Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA KARƁI KYAUTA MAFI DARAJA DAGA ALLAH?

Kyauta Mafi Daraja Daga Allah—Me Ya Sa Take da Tamani?

Kyauta Mafi Daraja Daga Allah—Me Ya Sa Take da Tamani?

Mene ne yake sa ka daraja kyautar da aka ba ka? Wataƙila don waɗannan abubuwa guda huɗu ne: (1) wanda ya ba ka kyautar, (2) dalilin da ya sa aka ba ka kyautar, (3) sadaukarwar da mutumin ya yi da kuma (4) idan kana bukatar kyautar sosai. Yin tunani a kan abubuwa nan zai taimaka mana mu nuna godiya don kyauta mafi daraja daga Allah, wato fansa.

WANE NE YA BA DA KYAUTAR?

Muna ɗaukan wasu kyauta da tamani sosai idan mutanen da muke darajawa ne suka ba mu kyautar. Wasu kyautar kuma ba su da tsada amma muna daraja su domin wani danginmu ko kuma abokinmu ne ya ba mu. Haka yake da kyautar da Russell ya ba Jordan. Amma ta yaya hakan yake da alaƙa da kyautar fansa?

Da farko, Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici cikin duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa.’ (1 Yohanna 4:9, Littafi Mai Tsarki) Hakan ya sa kyautar ta kasance da tamani sosai. Babu wanda yake da iko kamar Allah. Shi ya sa wani marubucin zabura ya ce: ‘Kai, wanda sunanka Jehobah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.’ (Zabura 83:18) Shin ba za mu karɓi kyautar da Allah mai iko duka ya ba mu ba?

Na biyu, Allah “Ubanmu” ne. (Ishaya 63:16) Ta yaya? Domin shi ya ba mu rai. Ƙari ga haka, yana kula da mu sosai kamar yadda uba yake kula da yaransa. Allah ya kira mutanensa a dā da suna Ifraimu kuma ya ce musu: “Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? . . . Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, hakika zan yi masa jinƙai.” (Irmiya 31:20, LMT) Har a yau ma, Allah yana ɗaukan bayinsa a matsayin ‘ya’yansa. Shi ba Mahaliccinmu kawai ba ne, amma shi Ubanmu da kuma Abokinmu ne mai aminci. Shin hakan bai kamata ya sa kowace kyauta da ya ba mu ta kasance da daraja ba?

ME YA SA AKA BA DA KYAUTAR?

Wasu kyauta suna da tamani domin wanda ya ba da kyautar ya yi hakan don yana ƙaunar mu. Wanda ba ya son kai yana ba da kyauta kuma ba ya sa ran cewa za a biya shi wata rana.

Allah yana ƙaunar mu shi ya sa ya ba da Ɗansa a madadinmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici.’ Don me? “Domin mu sami rai madawwami ta wurinsa.” (1 Yohanna 4:9) Shin wajibi ne Allah ya yi hakan? A’a. “Fansar da Almasihu Yesu ya yi” ta nuna ‘alherin Allah.’Romawa 3:24, LMT.

Me ya sa ‘alheri’ ce ta motsa Allah ya ba da kyautar? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah na tabbatar mana da ƙaunar da yake mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu.” (Romawa 5:8) Ƙauna da kuma rashin son kai ne suka motsa Allah ya tausaya mana domin mu ajizai ne. Ba mu cancanci ya ƙaunace mu ba kuma ba za mu iya biyan sa ba. Wannan kyautar ta nuna irin ƙaunar da ba a taɓa nuna irinta ba a duniya.

WACE IRIN SADAUKARWA CE AKA YI?

Wasu kyauta suna da tamani domin wanda ya ba da kyautar ya yi sadaukarwa sosai. Idan mutum ya ba mu kyautar abu da ke da tamani sosai a gare shi, hakan yana sa mu daraja kyautar sosai.

Allah ‘ya ba da makaɗaicin Ɗansa.’ (Yohanna 3:16, LMT) Ba lallai ba ne Allah ya ba mu wanda yake ƙauna sosai ba. Shekaru da yawa da Allah ya yi yana halittar sama da ƙasa, Yesu ya yi aiki tare da shi kuma ya zama “abar murnarsa.” (Misalai 8:30, LMT) Yesu shi ne ‘ƙaunataccen Ɗan’ Allah da kuma “surar Allah marar ganuwa.” (Kolosiyawa 1:13-15, LMT) Ba a taɓa samun irin dangantakar da ke tsakanin Yesu da Jehobah ba.

Duk da haka, Allah bai “keɓe Ɗa nasa ba.” (Romawa 8:32) Jehobah ya ba mu abin da ya fi so. Babu wata kyauta da Jehobah ya ba mu da ta fi wannan.

TA BIYA BUKATUNMU NA GAGGAWA

Wasu kyauta suna da tamani domin sun biya abin da muke bukata da gaggawa. Alal misali, a ce kana rashin lafiya kuma ba ka da kuɗin zuwa asibiti. Amma sai wani ya ce zai biya kuɗin. Babu shakka, za ka yi farin ciki kuma ka gode masa sosai! Ba za ka taɓa mantawa da abin da ya yi maka ba, ko ba haka ba?

‘Gama kamar yadda cikin Adamu duka suna mutuwa, haka nan cikin Kristi duka za su rayu.’ (1 Korintiyawa 15:22) Muna mutuwa domin mu ‘ya’yan Adamu ne. Kuma ba za mu iya guje wa rashin lafiya da mutuwa ba ko kuma mu kasance da dangantaka da Allah ba. Ƙari ga haka, ba za mu iya ceci kanmu ko kuma wani ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Har abada mutum ba zai iya fansar wani ba, ba kuwa zai iya biyan kuɗin ransa ga Allah ba. . . . Abin da zai iya biya, sam ba zai isa ba.” (Zabura 49:7, 8, LMT) Muna bukatar taimako da gaggawa domin ba za mu iya biyan kuɗin fansa ba. Idan aka bar mu, za mu rasa mafita.

Saboda da ƙaunar da Jehobah yake mana, ya yarda ya ba da “maganin” da muke bukata don ‘duka mu rayu’ ta wurin Yesu. Ta yaya fansa ta cim ma hakan? “Jinin Yesu Ɗansa yana tsarkake mu kuma daga zunubi duka.” Hakika, idan muka gaskata da hadayar da Yesu ya yi, hakan zai sa a gafarta zunubanmu kuma mu sami rai na har abada. (1 Yohanna 1:7; 5:13) Amma mene ne fansar za ta yi wa waɗanda suka mutu? “Gama tun da mutuwa ta wurin mutum take, ta wurin mutum [Yesu] kuma tashin matattu yake.”1 Korintiyawa 15:21. *

Babu wata kyauta da Jehobah ya bayar da ta fi ta hadayar Yesu kuma ya yi hakan ne don ƙaunar da yake mana. Babu wanda ya taɓa yi mana sadaukarwa kamar Jehobah Allah. Kuma babu wata kyauta da ta biya ainihin abin da muke bukata kamar wadda ta cece mu daga zunubi da kuma mutuwa. Hakika, babu wata kyauta da za ta kai na fansar Yesu.

 

^ sakin layi na 19 Ka duba babi na 7 na littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? don ka samu ƙarin bayani game da nufin Allah a kan tashin matattu. Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi kuma akwai shi a www.pr418.com/ha.