiltattu kamar yadda Allah ya nufa sa’ad da ya halicci duniya da kuma ’yan Adam. (Matta 19:28) Sa’ad da hakan ya faru, za mu ji daɗin rayuwa a duniya don

  • Aljanna za ta kasance a duniya kuma kowane ɗan Adam zai sami kwanciyar hankali da ci gaba.—Ishaya 35:1; Mikah 4:4.
  • Za mu yi aiki mai kyau kuma mai gamsarwa.—Ishaya 65:21-23.
  • Za a magance dukan cututtuka.—Ishaya 33:24.
  • Ba za a sake yin tsufa ba.—Ayuba 33:25.
  • Za a ta da matattu.—Yohanna 5:28, 29.

Idan muka yi “nufin Allah,” wato, abin da yake bukata a gare mu, ba za mu yi fargaba ba. A maimakon haka, za mu yi marmarin zuwan ƙarshen duniya.

Ƙarshen duniya ya kusa ne da gaske?

AMSAR DA LITTAFI MAI TSARKI YA BAYAR: “Sa’ad da kuka ga waɗannan al’amura na aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato.”—LUKA 21:31.

Farfesa Richard Kyle ya rubuta a cikin littafinsa, The Last Days Are Here Again, cewa “canjin da ake samu farat ɗaya da kuma tashe-tashen hankula da ake yi a wurare dabam-dabam ne suke sa mutane yin maganganu iri-iri game da ƙarshen duniya.” Hakan yake musamman idan mutane sun kasa fahimtar abin da ya sa waɗannan munanan abubuwan suke faruwa.

Amma abubuwan da marubutan Littafi Mai Tsarki suka annabta game da ƙarshen duniya ba bayani ba ne game da wasu munanan aukuwa da suka faru a zamaninsu. A maimakon haka, Allah ne ya hure su su bayyana yadda yanayi zai kasance sa’ad da ƙarshen duniya ya kusa. Ka yi la’akari da waɗansu daga cikin annabcin kuma ka bincika ko waɗannan annabcin suna cika a zamaninmu.

  •   Yaƙe-yaƙe da yunwa da girgizar ƙasa da kuma annoba.—Matta 24:7; Luka 21:11.
  • Mugunta zai ƙaru sosai saboda rashin imani.—Matta 24:12.
  • Mutane za su riƙa yin abubuwa da suke gurɓata duniya.—Ru’ya ta Yohanna 11:18.
  • Mutane ba za su kasance da ƙaunar Allah ba, a maimakon haka, za su kasance masu son kai, masu son kuɗi da kuma annashuwa.—2 Timotawus 3:2, 4.
  • Taɓarɓarewar zaman iyali.—2 Timotawus 3:2, 3.
  • Mutane ba za su kula da alamun da ke nuna cewa ƙarshen ya kusa ba.—Matta 24:37-39.
  • Za a yi wa’azin bishara game da Mulkin Allah a faɗin duniya.—Matta 24:14.

Yesu ya ce idan muka ga dukan “waɗannan al’amura” suna faruwa, mu san cewa ƙarshen duniya ya kusa. (Matta 24:33) Shaidun Jehobah sun yi imani cewa waɗannan abubuwan da suke faruwa sun nuna cewa tabbas ƙarshen duniya ya kusa, shi ya sa suke wa’azi ga mutane a ƙasashe 236.

Yadda mutane suke faɗin ra’ayoyi da ba daidai ba game da ƙarshen duniya yana nufin cewa ƙarshen ba za ya zo ba ne?

AMSAR DA LITTAFI MAI TSARKI YA BAYAR: “Bayan suna cikin faɗin, kwanciyar rai da lafiya, sai halaka farat ta auko musu, kamar yadda nakuɗa ta kan auko wa mace mai-ciki; ba kuwa za su tsira ba ko kaɗan.”—1 TASALONIKAWA 5:3.

Naƙuda da mace mai ciki take yi takan zo farat ɗaya kuma wajibi ta yi wannan naƙuda idan lokacin haihuwa ya yi. Hakazalika, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ƙarshen duniya zai zo tabbas kuma farat ɗaya. Yanayin da zai kai ga ƙarshen duniya yana kama ne da yanayin mai juna biyu. Mace mai juna biyu takan fahimci wasu canje-canje a yanayin jikinta da suke nuna mata cewa ta kusan haihuwa. Likita zai iya kimanta ranar da za ta haihu, amma ko da a ce ba ta haihu a ranar da take tsammani ba, ta tabbata cewa za ta sami ɗa ko ɗiya nan ba da jimawa ba. Hakazalika, ƙarshen duniya zai zo ba da jimawa ba don dukan alamu sun nuna cewa muna “kwanaki na ƙarshe,” ko da yake ba zai zo kamar yadda mutane suke zato ba.—2 Timotawus 3:1.

Za ka iya yin tambaya cewa, ‘Idan muna gab da ƙarshen duniya kuma alamun suna bayyane, me ya sa mutane da yawa ba su gane hakan ba?’ Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane da yawa za su yi watsi da waɗannan alamun. Maimakon su amince cewa waɗannan muhimman canje-canje suna faruwa ne a kwanaki na  ƙarshe, za su ɗauka cewa abubuwa suna tafiya daidai kuma za su riƙa yin ba’a suna cewa: “Tun daga randa ubanni suka kwanta barci, dukan al’amura suna nan kamar yadda suke tun farkon halitta.” (2 Bitrus 3:3, 4) Wato, mutane da yawa za su yi watsi da alamun da ke nuna cewa muna kwanaki na ƙarshe, ko da yake alamun nan a bayyane suke.—Matta 24:38, 39.

Wannan talifin ya tattauna wasu ne kawai daga cikin alamun da suke nuna cewa ƙarshen duniya ya kusa. * Idan kana so ka ƙara koya game da hakan, za ka iya tuntuɓar Shaidun Jehobah don ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su kyauta. Za su iya nazari da kai a gidanka ko kuma a duk inda ka ga ya dace, ko da ta wayar tarho ne. Lokacinka ne kawai za ka ba da kuma za ka amfana sosai.

^ sakin layi na 38 Don samun ƙarin bayani, ka duba babi na 9, mai kan maganar nan: “Muna Rayuwa ne a ‘Kwanaki na Ƙarshe’?” a cikin littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.