Koma ka ga abin da ke ciki

Yin Imani da Yesu Ne Kadai Zai Sa Mutum Ya Sami Ceto?

Yin Imani da Yesu Ne Kadai Zai Sa Mutum Ya Sami Ceto?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Kiristoci sun yi imani cewa Yesu ya mutu don zunuban ’yan Adam. (1 Bitrus 3:18) Amma, samun ceto na bukatar fiye da yarda cewa Yesu ne Mai Ceto. Aljannu sun san cewa Yesu “dan Allah ne,” duk da haka za a halaka su, ba za su sami ceto ba.​—Luka 4:41; Yahuda 6.

 Mene ne zan yi don in sami ceto?

  •   Wajibi ne ka gaskata cewa Yesu ya ba da ransa saboda zunubanmu. (Ayyukan Manzanni 16:​30, 31; 1 Yohanna 2:2) Hakan ya kunshi imani cewa Yesu mutum ne da ya wanzu da gaske, da kuma imani cewa dukan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi gaskiya ne.

  •   Ka koyi ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar. (2 Timoti 3:15) Littafi Mai Tsarki ya ce manzo Bulus da Sila sun gaya wa wani mai gadin kurkuku cewa: “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, kai da iyalinka za ku sami ceto.” Bayan haka, sai suka koya wa mai gadin “kalmar” Jehobah. a (Ayyukan Manzanni 16:​31, 32) Hakan ya nuna cewa mai gadin kurkukun ba kawai imani da Yesu yake bukatar yi ba amma yana bukatar ya fahimci Kalmar Allah. Yana bukatar sanin tabbataccen Kalmar Allah da ke Littafi Mai Tsarki.​—1 Timoti 2:​3, 4.

  •   Tuba. (Ayyukan Manzanni 3:19) Dole ne ka tuba, ko ka yi nadama, saboda halayenka da dabi’arka na dā. Mutane za su ga cewa ka canja halayenka na dā da ke bata wa Allah rai kuma ka soma ‘yin abubuwan da za su nuna ka tuba.’​—Ayyukan Manzanni 26:20.

  •   Ka yi baftisma. (Matiyu 28:19) Yesu ya ce duk wanda ya zama almajirinsa za a yi masa baftisma. Mai gadin kurkukun da muka ambata dazu ya yi baftisma. (Ayyukan Manzanni 16:33) Hakazalika, bayan manzo Bitrus ya koya wa taron jama’a gaskiya game da Yesu, “wadanda suka yarda da maganar Bitrus kuwa aka yi musu baftisma.”​—Ayyukan Manzanni 2:​40, 41.

  •   Yin biyayya ga umurnin Yesu. (Ibraniyawa 5:9) Wadanda ke yin abubuwan da Yesu ya ‘umurta,’ suna nuna cewa su almajiransa ne ta salon rayuwarsu. (Matiyu 28:20) Sun zama “masu aikata kalmar Allah ba masu ji kawai ba.”​—Yakub 1:22.

  •   Jimrewa har karshe. (Markus 13:13) Mabiyan Yesu na bukatar ‘jimrewa’ don su sami ceto. (Ibraniyawa 10:36) Alal misali, manzo Bulus ya yi abubuwan da Yesu ya koyar kuma ya nuna aminci ga Allah. Ban da haka, ya jimre tsanantawa daga ranar da ya zama Kirista har mutuwarsa.​—1 Korintiyawa 9:27.

 “Addu’ar mai zunubi” kuma fa?

 A wasu addinai mutane suna yin addu’o’i’ kamar “Addu’ar mai zunubi” da “addu’a don sami ceto.” Masu yin irin wadannan addu’o’in sun amince cewa su masu zunubai ne kuma Yesu ya mutu domin zunubansu. Sukan kuma roki Yesu ya shigo zuciyarsu ko rayuwarsu. Amma Littafi Mai Tsarki bai ambaci “addu’ar masu zunubi” ba.

 Wasu na zaton cewa da zarar mutum ya yi “addu’ar mai zunubi” to yana da tabbacin cewa zai sami ceto. Amma addu’a ba zai iya tabbatar wa mutum cewa zai sami ceto ba. Mu ajizai ne don hakan muna yin kuskurai. (1 Yohanna 1:8) Saboda haka, Yesu ya ce mu yi ta addu’a don a gafarta mana zunubanmu. (Luka 11:​2, 4) Kari da haka, wasu Kiristoci da ba za su sami rai na har abada ba domin sun daina bauta wa Jehobah.​—Ibraniyawa 6:​4-6; 2 Bitrus 2:​20, 21.

 A ina ne aka samo “addu’ar mai zunubi”?

 ’Yan tarihi suna mūsun asalin inda aka samo “addu’ar mai zunubi” ba. Wasu sun ce a lokacin da aka kafa darikar Protestant ne. Wasu kuma sun ce an fara “addu’ar mai zunubi” ne a lokacin kirkiro addinai dabam-dabam a karni a kan 18 da 19. Littafi Mai Tsarki dai bai goyi bayan wannan addu’ar ba kuma ba ta jitu da koyar Littafi Mai Tsarki ba.

a Jehobah shi ne sunan Allah kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna.