Koma ka ga abin da ke ciki

Ta Yaya Zan Tsare Kaina Daga Batsa?

Ta Yaya Zan Tsare Kaina Daga Batsa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Ka yi la’akari da wadannan shawarwari na hikima da ke cikin Littafi Mai Tsarki:

  1.   Ka zama mai gwaninta. Ka kasance da fara’a da ladabi wajen abokan aikinka, amma kada ka yi na’am a nuna kana jin dadin halinsu na lalata ba.​—Matta 10:16; Kolosiyawa 4:6.

  2.   Ka yi adon kirki. Idan ba ka adon da ya dace zai sa mutane su yi tunanin banza game da kai. Littafi Mai Tsarki ya ce mu “yafa tufafi na ladabi tare da tsantseni da hankali.”​—1 Timotawus 2:9.

  3.   Ka yi zaben abokai da kyau. Idan kana bad da lokaci tare da wadanda suke kwarkwasa ko kuma masu lalata, lallai za su bi da kai haka kai ma.​—Misalai 13:20.

  4.   Ka guji mugun zance. Ka bar wajen idan zancen ta zama na “dauda, ko kuwa zancen wauta, ko alfasha, wadanda ba su dace ba.”​—Afisawa 5:4.

  5.   Ka guji yanayin da zai sa ka rashin aminci. Alal misali, ka mai da hankali sa’ad da aka gayyace ka fita liyafa bayan an tashi aiki.​—Misalai 22:3.

  6.   Ka zama mai gaba gadi. Idan aka nuna maka halin banza, ka gaya wa mai yinsa cewa ba ka son haka. (1 Korintiyawa 14:9) Alal misali, kana iya cewa: “Kina dami na ainu kuma ba na son haka. Ki daina.” Za ka iya rubuta wa mai yin batsa wasika kana gaya mata yadda kake ji, ka nuna kana son ta daina wannan hali. Ka nuna yadda kake ji a fili saboda tarbiyyarka da kuma addininka.​—1 Tasalonikawa 4:​3-5.

  7.   Ka nemi taimako. Idan yin batsar ta ci gaba, ka gaya wa wani aboki na kud da kud, ko wani cikin iyali ko kuma abokin aiki ko wani da ya kware a taimaka wa wadanda suka taba fuskantar wannan halin banza. (Misalai 27:9) Wasu da yawa da suka taba fuskantar batsa sun sami taimako ta wurin yin addu’a. Ko idan ba ka taba yin addu’a ba, kada ka rena taimakon da Jehobah zai iya yi maka da yake shi “Allah na dukan ta’aziya” ne.​—2 Korintiyawa 1:3.

 Yin batsa yana sa mutane miliyoyi ba sa iya aiki cikin sukuni, amma Littafi Mai Tsarki zai iya taimakawa.