Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Elias Hutter Mai Littattafan Ibrananci Masu Kayatarwa

Elias Hutter Mai Littattafan Ibrananci Masu Kayatarwa

ZA KA iya karanta Littafi Mai Tsarki na Ibrananci? Wataƙila hakan zai yi maka wuya. Mai yiwuwa ba ka ma taɓa ganin Littafi Mai Tsarki na Ibrananci ba. Amma, idan ka ji labarin wannan marubuci mai suna Elias Hutter da ya yi rayuwa a ƙarni na 16 da kuma Littafi Mai Tsarki na Ibrananci da ya fassara, za ka daraja naka Littafi Mai Tsarki.

An haifi Elias Hutter a shekara ta 1553 a garin Görlitz da ke kusa da iyakar ƙasar Jamus da Folan da kuma Jamhuriyar Czech. Hutter ya karanta Yarukan da ake yi a kudu maso yammacin Asiya a Jami’ar Lutheran da ke birnin Jena. Ya zama Farfesan Ibrananci a birnin Leipzig sa’ad da yake ɗan shekara 24. A matsayinsa na malami, ya buɗe makaranta a Nuremberg don a riƙa koya wa ɗalibai Ibrananci da Girkanci da Latinanci da kuma Jamusanci cikin shekara huɗu. A makarantarsa ce kaɗai ake iya yin hakan a lokacin.

“KYAUN WANNAN JUYIN”

Bangon gaba na littafin da Hutter ya juya zuwa Ibrananci a shekara ta 1587

A shekara ta 1587, Hutter ya fassara Nassosin da ake yawan kira Tsohon Alkawari zuwa Ibrananci. Sunan juyin Derekh ha-Kodesh. An ɗauko sunan daga littafin Ishaya 35:8 kuma yana nufin ‘Hanya Mai Tsarki.’ Yadda aka tsara rubutun ya tabbatar da cewa “wannan juyi ne mai kyau sosai.” Amma abin da ya sa wannan juyin yake da ban sha’awa sosai shi ne yadda ɗalibai suke amfani da shi wajen koyan Ibrananci.

Me ya sa Littafi Mai Tsarki na Ibrananci da Hutter ya fassara ya taimaka wa ɗalibai sosai? Bari mu yi la’akari da ƙalubale guda biyu da ɗaliban da ke koyan Ibrananci suke fuskanta. Na farko, baƙaƙƙen ba waɗanda suka saba gani ba ne. Na biyu kuma, ɗoriyar farko da na ƙarshe da aka saka wa kalmomi suna sa sanin ma’anarsu ta yi wuya. Alal misali, ku yi la’akari da kalmar nan na Ibrananci נפשׁ (da aka juya zuwa ne’phesh), da ke nufin “kurwa.” A littafin Ezekiyel 18:​4, an saka wa kalmar ɗoriyar farkon nan ה (ha), kuma hakan ya sa ta zama הנפשׁ (han·ne’phesh). Idan mutum bai ƙware ba, ba zai san cewa הנפשׁ (han·ne’phesh) da kuma נפשׁ (ne’phesh) ɗaya ne ba.

Hutter ya kirkiro wata dabara don ya taimaka wa ɗalibansa. Ya yi amfani da fasalolin rubutu guda biyu. Ya rubuta kowace kalma da fasali na yau da kullum. Amma ya saka wa baƙaƙƙen ɗoriyar farko da na ƙarshe rami a tsakiya. Wannan dabarar ta taimaka wa ɗalibai su iya bambanta tsakanin asalin kalmomin Ibrananci da kuma ɗoriyar farko da na ƙarshe. An yi amfani da wannan dabarar ma a ƙarin bayani da ke juyin New World Translation of the Holy Scriptures​—With References. Hoton da ke sama ya nuna fasalin da aka yi amfani da shi a Ezekiyel 18:4 a juyin Hutter da kuma a ƙarin bayanin New World Translation of the Holy Scriptures​—With References.

JUYIN IBRANANCI NA “SABON ALKAWARI”

Hutter ya kuma buga juyin da ake kira Sabon Alkawari zuwa harsuna 12. An buga wannan juyin a birnin Nuremberg a shekara ta 1599 kuma ana yawan kiransa Nuremberg Polyglot. Hutter ya so ya buga Nassosin Helenanci na Kirista a Ibrananci. Amma ya ce ko da ya “yarda ya biya miliyoyi” don a fassara Littafi Mai Tsarki zuwa Ibrananci, mafassaran ba za su yi aiki mai kyau ba. * Saboda haka, ya yanke shawarar fassara Sabon Alkawari daga Helenanci zuwa Ibrananci da kansa. Hutter ya bar dukan ayyukan da yake da shi kuma ya mai da hankali a kan fassarar. Ya kammala fassarar cikin shekara ɗaya!

Nassosin Helenanci na Kirista da Hutter ya fassara zuwa Ibrananci yana da kyau kuwa? Wani marubuci Ba’ibrane mai suna Franz Delitzsch da ya yi rayuwa a ƙarni na 19 ya ce: “Hutter ya yi amfani da kalmomin da Kiristoci suka daraja sosai a fassarar da ya yi zuwa Ibrananci. Sau da yawa, ya yi amfani da kalmomin da suka fitar da ainihin ma’anar a yaren.”

YADDA AIKINSA YA TAIMAKA

Aikin da Hutter ya yi bai sa ya zama mawadaci ba. Babu shakka, mutane da yawa ba su sayi juyinsa ba. Amma, aikin da ya yi ya taimaka sosai. Alal misali, William Robertson ya yi wasu gyare-gyare a Sabon Alkawarin da Hutter ya juya zuwa Ibrananci a shekara ta 1661 kuma Richard Caddick ma ya yi hakan a shekara ta 1798. Sa’ad da Hutter yake fassara Nassosin Helenanci, ya juya laƙabin nan Kyʹri·os (Ubangiji) da The·osʹ (Allah) zuwa “Jehobah” (יהוה, JHVH) a wuraren da ayar ta yi ƙaulin Nassosin Ibrananci ko kuma a inda ya ga cewa ana magana ne game da Jehobah. Hakan abu ne mai ban sha’awa sosai domin mutane da yawa da suka fassara Sabon Alkawari ba su yi amfani da sunan Allah ba, amma Hutter ya so ya mai da sunan Allah a asalin inda yake a Nassosin Helenanci na Kirista.

Saboda haka, a duk lokacin da ka sake ganin sunan Allah, Jehobah a cikin Nassosin Helenanci na Kirista, ka tuna da aikin da Elias Hutter ya yi da kuma Nassosin da ya fassara zuwa Ibrananci.

^ sakin layi na 9 Babu shakka, wasu sun taɓa fassara Sabon Alkawari zuwa Ibrananci. Ɗaya daga cikinsu shi ne Simon Atoumanos a wajen shekara ta 1360. Da wani marubuci ɗan Jamus mai suna Oswald Schreckenfuchs a wajen shekara ta 1565. Amma ba a taɓa buga su ba kuma a yau, babu littattafan.