HASUMIYAR TSARO Na 1 2020 | Ta Yaya Za Ka San Gaskiya?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar tambayoyi da suka fi muhimmanci a rayuwa.

Ta Yaya Za Ka San Gaskiya?

Ko da yake mutane ba su yarda da juna ba, kuma karya ta bazu a ko’ina, akwai tsarin da za ka bi don ka sami amsoshi na kwarai ga tambayoyi mafi muhimmanci game da rayuwa.

Littafi Mai Tsarki Sanannen Littafi Ne Mai Fadin Gaskiya

Littafi Mai Tsarki ya cancanci ka gaskata da shi dari bisa dari.

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Mulkin Allah

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana ko waye ne Sarkin Mulkin Allah, da inda mulkin yake, da dalilin da ya sa aka kafa shi, da shugabanninsa, da kuma talakawansa.

Yadda Rayuwa Za Ta Kasance a Nan Gaba

Ka bincika abin da zai sa ka dada yarda da abin da Allah ya ce zai faru da duniya da kuma mutanen da za su zauna a cikinta.

Me Za Ka Samu Idan Ka San Gaskiya?

Za ka amfana sosai idan ka san ainihin abin da Kalmar Allah take koyarwa.