Allah Yana da Wani Wajen Zama Ne?
Amsar Littafi Mai Tsarki
E. Allah yana da wani wajen zama—sammai. Ka duba waɗannan ayoyin Littafi Mai Tsarki:
A cikin wata addu’a, Sarki Sulemanu ya ce: “Sai ka ji cikin sama mazauninka.”—1 Sarakuna 8:43.
Yesu Kristi ya koya wa almajiransa su yi addu’a ga ‘Ubansu wanda ke cikin sama.’—Matta 6:9.
Bayan da aka ta da Yesu daga matattu, ya shiga “cikin sama kanta shi bayyana a gaban fuskar Allah.”—Ibraniyawa 9:24.
Waɗannan ayoyi sun nuna a fili cewa Jehobah, Allah ne na ainihi kuma wajen zamasa a sama ne kaɗai, ba a ko’ina ba.