Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Allah da Kuma Kristi

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Allah da Kuma Kristi

Ko da yake ’yan Adam suna bauta wa alloli dabam-dabam, Allah na gaskiya guda ɗaya ne tak. (Yohanna 17:3) Shi ne “Mafi Ɗaukaka,” Mahaliccin kome, kuma shi ne Mai ba da rai. Shi ne kaɗai ya cancanci mu bauta masa.​—Daniyel 7:18; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11.

Wane ne Allah na Gaskiya?

Sunan Allah ya bayyana a rubutun farko na Littafi Mai Tsarki WAJEN SAU 7,000

JEHOBAH shi ne sunan Allah

ALLAH, UBANGIJI, UBA​—Wasu daga cikin laƙabin Jehobah

Mene ne Sunan Allah? Allah da kansa ya ce: “Ni ne Yahweh [“Jehobah,” NW ], sunana ke nan.” (Ishaya 42:8) Sunan Allah ya bayyana wajen sau 7,000 a Littafi Mai Tsarki. Amma juyi da dama na Littafi Mai Tsarki sun sauya wannan sunan da laƙabi kamar su “Ubangiji.” Allah yana so ka zama amininsa, shi ya sa ya ce ka ‘kira sunansa.’​—Zabura 105:1.

Laƙabin Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya kira Jehobah da laƙabi kamar su “Allah,” da “Mai Iko Duka,” da “Uba,” da “Ubangiji,” da kuma “Maɗaukaki.” A cikin addu’o’i da yawa da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki, an ambata sunan Jehobah da kuma laƙabinsa.​—Daniyel 9:4.

Allah Ruhu Ne. Allah ruhu ne da ba a gani. (Yohanna 4:24) Littafi Mai Tsarki ya ce “ba mutumin da ya taɓa ganin Allah.” (Yohanna 1:18) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa abubuwan da mutane suke yi za su iya ɓata wa Allah rai, ko su sa ya “ji daɗi.”​—Karin Magana 11:20; Zabura 78:​40, 41.

Halayen Allah. Allah ba ya nuna wariya, yana ƙaunar kowa. (Ayyukan Manzanni 10:​34, 35) Ƙari ga haka, shi ‘mai jin ƙai ne, mai alheri, marar saurin fushi, ƙaunarsa ba ta canjawa, kuma yana cike da aminci.’ (Fitowa 34:​6, 7) Amma a cikin halayensa, akwai guda huɗu da suke burge mu sosai.

Iko. Da yake shi ne “Allah Mai Iko Duka,” ba abin da zai hana shi cika duk wani alkawarin da ya yi.​—Farawa 17:1.

Hikima. Allah ya fi kowa hikima. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce “shi ne kaɗai mai hikima.”​—Romawa 16:27.

Adalci. Allah yana yin abin da ya dace a kowane lokaci. Kome da yake yi “cikakke ne,” ma’ana, ba ya kuskure kuma “babu rashin gaskiya a gare shi.”​—Maimaitawar Shari’a 32:4.

Ƙauna. Littafi Mai Tsarki ya ce, “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Ba za a iya raba shi da ƙauna ba. Ƙauna ce take sa shi yin kome da yake yi, kuma hakan yana amfanar mu.

Dangantakar da Ke Tsakanin Allah da ’Yan Adam. Allah shi ne Ubanmu na sama da ke ƙaunar mu sosai. (Matiyu 6:9) Idan mun yi imani da shi, za mu zama aminansa. (Zabura 25:14) Hakika, Allah yana so ka riƙa yin addu’a a gare shi kuma ka ‘danƙa masa dukan damuwarka, gama shi ne mai lura da kai.’ Hakan zai sa ka kusace shi.​—1 Bitrus 5:7; Yaƙub 4:8.

Me Bambancin Allah da Yesu?

Yesu Ba Allah Ba Ne. Allah ne ya halicci Yesu kuma babu yadda za a ce Yesu ɗaya ne da Allah. Amma Yesu ne kaɗai Allah ya halitta da kansa, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira shi Ɗan Allah. (Yohanna 1:14) Bayan da Jehobah ya halicci Yesu, sai ya yi amfani da shi a matsayin “gwanin aiki” don ya halicci sauran abubuwa.​—Karin Magana 8:​30, 31; Kolosiyawa 1:​15, 16.

Yesu Kristi bai taɓa ce shi ne Allah ba. A maimakon haka, ya ce: “Daga wurin [Allah] na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.” (Yohanna 7:29) Da Yesu yake magana da ɗaya daga cikin mabiyansa, ya ce Jehobah ne “Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.” (Yohanna 20:17) Bayan rasuwar Yesu, sai Jehobah ya ta da shi zuwa sama kuma ya ba shi iko mai girma.​—Matiyu 28:18; Ayyukan Manzanni 2:​32, 33.

Yesu Kristi Zai Iya Taimaka Maka Ka Kusaci Allah

Yesu ya zo duniya don ya koya mana abubuwa game da Ubansa. Ga abin da Jehobah da kansa ya faɗa game da Yesu: “Wannan shi ne Ɗana, wanda nake ƙauna. Ku saurare shi!” (Markus 9:7) Babu wanda ya kai Yesu sanin Allah. Yesu ya ce: “Ba wanda . . . ya san ko wane ne Uban sai dai shi Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana masa” Uban.​—Luka 10:22.

Yesu ya yi koyi da halayen Ubansa. Yadda Yesu yake bin halin Ubansa ne ya sa ya ce: “Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban.” (Yohanna 14:9) Yadda Yesu ya nuna ƙauna kamar Ubansa ta furucinsa da kuma ayyukansa ya sa mutane sun soma bauta wa Allah. Ya ce: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Ƙari ga haka, ya ce: “Masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada cikin ruhu, da kuma gaskiya, gama Uba yana neman irin waɗannan ne su yi masa sujada.” (Yohanna 4:23) Ka ga, Jehobah yana neman mutane irin ka da suke so su san gaskiya game da shi.